✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda gasar tsere ta makarantar Centagon ta gudana a Abuja

Filin ya cika ya batse da xalibai da malamai da iyayen yara da kuma ’yan kallo a lokacin da makarantar Centagon International School da ke…

Filin ya cika ya batse da xalibai da malamai da iyayen yara da kuma ’yan kallo a lokacin da makarantar Centagon International School da ke Abuja ta shirya gasar tsere a tsakanin xalibanta a matakai daba-daban.
Gasar wacce makarantar ta yi mata taken: “Gasa ta biyar a tsakanin xaliban makarantar Centagon” ta gudana ne a katafaren filin wasa na kasa da kasa da ke kan hanyar filin saukar jiragen sama na Abuja a karshen makon da ya gabata.
Xaliban da ke wakiltar Green Bee Eaters su ne suka zama zakara a gasar tseren inda suka samu maki 191 inda xaliban Red Fishers suka zo na biyu da maki 181, xaliban Yellow Weabers suka zo na uku da maki 117 sannan kuma xaliban Blue King Fishers suka zo na karshe da maki 116.
Da yake karin bayani kan gasar, shugaban gasar kuma xaya daga cikin iyayen yaran makarantar Muhammad Sidi Ali ya bayyana cewa gasar ta kayatar da su sosai.
Ya bayyana cewa a matsayinsu na iyayen yara za su ci gaba da bai wa makarantar goyon baya don ganin ta ci gaba da karfafa wa yara gwiwa a fanin wasannin motsa jiki.
Shugabar makarantar, Misis Nosen Omoluwa ta ce makarantar ta shirya gasar ce don ta bunkasa harkokin wasannin motsa jiki a tsakanin yaran makarantar.
Ta bayyana cewa makarantar za ta ci gaba da shirya gasa daban-daban a fannin wasannin motsa jiki don taimaka wa yaran da suke da sha’awar wasan motsa jiki su koyi yadda za su cimma burin su a fannin wasanni.
Xalibai da dama da Aminiya ta tattauna da su jim kaxan bayan kammala gasar sun bayyana jin daxinsu ga yadda makarantar ta shirya musu gasar.
Sun yi kira ga shugabannin makarantar su ci gaba da gudanar da irin gasar shekara-shekara sannan kuma ta bullo da gasar wasanni iri-iri don su rika karawa a tsakaninsu.
Hakazalika su ma iyayen yara da dama da Aminiya ta tattauna da su a wurin gasar sun bayyana farin cikinsu ga yadda gasar ta gudana.
Sun jadadda ci gaba da bayar da goyon bayansu ga makarantar don cimma burin da makarantar ta sanya a gaba.