✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Hakimi ya sha guba ya mutu

A ranar Lahadin da ta gabata ce Hakimin Gidan Waya da ke masarautar Godogodo a Qaramar Hukumar Jama’a da ke Kudancin Jihar Kaduna Mista Justine…

Marigayi Justine Y. Dauda Hakimin Gidan WayaA ranar Lahadin da ta gabata ce Hakimin Gidan Waya da ke masarautar Godogodo a Qaramar Hukumar Jama’a da ke Kudancin Jihar Kaduna Mista Justine Y. Dauda ya kashe kansa ta hanyar kwankwaxar maganin vera, inda ya ce ga garinku nan bayan an garzaya da shi asibiti.

Hakimin mai kimanin shekara 60 a duniya wasu majiyoyi sun ce sun ji shi yana faxi a ranar da zai kashe kansa cewa ya gaji da rayuwar duniya saboda talauci.

Mai unguwar Hausawa na Gidan Waya, Malam Abdullahi Umar, yana xaya daga cikin waxanda marigayin ya faxa wa cewa ya gaji da wannan duniyar, inda shi kuma ya ba shi haquri sannan. Kuma an ce ya faxa wa iyalansa qudirinsa na kashe kansa amma ba su xauki maganar da wata muhimmanci ba sai bayan shan maganin veran da ya yi da misalin qarfe 11:00 na safe, inda ya sheqa barzahu da misalin qarfe 4:30 na yamma bayan garzayawa da shi Asibitin Francis da ke Gidan Waya.

“Da misalin qarfe 11:00 na safe ya je shagon Ibrahim Maitaki yana neman maganin vera don ya saya ba tare da sanin abin da yake shirin yi ba, inda aka shaida masa cewa ya qare har ma Limamin Masallacin Juma’a na Gidan Waya, Malam Jibril ya ce masa ai kyanwa ce maganin vera, cikin raha, inda ya kama hanya ya tafi, sai daga baya muka ji labari wai ya sha maganin vera ya rasu,” inji majiyarmu.

Matansa biyu; Maman Comfort, uwargida mai ‘ya’ya biyar da Maman Gideon, amarya mai ‘ya’ya huxu, sun bayyana kaxuwarsu kan faruwar lamarin.

Maman Comfort ta bayyana cewa a safiyar ranar da zai sha maganin veran sai da ya faxa mata cewa shi fa zai sha maganin vera don ya gaji da duniya, amma ta ce sai ba ta xauki abin da yake faxa da muhimmanci ba. “Zuwa can jimawa ina aiki a tsakar gida sai na ga ya shigo cikin xaki. Bayan wani lokaci kamar an ce in shiga in duba, kawai shigata cikin xakin ke da wuya sai na ji warin maganin vera ya game xakin, shi kuma ga shi kwance a kan gado. Da na tambaye shi, kan maganin veran, sai ya ce min shi ne ya sha maganin. Nan da nan na ga bakinsa ya fara kumfa shi ne muka kirawo mutane aka kai shi asibiti bayan wani lokaci kuma ya rasu.”

Ita kuwa Maman Gideon, ta bayyana cewa a iya saninsu babu wani abu na tavin hankali da yake damun mijinsu in ban da kukan talauci da yake yi kowane lokaci da kuma kukan rashin biyansu albashi da yake yawan yi a matsayinsu na hakimai. Ta ce “Sai xan kuxin fanshon da yake karva a matsayinsa na tsohon Ma’aikacin Hukumar Jiragen Qasa ta Najeriya (Najeriyan Railway Corporation), yake samu yana gudanar da rayuwarsa, amma duk da haka ba mu tava tsammanin zai yi abin da ya aikata ba,” inji shi.

Wani maqwabcin mamacin da ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana wa Aminiya cewa, “Akwai abin da ke damun marigayin, kwana biyu sai ka gan shi a kasuwa ya zo ya zauna a benci ya sa an zuba masa shayi, har sai da muka tava yi masa magana cewa bai dace a matsayinsa na Hakimi ya riqa zuwa shan shayi a kasuwa ba, kafin ya xan xaga qafa, tabbas akwai wani abu da ke damunsa. Kuma yana yawan kukan talauci.”

Lokacin da Aminiya ta tuntuvi Kakakin Rundunar ‘Yan sandan Jihar Kaduna ASP Aliyu Usman, bayan ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce yunqurin kisan kai babban laifi ne a dokar qasa haka ma haxa baki don hallaka mutum ko ta hanyar shayar da mutum guba ko wani abu daban. Ya ce amma idan mutum ya hallaka kansa da kansa ko ta wace irin hanya ce, matuqar babu gudunmawar wani ko wata wajen taimakawa ya kashe kansa, to wannan bai zamo wani laifi ba a doka.

Aminiya ta yi qoqarin jin tab akin Shugaban Qaramar Hukumar Jama’a Dokta Katuka Bege domin jin dalilin da ba a biyan hakiman albashinsu tsawon wata uku, amma ba ta samu nasara ba, sakamakon yadda dokar hana fita ta tsayar da komai ta yadda ma’aikatan qaramar hukumar ba su fita aiki.

Wata majiya ta ce rikicin da ke yawan tashi a qaramar hukumar da maqwabtanta Qaura da Zangon Kataf yana daga cikin dalilan da ke kawo rashin biyan albashin hakiman.

A shekaranjiya Laraba ce aka yi jana’izar marigayin a gidansa.