Ana neman tono gawar tsohon Gwamnan Jihar Oyo, marigayi Otunba Christopher Adebayo Alao-Akala, domin yin gwajin ƙwayoyin halitta (DNA) da nufin tantance halastattun ’ya’yansa da za su ci gadon dukiyar da ya bari.
Batun tono gawar ta kunno kai ne bayan taƙaddama ta yi tsami a tsakanin ’ya’yan tsohon gwamnan a kan rabon gadonsa.
Babbar ’yar marigayin mai suna Uwargida Oluwatoyin Alao-Aderinto ce ta shigar da ƙara a gaban Mai Shari’a Taiwo na Babbar Kotun Jihar Oyo ta hannun lauyanta, Oladipo Olasope (SAN), inda ta roƙi kotun ta bayar da umarnin tono gawar mahaifin nasu daga kabarinsa domin yin gwajin ƙwayar halittarsa ga wasu mutane bakwai da ke iƙirarin cewa su ne halastattun ’ya’yan marigayin.
Uwargida Aderinto ta shigar da ƙarar ne bayan abin da ta kira barazanar da ’yan uwanta ke yi na neman cire sunanta daga cikin jerin halastattun ’ya’yan marigayin da za su gaje shi.
A takardar ƙarar, ta bayyana cewa ɗaukar matakin tono gawar mahaifin nasu da yin gwajin jini ga ’yan uwan nata su bakwai, har da ita kanta, shi ne zai taimaka wajen tantance ainihin halastattun ’ya’yan
marigayin da suka cancanci cin gadon ɗimbin dukiyar da ya bari a ciki da wajen Nijeriya.
Tsohon Gwamna Otunba Adebayo-Alao Akala ya mutu ne cikin watan Janairu na shekarar 2022, inda aka binne shi a cikin watan Oktoban shekarar a wani ƙasaitaccen kabari da aka gina a harabar gidansa da ke mahaifarsa a garin Ogbomosho da ke jihar.
Dukiyoyin da tsohon gwamnan ya mutu ya bari da ’ya’yan nasa suke jayayya a kai, waɗanda Lauya Oladipo ya gabatar gaban kotun, sun haɗa da rukunin gidajen alfarma a biranen Ibadan da Legas da Abuja da kuma ƙasashen Amurka da Birtaniya da wani katafaren otel a ƙasar Ghana.
Sauran sun haɗa da motocin alfarma da maƙudan kuɗaɗe a bankuna daban-daban a Nijeriya da ƙasashen Amurka da Birtaniya.
Tushen rikicin rabon gadon Alao-Akala
An fara wannan taƙaddama a tsakanin ’ya’yan tsohon gwamnan ne bayan da aka binne gawarsa a watan Oktoba na shekarar 2022.
Rikicin ya samo asali ne bayan mutum biyu daga cikin ’ya’yannsa masu suna Kemi Alao-Akala da Olamide Alabi suka samu izinin daga magatakardan kotun rabon gado na Jihar Oyo, ba tare da sani ko amincewar Uwargida Oluwatoyin Alao-Aderinto ba, a matsayinta na babbar ’ya ga marigayin.
Ta yi zargin cewa ’yan uwan nata sun kitsa lamarin ne da gangan ta bayan fage, kuma abin da suka yi ya saɓa wa dokokin rabon gado na Nijeriya. Don haka ta zargi ’yan uwan nata da neman yin kwanciyar magirbi a kan dukiyar da mahaifinsu ya bari.
A watan Agustan2023, Lauya Oladipo Olasope (SAN) ya yi zargi a cikin wata wasiƙa cewa, ƙoƙarin cire sunan Uwargida Oluwatoyin AlaoAderinto, a matsayinta na babbar ’yar Marigayi Adebayo Alao-Akala daga cikin jerin ’ya’yansa zai iya haifar da babbar ɓaraka da rabuwar kawunan wannan babban gida.
Saboda haka ya nemi kotun ta hanzarta ɗaukar matakin biyan buƙatun wadda yake karewa, na tono gawar marigayin domin a kawo ƙarshen matsalar ɗungurungum.