✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda gwamnoni suka kashe biliyoyin Naira wajen sayen motocin alfarma ga ’yan majalisa

Gwamnonin jihohi da dama sun kashe biliyoyin Naira wajen sayen motocin alfarma daga kasashen duniya daban-daban ga wakilan majalisun dokokin jihohinsu duk da karayar tattalin…

Gwamnonin jihohi da dama sun kashe biliyoyin Naira wajen sayen motocin alfarma daga kasashen duniya daban-daban ga wakilan majalisun dokokin jihohinsu duk da karayar tattalin arziki da kasar nan ke fama da shi.

Nazarin da Aminiya ta yi ya nuna cewa jihohi tara sun kashe sama da Naira biliyan 15 wajen sayo nau’o’in motocin dabandaban galibi ga ’yan majalisar dokokin a wannan zubin siyasa.

Kano

A bayan nan Gwamnan Jihar Kano Injiniya Abba Kabiru Yusuf, ya raba wa ’yan Majalisar Dokokin Jihar motocin alfarma da kudinsu ya kai Naira biliyan 2 da miliyan 700, kuma tuni wasu daga cikinsu suka karbi motocin alfarmar da kudin kowacensu ya kai Naira miliyan 68.

Majalisar Dokokin Jihar Kano tana da wakilai 25 da suka fito daga Jam’iyyar NNPP, yayin da 14 suka fito daga Jam’iyyar APC inda har yanzu ba a kammala zabe a kan kujerar dan majalisa daya ba.

’Yan majalisa sun samu motocin alfarma a Binuwai

Dukkan ’yan majalisa 32 na Majalisar Dokokin Jihar Binuwai sun karbi motocin alfarma da Gwamnan Jihar Hyacinth Alia ya saya musu. Kowace mota an ce kudinta ya kai Naira miliyan 60.

Gombe

A Jihar Gombe, a ranar 30 ga Disamban 2023 ne Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, ya mika sababbin motocin alfarma ga dukkan wakilan majalisar dokokin jihar 24 da kuma kwamishinoni 17.

An ce motocin 41 samfurin GAC Motor ‘All New GS4’ kudinsu ya kai kimanin Naira miliyan 33.5 kowace.

Gwamna Inuwa Yahaya ya ce an sayo motocin ne don a taimaka wa ’yan majalisar su gudanar da aikinsu na sa ido yadda ya kamata kuma su shiga a dama da su wajen gudanar da harkokin mulki.

Jihar Kogi

A Jihar Kogi, tsohon Gwamna Yahaya Bello ya mika motocin alfarma 40 da Tayota Hilux guda hudu ga ’yan Majalisar Dokokin Jihar da alkalai a ranar 22 ga Disamban, 2023.

Hakan ya faru ne saura wata daya ya sauka daga mulki Shugaban Majalisar Dokokin Jihar, Umar Yusuf ya samu motar alfarma daya da motoci biyu da za su tallafa masa ciki har da Toyota Hilux; yayin da mataimakinsa da shugaban masu rinjaye da sauran wakilai 22 suka samu guda daidai.

Da aka tuntubi wasu daga cikin ’yan majalisar sun ki bayyana kudin da aka sayi kowace mota; yayin da Kwamishinan Yada Labarai, Kingsley Fanwo, bai amsa sakon tes da aka aika masa ta tarho dinsa ba.

Ondo

A watan Agustan bara ne marigayi Gwamnan Jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya mika motoci da Kamfanin Motoci na JAC ya kera ga mambobin majalisar dokokin jihar 26 “domin saukaka” musu ayyukansu.

Majiyoyi a Gidan Gwamnatin Jihar sun shaida wa Aminiya cewa kowace mota ta kai Naira miliyan 19.

Sannan motocin alfarma kirar Toyota Land Cruiser da aka kiyasta kudinsu a kan Naira miliyan 106 kowace, aka saya wa Shugaban Majalisar Dokokin Jihar, Olamide Oladiji da Mataimakin Shugaban Majalisar, Abayomi Akinrutan.

Ebonyi

Gwamnan Jihar Ebonyi, Mista Francis Nwifuru, ya sayi motocin alfarma kirar BDR Land Cruiser Prado Jeep ga dukkan ’yan Majalisar Dokokin Jihar 24.

Bayanai sun ce kowace daya daga cikin motocin kudinta ya kai Naira miliyan 51.

Jihar Kebbi

A ’yan watannin da suka gabata ne Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris ya rarraba motoci kirar Toyota Jeep ga wakilan Majalisar Dokokin Jihar 24.

Wani babban jami’in gwamnatin jihar ya shaida wa wakilinmu cewa kowace mota kudinta ya kai Naira miliyan 1.9.

