✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda fyade ga kananan yara ke yawaita a Sakkwato

Masu ruwa-da-tsaki a Jihar Sakkwato sun yi tir kan yadda fyade  ga kananan yara mata ke yawaita a jihar, inda suka ce lamarin da abin…

Masu ruwa-da-tsaki a Jihar Sakkwato sun yi tir kan yadda fyade  ga kananan yara mata ke yawaita a jihar, inda suka ce lamarin da abin damuwa musamman yadda ake haihuwar yara ba ta hanyar aure ba, inda suka yi kira a dauki matakin magance matsalar.

Hukumar Hisba ta Jihar Sakkwato ma ta koka kan lamarin, inda ta ce a bara ta samu rahoton fyade har guda 606.

Kwamandan Hisbah na Jihar Sakkwato Dokta Adamu Bello Kasararawa ya bayyana haka, inda ya ce hakan ya nuna an samu karuwar fyade 296 kan na shekarar 2018.

Ya ce, “A watan Janairun bana kawai mun samu rigimar fyade 31. Abin da nake son a gane wadanda ake yi wa fyaden yara ne mata daga shekara 5 zuwa 16.”

Kwamandan ya ce wadanda ake zargi da aikata fyaden ana samunsu a cikin ’yan siyasa da sarakuna da ’yan kasuwa da malaman addini da manyan mata.

Ya dora laifin kan wadansu iyaye da ke ganin talauci zai sa su bari ’ya’yansu su fada cikin wannan matsala.

Yadda ake yaudarar yara a yi musu fyade

Wata yarinya mai shekara 7 da aka sakaya sunanta, tana cikin wadanda aka taba yi wa fyaden. Mahaifiyarta ta bayyana wa wakilinmu yadda lamarin ya faru cewa, “Ita wannan yarinyar ita ce ta bakwai a cikin ’ya’yana, a wata ranar Lahadi da karfe 6 na yamma na nemi yarinyar ban ganta ba, na shiga ko’ina cikin gidajen makwabta ba a ganta ba, sai zuwa wani lokaci ta dawo. Na tsare ta ina tambayarta inda ta je, da na tsorata ta shi ne sta fada min cewa tsohon makwabcinmu ne ya sanya ta a dakinsa na gefen gida ya ba ta sukari ya yi mata abin da ya yi mata.”

Ta ce wannan mutum ana zarginsa a unguwar cewa yana raba wa yara sukari ne domin ya yaudare su. “Mun je Asibitin Kwararru na Jiha da yarinyar an tabbatar an bata ta, kan haka muka kai maganar gaban hukuma,” inji ta.

Mahaifin yarinyar mai shekara 54 ya ce ya so ya dauki mataki mai tsanani kan lamarin, amma mutanen unguwa suka ba shi baki kan ya sassauta lamarin, shi ne ya amince amma da sharadin su yi yarjejeniya ba zai sake kula ’ya’yansa ba, duk da mahaifiyar yarinyar ba ta gamsu da wannan hukunci ba.

Wanda ake zargin, mai shekara 55 da ke aiki a wani otel, ya ce kazafi aka yi masa, “Wannan maganar karya ce sun yi min kazafi ne domin ina da wata jikakkiya tsakaninmu, in har ina yi Allah Ya tona asirina kada Ya ba ni abin da nake so duniya da Lahira. Maganar ina raba wa yara sukari, kyauta ce ba don wani abu ba. Ni ba zan taba aminta da abin da ban yi ba.”

Wata budurwa mai shekara 21 wadda tun tana ’yar shekara 10 wani mutum mai shekara 72 mai sana’ar wanki da guga a unguwarsu ya yi mata fyade, abin da ya yi sanadiyyar ta ci gaba da ba shi kanta har ta samu ciki, bayan da mako biyu aka gane tana da juna biyu da aka bincika asibiti aka gano ya kai wata shida da shiga, yanzu ta haifi ’ya mace.

“Wata rana ce an aike ni sai na shiga gidansa ba kowa sai ya ba ni kasarin da na je nema (abincin da ya lalace) ya kuma ba ni Naira 100 kyauta, ya ce gobe in dawo akwai kasarin in dauka. Kullum idan na zo sai ya ba ni 100 a hakan har ya shige ni, daga nan na rika kai kaina wurinsa, yanzu da hukuma ta shiga ciki ya aminta zai aure ni, ni ma na yarda zan aure shi,” inji ta

Kakar yarinyar mai kimanin shekara 60 ta yi da-na-sanin rashin kulawar gaske wa jikarta har wannan lamari ya rika faruwa tsawon shekara 10 ba ta sani ba, kuma ta aurar da yarinya da ciki, sanadin haka za ta auri tsoho don ya bata mata rayuwa.

Wata mai shekara 16 da aka yi wa fyade ta samu ciki har ta haifi yaro, hukuma ta shiga tsakaninsu kuma shi ma wanda ake zargin ya yi mata ya yarda zai aure ta.

Mahaifin yarinyar ya ce matakin hukuma da muka dauka ne ya sanya wanda ya yi aika-aikar ya aminta zai aure ta da alkawarin zama ne na Sunnah ba cutarwa a tsakaninsu, “Mun aminta da hakan yanzu za su yi aure,” inji shi.

A Karamar Hukumar Wurno, akwai wata yarinya mai shekara 17  da maza hudu suka amince sun yi mata fyade a lokacin. Yayan yarinyar ya ce ba za su bar maganar haka ba sai an kwato wa kanwarsa hakkinta.

Babban Limamin Unguwar Dambuwa, Ustaz Abubakar ya ce wannan abin yana nuna akwai matsala a tsakanin al’ummar Musulmi, inda ya ce “Da wuya ka samu haka a wajen wadanda ba Musulmi ba.”

Sannan ya yi kira ga hukumomi su dauki mataki kan matsalar, musamman ta samar wa matasa aikin yi da magnce talla a tsakanin mata kanana.

Daya daga cikin jagorori a Karamar Hukumar Sakkwato ta Arewa Alhaji Ahmad Gwagawo ya bayyana damuwarsa kan, inda ya ce abin da ke kara kawo faruwar lamarin akwai yawan matasa sun kai mizanin aure amma ba su yi ba domin ba aikin yi.

Dokta Kasarawa ya ce samar da doka kan fyade a jihar za ta taimaka wajen rage matsalar in ba ta kau gaba daya ba, sai ya yi kira ga iyaye su daina boye maganar fyade idan aka yi wa ’ya’yansu domin hakan na taimakawa ga yaduwar lamarin.