Wasu fatake ragon layya daga Arewacin Najeriya sun gano wani dan uwansu da ya je cirani Jihar Ogun, amma ya mike kafa a garin Ogunmakin, ya yi zamansa babu amo babu labarinsa.
Fataken sun samu labarin dan uwan nasu ne mai suna Abdullahi Dodo, sai suka yi masa dabara ya zo wurin da suka sauke dabobbinsu a garin Sabo Abeokuta, inda suka nemi ya shirya su koma gida tare da shi, amma ya ce atafau.
Da ‘yan uwan nasa suka ga haka sai suka kama shi da karfin tsiya suka yi masa daurin huhun goron, suka jefa shi a babbar motar daukan kaya.
Da yake tabbatar wa Aminiya da faruwar lamarin, shugaban matasan garin Sabo Abeokuta, Bashir Danladi Kaura, ya ce ‘yan uwan dan ciranin sun shaida masa cewa mutumin ya baro gidansu da ke Gidan Goga a Jihar Zamfara shekaru shida da suka shige a lokacin da za a yi bikin auren diyarsa.
“Ya baro gida ne da nufin neman kudin da zai aurar da ‘yarsa, tunda ya fito bai koma ba, ba ya aike, ‘yan uwansa basa jin duriyarsa.
“Don haka suka bukaci ya bi su su koma gida amma ya yi gardama, sai suka kama shi suka daure, suka kuma tafi da shi da karfin tsiya.
“Irin wannan yana faruwa, sai ka ga mutum ya baro gida ya mike kafa ya manta da ‘yan uwansa; ka san wani idan ya samu wuri a bariki sai ya mike kafa domin babu mai fada masa ya ji”, inji shi.
‘Yan uwan mutumin da ba su so a bayyana sunansu ba, sun shaida wa Aminiya cewa an dade ana neman dan uwan nasu, ba a san inda ya shiga ba.
Sai yanzu da suka kawo ragunan layya domin sayarwa a Abeokuta suka sami labarin inda yake, suka kuma shirya yadda za su komar da shi gida.
Suka ce an dade da yi wa ‘yar tasa aure har ma ta haifi ‘ya’ya biyu, bayan fitowarsa gida da sunan neman kudin aurar da ita.
Aminiya ta zanta da mutumin mai suna Abdullahi Dodo inda ya shaida cewa tun da ya fito neman kudin da zai yi wa ‘yarsa aure bai samu ikon komawa gida ba.
Yace yana sana’ar hakar rijiya ne a garin Ogunmakin da ke jihar Ogun.