Ibtila’i ya afka wa Kasuwar Daji da Kasuwar Kara da ke Jihar Sakkwato, inda gobara ta lakume kantuna da kayan miliyoyin kudi.
Aminiya ta gano cewa shaguna sama da 150 ne suka kone kurmus a Kasuwar Daji, gami da konewar kayan miliyoyin kudi a gobarar ta ranar Laraba.
- Najeriya A Yau:Tattalin Arziki: Yadda 2021 Ta Zo Wa ‘Yan Najeriya
- An dauki Jose Peseiro sabon kocin Super Eagles
Wutar ta tashi ne da misalin karfe 11:30 na safiyar Laraba, ta yi ta ci har zuwa yammacin ranar kafin a yi nasarar kashe ta.
Gobarar Kasuwar Kara kuma ta dauki lokaci tana ci ba tare da an samu kashe ta ba, sai da hadin gwiwar jami’an kashe gobara na tarayya da na jihar Sakkwato suka so daga bisani suka yi nasarar kashe ta daga baya.
Wutar ta tashi da misalin karfe 7 na yammacin ranar Laraba.
Har zuwa lokacin kammala hada wannan rahoto ba a samu tabbacin abin da ya haddasa tashin gobarar a kasuwannin biyu ba, amma ana zargin yana da alaka da wutar lantarki.
Da yake magana kan gobarar, Shugaban Kungiyar ’Yan Kasuwar Jihar Sakkwato, Alhaji Chika Sarkin Gishiri, ya ce an yi asarar dukiya mai tarin yawa a kasuwannin biyu.
Kwamishinan Kasuwanci da Ma’aikatu na jihar, Bashir Jegawa, wanda ya ziyarci kasuwannin, ya ce gwamnatin jihar za ta kafa kwamiti na musamman don tabbatar da girman asarar da aka yi, tare da tallafawa wanda abun ya shafa.