Kuma Kakakin Gwamnan, Ahmed Idris ya shaida wa Aminiya cewa an sayo motocin ne ga jami’an gwamnati don su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Jihar Osun

Gwamnatin Jihar Osun ta rarraba motoci samfurin Fortuner ga dukkan mambobin majalisar jihar 26 a wannan shekarar.

Sai dai Aminiya ba ta iya gano kudin da aka sayi motocin ba, saboda jami’an gwamnatin jihar sun ki cewa uffan lokacin da ta tuntube su.

Neja

A Jihar Neja, mambobin Majalisar Dokokin Jihar 25 daga cikin 27 sun karbi motocin samfurin Prado Jeep kowanensu daga Gwamna Mohammed Bago; yayin da Shugaba da Mataimakinsa aka ce sun samu samfurin Land Cruiser Jeep.

Kowace Prado Jeep an ce an saye ta a kan kimanin Naira miliyan 70.

Delta

A farkon wannan wata ne Gwamnan Jihar Delta, Sheriff Oborebwori ya ba wakilan Majalisar Dokoki ta Kasa daga jihar motoci don taimaka musu wajen gudanar da aikin kasa.

Bayan ba su motocin Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai kan Dokoki da Ayyukan Majalisa, Mista Francis Ejiroghene Waibe, ya zuba ruwan yabo wa Gwamna Oborebwori.

‘Rashin damuwa da talaka ne’

Wani tsohon Shugaban Jam’iyyar NCP ta Kasa, Mista Bayo Ogunleye ya bayyana yawaitar sayo motocin alfarma a matsayin rashin kan gado ko damuwa da talaka.

Ya ce wadannan ’yan majalisa suna koyi ne da takwarorinsu na Majalisar Dokoki ta Kasa, wadanda su ma suka sayi motocin alfarmar.

Ya ce, tunda Gwamnatin Tarayya ba za ta daina sayo motocin ba, zai yi wahala a gamsar da jihohi su daina sayo motoci masu tsada irin wadannan.

“Dukkan wadannan da ake kira zababbu sun zamo ba su damu da halin da al’umma suke ciki ba.

“Dubi halin da kasar nan take ciki, mutane suna fama da yunwa, farashin kayan abinci ya yi tashin gwauron zabo, amma duk da haka suna sayen motocin alfarma masu tsada ga ’yan majalisa,” in ji shi.

Kungiyoyi sun koka

A tattaunawa da Aminiya, Babban Jami’in Sadarwa na Kungiyar Yiaga Africa, Mark Amaza, ya ce lura da halin da tattalin arziki ke ciki a Nijeriya, kashe “makudan kudi a kan ’yan kalilan din mutane, na nuna rashin damuwa da halin da mutanen mazabunsu ke ciki ne.”

Ya ce, “Na biyu, wannan kyauta daga gwamna zuwa ga ’yan majalisa, ba ma kawai tana nuna rashin ’yanci ga majalisun dokokin kadai ba ne, har ma tana haifar da babbar ayar tambaya: Shin wadannan ’yan majalisa za su iya tuhumar bangaren zartarwa ko su sa ido wajen ganin yana yi daidai kamar yadda ake fata daga gare su?”

Babban Daraktan Gidauniyar Cleen Foundation, Gad Peter, ya ce, ba da motoci ga ’yan majalisa da sauran jami’an gwamnati ya zama “al’ada da dabi’a a Nijeriya da bangaren zartarwa ke yi.”

Ya ce, “Mun ga irin wannan tattaunawa lokacin da Majalisar Dokoki ta Kasa ta zo nata bukatar.

“Lokacin in ka yi magana sai su ce suna bukatar wadannan motoci don su rika zuwa yankunansu, wadannan hanyoyi ba su da kyau.

“To me ya sa ba za ku gyara wadannan hanyoyi ba ku rika kashe kudin kadan? “Idan muka zuba wadannan kudade a manyan ayyuka, za a samar da hanyoyi masu kyau,” in ji shi.

Shi ma da yake tattaunawa da Aminiya, Babban Daraktan Cibiyar Kare Hakkin Dan Adam da Wayar da Kai (CHRICED), Ibrahim Zikirullahi, ya ce Gwamnatin Tarayya ma ta yi irin haka duk da adawar da jama’a suka nuna.

Ya koka cewa “Cikakken rashin nuna damuwa da halin kuncin da talakan Nijeriya ke ciki yana da matukar daga hankali, musamman lura da abin da Gwamnatin Tarayya ke shirin biya a matsayin mafi karancin albashi ga ma’aikata.”