Gobara ta lakume dukiyoyin miliyoyin Naira a babbar kasuwar abincin dabbobi da ke Gashua a Jihar Yobe.
Ganau sun tabbatar wa Aminiya cewa wutar ta tashi ne ranar Asabar da dare, ta yi ta ci har zuwa safiyar Lahadi.
- Gobara ta tashi a kusa da Masallacin Annabi na Madina
- Guguwa ce ta sa na ‘samu juna biyu’ —Mace
- Yadda aka kama wata mata da ke shayar da maciji nononta
- Yadda kayan hada rabobi ka sa kankancewar al’aura —Bincike
Wani dan kasuwar, Alhaji Ibrahim Faraja, ya ce gobarar ta cinye kayan masarufi, abincin dabbobi, rumfuna, da injinan yanka katako na miliyoyin Naira a kasuwar.
Alhaji Ibrahim Faraja ya ce shi kansa ya yi asarar siminti na fiye da Naira miliyan uku a kantinsa sakamakon gobarar.
Ya ce ba a kai ga tantance musabbabin gobarar ba, amma ana ayyukan masu shaye-shayen da ke taruwa a kusa da kasuwar na da hannu a ciki.
Dan kasuwar ya roki Gwamnatin Tarayya da ta Jiha da sauran hukumomi da su agaza wa ’yan kasuwar da suka yi asara a gobarar.
Gobarar ta Kasuwar Gashua ta tashi ne kasa da mako guda bayan makamanciyarta da aka samu a Babbar Kasuar Katsina.