✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda gasar wakar Yahaya Bello ta tayar da kura a Kannywood

Godiya, gugar zana da tsarguwa ta biyo bayan gasar Wakar Garkuwan Matasa.

A makon jiya ne furodusa Abdul Amart Maikwashewa ya yi taron bikin karrama gwarazan gasar wakar Garkuwan Matasa, wadda mawakan Kannywood suka yi wa Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, inda aka raba kyautar motoci da babura da babura masu kafa uku da sauransu.

Kyaututtukan da aka raba a taron Hoto: Instagram @generalbmb4pmb

Bayan taron bikin, wasu ’yan Kannywood sun shiga Instagram suna yaba wa Abdul Amart tare da godiya bisa tagomashin da yake samar musu.

Daga cikin masu godiyar akwai Nasiru Ali Koki, wanda ya ce, “Ban san iya godiyar [da] zan ma [ba], amma zan ce Allah Ya kai rahama kabarin mahaifanka amin, Ya kare ka da karewarsa. Ina godiya.”

Shi ma Bello Muhammad Bello ya yi dogon rubutu da Turancin Ingilishi yana yabo da godiya.

A cikin hakan ne har abin ya fara rikidewa zuwa gugar zana, da habaice-habaice.

Gugar zana ko tsarguwa?

Khalid Yusuf Ata, daya daga cikin manyan yaran Ali Nuhu shi ma ya rubuta cewa, “Ba ka nuna ka fi kowa komai ba, a hakan ka faranta wa kowa!

“Ba ka yi fariya da yabon kai ba, dalilin hakan Allah Ya ba da amsa a kan kokwanton da ’ya’yan banza ke yi a kanka!

“Sun dade suna ba za ka iya ba, amma suna ji suna gani Allah Ya iya maka!

“Bukatar wasu ka fifita a kan taka, sai Allah Ya fifita maka taka a kan takadiran mahassada!

“Ka zamto dan aiken da bai ajiye komai ba a kan bukatar kansa ba! Yadda ka sanya farin ciki a zukatan mutane Allah Ubangiji Ya ci gaba da faranta maka duniya da lahira.

“Allah Ya maka tsari da ’yan kiran lamba. Kwashewa farin cikin al’umar masa’antar shirya fina-finai.”

A kasan rubutun nasa sai wasu suka yi ta jan hankalinsa a kan cewa habaici babu kyau.

Takaddama

Ana cikin wannan ne sai darakta Sanusi Oscar 442 ya wallafa wani hoton rubutu mai dauke da cewa, “Ba don Abdul Amart ba, da yanzu ’yan Kannywood mabarata ne,” sannan ya rubuta cewa, “Wannan ra’ayina ne, ku biyo ni a sannu za ku ji dalilin da ya sa na rubuta haka.”

A kasan rubutunsa, Hamza Talle Maifata ya ce, “Ina daya daga ciki.” Shi ma Garzali Miko ya ce, “Haka yake ko shakka babu,” sannan furodusa Abdulaziz Dan Small ya ce, “Ba karya ba ne, haka abin yake.”

A wani bangaren kuma, Darakta Aminu S. Bono ya wallafa wani dogon rubutu, wanda ya yi na daya da na biyu, inda a ciki ya yaba tare da kawo wasu hanyoyi da dama da mawakin siyasa Dauda Kahutu Rarara ya bi domin kawo sauyi a masana’antar Kannywood.

Kwatsam sai Mansur Make Up wanda na kusa da Adam A. Zango ne sosai ya wallafa cewa, “Rayuwar ’yan fim ta shiga rudani. Wannan ya ce ba don wane ba da harkar ta lalace, wannan ma ya fada nasa gwanin.”

Sannan ya rubuta cewa, “Kuma babban abin damuwar ita ce in fa ba ka yi hakan ba wai ba ka cikin manya a bangaren da kake yabo, kuma ba su san wannan habaice-habaicen ba ne ya kashe film din tun farko.

“Ni dai ba na bayan kowa duk wanda ya yi abin alheiri zan yi masa addu’a ko a cikin zuciyata ne. Allah Ka saita tunaninmu, Ka hane mu hassada da ganin kyashin juna.

“Shawarata ita ce kar ka tsaya fim kadai, ka nemi wata sana’a kuma in ba haka ba kullum kana cikin jin haushin wani.”

A kasan rubutun ne darakta Aminu S. Bono, makusancain Rarara ya rubuta cewa, “Mansur ni ban yi rubutu don cece-kuce ba, na yi domin karin karfin gwiwa ga kowanne bangare [ne] saboda ni na san amfaninsu, amma wasu suna amfani da haka don cin mutuncin wasu, ba daidai ba ne wannan.

“Mutane da Allah Ya ba mu suke taimakon masana’antar mu yi musu addu’a tare da fatan samun irinsu da yawa nan gaba, shi ke nan fa rubutuna kuma a ciki na yabi kowanne bangare saboda ko’ina na amfana da su kuma sun amfanar.”

Sai wani mai amfani da sunan Garkwan_Abdulamarta ya mayar wa Aminu S. Bono da martani cewa, “…ka tsargu ke nan?”

Sannan Mansur ya ce, “Idan kai ka fara yi, to ba kai ne mai laifi ba, idan kuma shi ya fara yi, to kai ne mai laifi. Allah Ya gyara zukatanmu.”

Hakan ya sa Aminu S. bono ya dawo ya ce, “Au wani yayi rubutu ne, ni wallahi ban ma sani ba.”

Kannywood ta dade tana fama da matsalolin rashin hadin kai, duk da cewa matsalar ba a kanta kadai ta tsaya ba, har da masana’antun fim na duniya.