Gwamnan Jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri ya yi wa rayuwar wani dan adawar gwamnatinsa, Husaini Gambo barazana.
A sautin kiran wayan gwamnan da matashin da ya karade kafafen sada zumunta, Fintiri ya yi barazana ga rayuwar Husaini idan har ya sake shiga gonarsa.
- #EndSARS: An cafke ‘barayi’ 238 da taraktoci 35 a Adamawa
- An ba ‘barayin’ kayan tallafin Adamawa sa’a 12 su dawo da su ko a rushe gidajensu
- Gwamnatin Adamawa ta gargadi jama’a game da dokar hana fita
- Fasa Rumbuna: An sanya dokar hana fita a Adamawa
“Husaini idan ka sake magana a kaina sai na yi maganinka, kuma babu wanda ya isa ya cece ka a kasar nan”, inji furucin.
Shi kuma daga bangarensa Husaini bayan ya hasala shi ma ya mayar wa da gwamnan martani, inda yace “ranka ya dade iyakacin abin da za ka iya yi shi ne ka daure ni a gidan yari”.
Husaini shi ne Shugaban Kungiyar Matasa Masu Rajin Cigaban Jihar Adamawa ta Adamawa Concerned Citizens, kuma daya daga cikin masu adawa da gwamnatin Fintiri.
Yayin da jaridar Daily trust ta tuntubi Husaini domin jin ta bakinsa dangane da lamarin, ya tabbatar da cewa gwamnan ya kira shi a waya ranar Laraba da misalin karfe 8 na dare.
A cikin wani bidiyo da Husaini ya saki, ya bayyana cewa da gwamnatin jihar ta raba kayan tallafin COVID-19 da babu wanda zai shiga satar kayan al’ummar jihar.
- Fintiri ya tayar da kura
Masu ruwa da tsaki da masana siyasa a fadin jihar Adamawa, sun shiga tofa albarkacin bakinsu game da lamarin.
Tuni dai jam’iyyar APC mai adawa a jihar ta yi tir da abin da gwamnan ya yi.
A martaninta, Sakataren Tsare-tsaren APC a Jihar Adamawa, Ahmad Lawan ya yi abin kunya da kyama ne a samu gwamna ya yi hakan.
Ya ce ana zabi gwamna ne domin ya kare rayukan daukacin mutanen jiha ba ya zama barazana ga rayuwarsu da ‘yancinsu ba.
Sai dai Solomon Kumangar, Hadimin Gwamnan kan Kafofin Sadarwa ya bayyana cewa sautin da aka nada an yi masa kari a ciki.