✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda fim ya hada Mansura Isa da Sani Danja

A kasan hoton, masoyansu da dama sun ta yin kira gare su da su shirya tsakaninsu.

A ranar Lahadi ce tsohuwar jarumar Kannywood, Mansurah Isa ta hadu da tsohon mijinta, kuma tsohon jarumin Kannywood, Sani Danja a wajen kallon fin dinta, ‘Fanan’.

A wani hoto da ta wallafa a shafinta na Instagram, jarumar ta sanya hotonta a kusa tsohon mijin nata, inda ta ce, “Anya ya yi murmushi kuwa? Ku taimaka min ku duba.

“Bai kamata wannan kwalliyar ta tafi a banza ba. Ina tunanin ya kamata in bude shi a Instagram domin ya samu damar ganin wannan hoton da na sanya.”

Fim din Fanan yana jan hankalin mutane musamman yadda wakar fim din ta yadu, tun kafin fim din ya fito.

A kasan hoton, masoyansu da dama sun ta yin kira gare su da su shirya tsakaninsu su koma su cigaba da zamansu a matsayin mata da miji.

Aminiya ta ruwaito rabuwar auren tsofaffin jaruman masana’antar ta Kannywood a watan Mayun bana, lamarin da ya dauki hankalin mutane da dama a ciki da wajen masana’antar.