✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda gidan talabijin a Turkiyya ya kwashe ma’aikatan BBC Hausa guda 9

Wasu daga cikin ma'aikatan sun shafe sama da shekara 10 suna aiki da BBC.

Wata sabuwar kafar yada kabarai mai suna TRT da aka bude a kasar Turkiyya ta kwashe kwararrun ma’aikatan Sashen Hausa na BBC har guda tara.

Ma’aikatan dai wadanda da yawansu sun yi shura wajen gudanar da shirye-shirye a kafafen sada zumunta da intanet na na kafar yada labaran.

An dai bude sabuwar kafar ne da ke Turkiyya da zummar mayar da hankali kan yada shirye-shirye cikin harshen Hausa.

Gidan talabijin din na TRT dai ya nada Nasidi Adamu Yahaya a matsayin Shugaban sashen Hausa, inda kuma Halima Umar Saleh da Ishaq Khalid suka kasance a matsayin mataimakansa.

Daga cikin wadanda gidan talabijin din ya dauke daga BBC Hausa akwai Umar Rayyan, wanda shi ne yake kula da shafukan sada zumunta na BBC Hausa; da suka hadar Twitter, Facebook da kuma Instagram.

Ragowar da suka kama aiki da sabon gidan talabijin din sun hadar da Abdulbaki Aliyu Jari, Mustapha Musa Kaita, Abdulsalam Usman Abdulkadir, Bashir Idris Abubakar.

Sai kuma Abdulwasi’u Hassan wanda aka dauko shi daga Sashen BBC na Yoruba.

Sai dai BBC har yanzu ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan sauya wurin aiki da ma’aikatan nata suka yi ba.