A wani yanayi mai kama da banbarakwai, a karon farko al’ummar birnin Kano za su yi bikin Karamar Sallah ba tare da irin hada-hadar da aka saba gani a al’adance ba.
Kama daga cefanen Sallah zuwa dinke-dinke, Aminiya ta gano cewa a bana babu yawan hada-hadar da aka saba gani idan Sallah ta matso.
A ranar Juma’a a wasu unguwanni da manyan titunan Kano, ana iya ganin mutane suna ta kai da kawowa, to sai dai akasarinsu sun ce yanayi bai ko kama kafar yadda aka saba yi kafin zuwan annobar coronavirus ba.
Yawanci idan Sallah ta karato, akan ga kasuwanni na wucin-gadi inda ake sayar da kaji a kusan dukkan manyan titunan dake anguwannin birnin.
Amma a wannan karon galibin wadannan kasuwannin ba su ci ba.
A unguwar Gwauron Dutse alal misali, irin wadannan masu sayar da kaji sukan yi dandazo don baje-kolin hajojinsu, amma a ranar Juma’a ba su da yawa in an kwatanta da shekarun baya.
Malam Bala wani mai sana’ar sayar da kaji ne kuma ya ce, “A gaskiya kamar yadda za ka iya gane wa idanunka babu masu saye da ma masu sayarwa kamar yadda muka saba gani bisa al’ada a shekarun baya.
“Hakan kuma ba ya rasa nasaba da halin kaka-ni-kayi da jama’a suka tsinci kansu a ciki a sakamakon kullen da wannan annobar ta coronavirus ta haddasa”.
Mun kuma yi katarin zantawa da wani wanda ya zo sayen irin wadannan kaji ko da dai ya nemi a sakaya sunansa.
“Gaskiya harkar a bana sai hamdala, kawai karfin hali mu ke yi mu kanmu. Mun riga mun saba faranta wa iyali amma su ma dole sai dai su yi hakuri a bana”, inji shi.
Ya kara da cewa a baya yakan yi yanka ne a gidansa yayin bikin Sallar Karama, amma a wannan karon sai dai ya sayo musu kaji su yi maneji.
Kasuwanni ba masaka tsinke
Ko da yake ilahirin manyan kasuwanni sun kasance a garkame bisa umarnin gwamnatin jihar in ban da kasuwannin abinci da na kayayyakin masarufi, da yawa daga cikin ‘yan kasuwar sun kasa kayayyakin su a bakin tituna daura da kasuwannin.
Hakazalika, Aminiya ta shaida cunkoson abubuwan hawa a kusan duk manyan titunan da suka hada manyan kasuwannin Kano.
Daga titin IBB, zuwa Ibrahim Taiwo Road da kuma titin Murtala Muhammad, mutane su kan shafe lokaci mai tsawo kafin su wuce saboda cunkoson ababen hawa da kuma kasa kayan da mutane suka yi.
A bangaren kasuwannin Muhammadu Abubakar Rimi dake Sabon Gari da kuma ‘Yan-Kura, da yawa daga cikin ‘yan kasuwar sun kasa kayan su ne a karkashin gadar sama ta Sabon Garin.
Ba a taru an zama daya ba
To sai dai a karon farko a cikin ‘yan kwanakin nan, mun lura cewa ranar Juma’a an bude hamshakiyar kasuwar nan ta kayan masarufi ta Kwanar Singa.
A cikin kasuwar dai akwai dubun-dubatar masu saye da sayarwa suna kai da komowa don hada-hadar Sallah a lokacin da Aminiya ta leka can.
Masu kayan miya da kayan marmari sun ce san-barka
A kasuwar sayar da kayan miya ta ‘Yankaba kuwa, ‘yan kasuwar sun ce sai san-barka domin kuwa suna ta hada-hada ba kama hannun yaro.
Mutane da dama wadanda akasarinsu mata ne sun fito domin cefanen miyar Sallah.
Zuwa yanzu dai gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da cewa za a gudanar da Sallar Idi kamar yadda aka saba, sai dai cikin taka-tsantsan da kuma kiyaye dokokin lafiya.
Ko a ranar Juma’a ma dai an gudanar da sallar a kusan ilahirin masallatan Juma’a dake jihar.
Bikin Sallar na bana zai zo da wani sabon salo da ba a taba ganin irinsa ba kasancewar ba wasu shagulgula da za a gidanar bayan Sallar ta Idi.