✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya magantu kan juyin mulkin sojoji a Nijar

Ni da iyalina muna jimamin halin da Shugaba Bazoum ya tsinci kansa a Nijar.

Tsohon Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya bayyana kaduwarsa kan halin da Shugaban Nijar, Mohammed Bazoum da iyalansa ke ciki bayan juyin mulki da soji suka yi a kasar.

Cikin wani sako da mai magana da yawunsa Mallam Garba Shehu ya fitar, Buhari yana fatan cewa abubuwa za su koma yadda suke a baya domin tabbatar da lafiyar Shugaba Bazoum da iyalansa.

Sai dai kuma Buhari ya ce yana farin ciki dangane da yadda Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka ECOWAS karkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta gaggauta tarar hanzari domin tunkarar lamarin.

A cikin sanarwar, Buhari ya jaddada cewa shi da iyalansa sun bi sahun ’yan Najeriya wajen bayyana kaduwarsa kan wannan lamari.

Aminiya ta ruwaito cewa a Larabar wannan makon ce sojojin Nijar suka sanar da rusa Kundin Tsarin Mulkin Kasar, tare da dakatar da dukkan hukumomi gami da rufe iyakokin kasar da ke Yammacin Afirka.

Gabanin faruwar wannan lamari, Majalisar Dinkin Duniya da Amurka da Kungiyar Kasashen Turai EU da Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Afrika ta Yamma, ECOWA sun yi Allah-wadai da abin da ke faruwa a Jamhuriyar Nijar.