✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Gidauniyar bSF ke gyara Arewa maso Gabas

Gidauniyar Tallafa wa Wadanda Rikici ya Shafa (bSF) yana ci gaba da inganta rayuwar mutanen yankin Arewa maso Gabas ta hanyar sake gine-ginen kayayyakin inganta…

Gidauniyar Tallafa wa Wadanda Rikici ya Shafa (bSF) yana ci gaba da inganta rayuwar mutanen yankin Arewa maso Gabas ta hanyar sake gine-ginen kayayyakin inganta rayuwa da Boko Haram ta barnata.

Babban Daraktan Gidauniyar bSF, Farfesa Sunday Ochoche ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabin bude taron kara wa juna sani a kan muhimmancin amfani da sababbin kafafen watsa labarai na zamani wajen kawo labaran jinkai da ci gaba a ranar Litinin da ta gabata. Taron wanda aka yi da hadin gwiwar Gidauniyar bSF da Kwamitin PCNI ya gudana ne a Yola, Jihar Adamawa. Ochoche ya yaba kyakkyawar dangantakar da ke tsakanain Kwamitin PCNI da Gidauniyar bSF, inda ya ce abin koyi ne, sannan ya ce Gidauniyar bSF tana ba bangaren ilimi da rayuwar al’umma da kiwon lafiya muhimmanci a yankin Arewa maso Gabas.

Da yake nazari kan ayyukan gidaauniyar a fannin ilimi, Shugaban Gidauniyar ya ce shirin ilimi na gidauniyar ya shafi kananan yara dubu 100, sannan sun kusa kammala ginin makarantu shida a Michika da makarantu 24 da ke yankunan Madagali da Hawul da Chibok da Hong da Askira Uba a jihohin Adamawa da Borno. daukacin makarantun da ke Dikwa da tsakiyar Bama an sake gininsu, inda batun tsaro ya haifar da tsaikon aikin makarantun da ke wajen garin. Ana sake ginin daukacin makarantun Buni Yadi da ke Jihar Yobe da Sakandaren Gwamnati ta Takum a Jihar Taraba, wanda aka yi mummunar lalata ta sanadiyyar rikicin kabilanci. Ya yi bayani kan aikin da suke yi mai taken Shirin Wajibi ne Ilimi Ya ci Gaba da Samuwa, wanda ba na samun riba ba ne da Gidauniyar bSF ke tallafa masa kuma yake daukaridawainiyar yara fiye da 700 a Yola da Lasa, a matsayin shirin hadin gwiwar farfado da ilimi a yankin Gabas maso Gabas.

Gidauniyar bSF ta kai tallafi a fannin kiwon da lafiya daga asibitoci 7 zuwa 16. Kuma kowace cibiyar kiwon lafiya tana karbar tallafin Naira miliyan 20 domin daukar dawainiyar kula da lafiyar harin Boko Haram ya shafa, tare da biyan kudin magani da zarar an tura su zuwa wasu cibiyoyin kula da lafiya, ga wadanda suke bukatar ayyukan kula da lafiya na musamman da dauki wajen yi musu dori a asibitin kashi. Ochoche ya yi nuni da tallafin Gidauniyar bSF ga asibitoci irin su Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri domin shawo kan mummunar illar raunukan da aka samu sanadiyyar hare-haren kunar bakin wake.

Shugaban Gidauniyar bSF din ya yi nuni da cewa harin kunar bakin wake ya hargitsa tsarin zaman al’umma a Arewa maso Gabas, inda mata suka kasance masu nema wa iyalansu abinci a al’ummomi da dama bisa la’akari da yawan mazan da aka rasa saboda ayyukan ta’addancin. Kan wannan dalilin, ya ce, Gidauniyar bSF ta karkata akalar shirin samar da abin gudanar da harkokin rayuwa kacokam domin tallafa wa mata. Shirin ya fara ne da mata dubu da ke tsugunne a sansanin ’yan gudun hijira, wadanda aka ba su tallafin Naira dubu 20 kowanensu a matsayin jari. Shirin ana ta fadada shi daga lokaci zuwa lokaci don karade jihohin Adamawa da Yobe, inda a halin yanzu ya tallafa wa mata dubu 10, yayin da aka kara yawan kudin tallafin jarin zuwa Naira dubu 30. Mata sun samu horo da tallafi daban-daban a fannoni daban-daban na koyon sana’o’in dogaro da kai, wadanda aka tsara domin bunkasa hanyoyin neman abincinsu a matsayinsu na jagaban al’ummominsu. Aikin da shirin zai gudanar nan gaba a shirin bayar da tallafin zai karkata akala ne wajen bayar da tallafi ga daidaikun jama’a wadanda za su kara kaimi wajen aiwatar da ayyukan hadin gwiwa a al’ummomin, inda Gidauniyar bSF za ta bunkasa tallafinta wajen tara kudi da bayar da bashi ga kungiuyoyi da sauran kungiyoyin mata da ke yin sana’o’i.

An fadada kudin shirin zuwa aikin gona inda zai hada da noman rani da na damina. Haka Gidauniyar bSF ta samar da wani tsari na tallafin Naira dubu 20 ga kowanne mutum a shirin a koma gona a wannan yankin mai cike da albarkar kasar noma.

Kuma an kaddamar da sabon shirin kiwon dabbobi a Geidam na Jihar Yobe, tare da iyali 200 wanda kowane mutum daya ya samu dabbobi hudu. Farfesa Ochoche ya sake cewa tsarin karafafa wa mata gwiwa don dogaro da kai yana fuskantar kalubale musamman yadda ake yunkurin siyasantar da lamarin zabar wadanda ya kamata su amfana a shirin.

Ya ce inda lamarin ya zama haka an dakatar da zaben domin tabbatar da cewa wadanda suka cancanta ne kawai daga matan aka zabo. Ya ce wannan dakatarwar ta jawo tsaikon aiwatar da shirin, inda ya yi kiran a ba su lokaci, ya ce, ana samun tsaikon ne saboda burin bSF na tabbatar ba a yi almundahana a lokacin zabo masu cin gajiyar shirin ba.

Farfesa Ochoche ya jawo hankalin kan shirin kula da yara na bSF, inda ya ce yanzu shirin yana tallafa wa yara dubu daya da rikicin Boko Haram ya mayar marayu. Kuma kowane iyali yana karbar Naira dubu 14, kuma saboda bSF galibi yana sanya yara biyu ne a karkashin kulawar gidaje, adadin ya karu zuwa Naira dubu 28 a duk wata. Wadannan kudade ana biyansu ne na tsawon wata 10  don iyalan su koma cikin hayyacinsu. 

Kuma Kwamitin Kare Hakkin Yara ne yake sanya ido kan yadda ake tafiyar da shirin, inda kuma yake tsaye don kawo dauki a duk lokacin da aka yi yunkurin musguna musu. A karshe Mista Ochoche ya gode wa wadanda suka shirya taron bitar, sannan ya bukaci wadanda suka halarta su hada hannu da PCNI da kuma bSF a kokarinsu na sake gyara yankin.