✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda gobara ta yi ajalin uwa da ’ya’yanta 3

Gobarar ta tashi da tsakar dare a yayin da suke bacci.

Gobara ta yi ajalin wata mata mai uwa tare da ’ya’yanta uku a yayin da suke tsaka da barci da dare. Jihar Ebonyi, yayin da suke tsaka da barci.

Lamarin ya ritsa da suna Misis Chigozie da ’ya’yan nata ne a ranar Talata a yankin Aguabata Echara da ke Karamar Hukumar Ikwo a Jihar Enboyi.

Aminiya ta gano cewar wutar gobarar da ta tashi a lokacin da suke tsaka da barci da kama gidan da suke ciki ne baki daya.

Mista Samuel Okoro, wanda dan uwa ne ga wadanda lamarin ya rutsa da su ya tabbatar da faruwar lamarin.

Sai dai ya zargi cewa wani ne ya yi sanadin tashin gobarar, saboda a cewarsa, babu wata alama da ta nuna an kunna wuta a kusa da gidan.

“’Yar uwata ce matar da ta rasu. Mijin da take aure matansa biyu amma matarsa ta farko ba a gida daya suke zaune tare ba.

“Na samu labari cewa da aka sanar da mijinta abin da ya faru sai da ya kusa suma saboda kaduwa.

“Sai dai har zuwa yanzu ba mu san inda ya shiga ba.

“Watakila yana tunanin za mu huce haushinmu a kansa ne. Amma za mu koma tunda har yanzu ba a dauke gawarwakin ba suna can,” a cewar Mista Okoro.

Mun yi kokarin jin ta bakin kakakin ’yan sandan jihar ta Ebonyi, DSP Loveth Odah, amma hakarmu ba ta cim-ma ruwa ba.