Mutum fiye da miliyan 20 na fama da ciwon hanta a Najeriya a yayin da alkalumma suka nuna cewa masu fama da cutar sun kai biliyan biyu a Duniya.
Wani kwararren likita, Farfesa Musa Muhammad Borodo ne ya bayyana hakan kamar yadda BBC ya ruwaito.
- Yau take ranar cika-ciki da cin jela a Kasar Hausa
- Buhari ya magantu kan juyin mulkin sojoji a Nijar
Farfesa Borodo, ya ce cutar ta yi yawa a kasar “Mutane biliyan biyu ke fama da cutar ciwon hanta, yayin da a Najeriya mutane sama da miliyan 20 ke fama da cutar.”
Ya ce “alamomin cutar sun hada da, sauyin launin ido zuwa kalar rawaya, zazzabi, da amai, sai dai idan cutar ta yi kamari tana haifar da aman jini, da kunburin ciki da kafafu.
“Kuma idan aka yi rashin sa’a tana shafar koda ko ta haddasa cutar kansa.
Wannan dai na zuwa a yayin da yau take ranar yaki da cutar ciwon hanta ta duniya, inda ake gangamin wayar da kai don kawar da cutar da kuma karfafa gwiwar al’umma su rika yin gwaji don gano mutum yana dauke da cutar ko akasin haka.
Bincike ya nuna cewa cutar hanta nau’in Hepatitis B wadda aka fi samun ta a yankin Afirka, ta kasance mafi hadari cikin nau’o’in cutar.
Miliyoyin mutane ne ke harbuwa da cutar duk shekara ba tare da sun sani ba, abin da ya sa ake ta kiraye-kiraye ga jama’a su rika yin gwaji a kai-a kai.
Likitoci sun bayyana cewa akwai cutukan hanta kusan kashi biyar da ake kamuwa da su walau ta hanyar shan gurbataccen ruwa da abinci ko shan kwayoyi barkatai ko ta hanyar da aka bai wa mutum jinin da bai dace ba.
Likitoci na kallon cutar hanta a matsayin shu’uma saboda yadda take cin karfin dan’adam kafin a gano ta.
Ciwon hanta na cikin manyan cutuka masu hadari da ke addabar jama’a, abin da ya sa Hukumar Lafiya ta Duniya ta hada gangami don kawar da ita nan da shekara ta 2030, ta hanyar yi wa jama’a gwaji da kuma riga-kafi musamman ga kananan yara.