Gobarar da ta rika tashi a muhimman gine-gine uku na Gwamnatin Tarayya a Abuja a cikin kwana 9 na wannan wata, ta jawo zargi da neman a yi bincike daga kungiyoyi da jama’a da kuma babbar jam’iyyar hamayya ta PDP.
Gobarar farko ta auku ne a ofishin Akantan Janar, inda bayanan harkar kudi na Gwamnatin Tarayya suke. Gobar ta auku ne ranar 8 ga Afrilu, yayin da gobara ta biyu ta auku a ranar 15 ga Afrilu, a Hedikwatar Hukumar Yi wa Kamfanoni da Kungiyoyi Rajista ta Kasa (CAC) da ke Abuja. Sai ta uku wadda ta auku a Hedikwatar Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) a ranar 17 ga Afrilu.
A bayanan da aka fitar bayan aukuwar tashe-tashen gobarar, wasu daga cikin hukumomin da lamarin ya shafa sun danganta haka da matsalar dawowar wutar lantarki bayan daukewa.
Sai dai kungiyoyin sa-ido da babbar jam’iyyar adawa ta PDP, sun bayyana mamaki kan lamarin inda suka ce akwai ayar tambaya a kai, inda suka yi zargin cewa daukacin lamarin na da nasaba da juna.
Ofishin Akanta Janar
A ziyarar da ya kai kwana daya bayan aukuwar gobarar Ofishin Akanta Janar, Alhaji Ahmed Idris, Minista a Ma’aikatar Kudi, Yarima Clem Agba ya ce za a binciki lamarin don tantance ko na da nasaba da daga na’urar sanyi da ake zargin daga gare ta wutar ta faro, ko wani abu ne daban ya haddasa wutar. Ministan wanda ya ce lamarin ya auku ne a benen da ke dauke da bayanan kwangilolin ma’aikatu da hukumomi, ya ce abin farin cike shi ne matsalar ba ta shafi na’urar adana bayanai na ofishin ba. “Saboda haka ba wani muhimmin bayani da muka rasa a gobarar,” inji shi.
A Hukumar CAC wadda ta hadu da gobarar da misalin karfe 10:20 na safe a ranar 15 ga Afrilu, a hawa na 6 , mahukuntan hukumar sun ce ta faro ne daga na’urar sanyaya daki. Sai dai sun ce ba wani muhimmin kundin bayani da aka rasa a gobarar.
Yadda gobarar Hukumar INEC ta kasance
Gobara ta karshe da ta auku a Hedikwatar Hukumar INEC, bayanin da mahukuntanta suka fitar, ya ce gobarar ta fara ne da misalin karfe 11 na safe inda ta rutsa da ofishin Mataimakin Daraktan Sa-ido a kan Zabubbuka da Jam’iyyu. Hukumar ta ce lamarin ya shafi hoton takardun bayanai (photocopy) da na’urorin kwafe takardu da kwamfutoci. Sai dai ta ce ba ta shafi muhimman takardunsu ba.
Tuni Hukumar Kashe Gobara ta Kasa (FFS) ta sanar da niyyarta ta gudanar da bincike kan tashe-tashen gobarar. Babbar Kakakin Hukumar Misis Huan Ugo wadda ta tabbatar da hakan ga Aminiya a ranar Talatar da ta gabata, ta ce binciken nasu zai shafi tantance musabbabin aukuwar gobarar a wuraren uku da nufin magance aukuwar haka a gaba.
Sai dai a zantawarsa da wakilinmu, Babban Daraktan Kungiyar CISLAC, Malam Auwal Ibrahim Rafsanjani ya nuna kokwanto kan shirin binciken, wanda ya bayyana da cewa akwai lauje cikin nadi.
M alam Auwal Rafsanjani ya ce binciken matsalar na bukatar masana a bangaren zakulo bayanai da kuma hukumomin tsaro. Ya ce kasancewar matsalar farko ta auku ne kwana biyu bayan Majalisar Dokoki ta Kasa ta nemi Ministar Ayyukan Jinkai da Bada Tallafi, Hajiya Sadiyya Umar Faruk ta gabatar musu da takardun bayanai kan tallafin da gwamnatin ke rabawa ga jama’a mafiya talauci, inda aka ce ta shaida musu cewa takardun bayanan suna ajiye ofishin, ya sa akwai bukatar cikakken bincike.
“Sannan sanin kowa ne cewa kashi 70 cikin 100 na almundahanar kudi a gwamnati na faruwa ne a kwangila, kuma sanannen abu ne babu wani kamfani da ya cancanci a ba shi kwangila sai yana da rajista da Hukumar CAC. Sai ga gobara ta biyu ta auku a ofishin hukumar da ke dauke da sunayen masu kamfanoni, mako 1 bayan ta farko.
Game da gobarar Hedikwatar INEC, Rafsanjani ya yi zargin cewa akwai wadanda suka tabbatar ba zabensu aka yi ba, inda ya ce irin wadannan mutane za su yi duk mai yiwuwa wajen ganin bayanan yadda aka bi wajen zabensu sun kau. “Duk da gwamnatin Shugaban Kasa Buhari na tutiyar yaki da cin hanci, har yanzu gwamnatin ta gaza sa hannu kan dokar bada kwangila (Public Procurement Act), kuma rashin hakan na sa ana yin badakala a harkar kwangila,” inji shi.
Alhaji Salihu Yakudima wani jigo a Jam’iyyar PDP a Abuja, bukatar a yi garbawul a Maaikatar Jinkai da Tallafa wa Mabukata ya yi, inda ya yi zargin cewa mutane kalilan ne ke tafiyar da ma’aikatar sabanin sauran ma’aikatun gwamnati da ke da isassun ma’aikata. Ya yi zargin cewa Ministar Ma’aikatar ba ta da kwarewa kan sha’anin ma’aikatar, kuma jadawalin mabukata da ake amfani da shi don tantance masu fama da talauci ya gaza, inji shi. Saboda haka ya bukaci a nemi kwararru (Consultants) don sake fasalta tsarin.