Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce mutum 300 na mutuwa a kullum a nahiyar Afirka sakamakon matsalolin cutar hanta ta Hepatitis B da kuma C.
Mutum miliyan 71 na fama da matsananciyar cutar hanta da kwayar cutar virus ke haddasawa, kamar yadda Darektar WHO ta yankin Afirka, Dakta Matshidiso Moeti ta bayyana a sakon hukumar na Ranar Yaki da Ciwon Hanta ta Duniya ta 2020, wanda wakilin WHO na Najeriya Kazadi Mulombo ya karanta.
“Hepatitis B na iya ci gaba na tsawon shekaru ba tare da an gane ba kuma tana da mutukar hadari”, inji ta, a bayaninta game da hadarin cutar Hepatitis B.
Moeti ta ce kashi 85 na masu cutar hanta a Afirka na fama ne da Hepatitis B.
Ta ce yara ’yan kasa da wata daya da duniya sun fi saurin kamuwa, amma allurar rigakafin cutar cikin sa’a 24 da haihuwar jariri na magance ta.
Jami’ar lafiyar ta ce samar da maganin cutar da kuma wayar da kan kashi 90 na ’yan nahiyar zai takaita kamuwar mutum miliyan 1.2 da kuma mutuwar mutum miliyan 1.2 daga cutar a Afirka zuwa shekarar 2035.
Game da taken ranar ta bana (Rayuwa Marar Cutar Hanta a nan Gaba) Moeti ta jaddada muhimmancin hana yaduwar cutar daga uwa zuwa da ta hanyar gwajji da kuma bayar da maganin cutar Hepatitis B da kuma C.
Sai dai ta koka cewa duk da arahar rigakafin cutar Hepatitis B, kasashen Afirka 13 ne kawai suka aiwatar da shi a matakin kasa, wanda hakan ya kasa daga kasashe 25 da aka shirya samu a 2020.
Ta ce cimma yunkurin takaita Hepatitis B da kashi 90 da kuma Hepatitis C da kashi 65 zuwa shekarar 2030 “Zai yi nasara ne idan aka fadada bayar da rigakafi ta hanyar cin moriyar tsarin kare yaduwar cutar HIV da na Syphilis daga uwa zuwa da”.
WHO ta yi gargadin cewa jinkirin fadada magance cutar na iya kara yaduwarta, musamman a yanayin cutar COVID-19.