Hauhawar farashi a Najeriya ya ƙaru a watan Satumba, inda ya kai mataki mafi girma cikin kimanin shekara 20 da kashi 26.72 cikin 100, daidai lokacin da tsadar rayuwa ke ƙara ta’azzara a ƙasar.
Hauhawar farashn na watan Satumba, ya ƙaru karo na 9 a jere daga kashi 25.8 cikin 100 a watan Agusta, kamar yadda alƙaluman Hukumar ƙididdiga ta Najeriya (NBS) suka nuna.
Hauhawar farashin kayan abinci ne ya fi yawa, idan an kwatanta da ƙaruwar farashi a sauran bangarorin kayayyaki da na ayyuka, inda ya tashi zuwa kashi 30.60 cikin 100 a watan Satumba daga kashi 29.34 cikin 100 a watan Agusta.
Cire tallafin man fetur da Shugaba Tinubu ya yi tun a watan Mayu, har yanzu na haifar da tsadar abinci da na sauran kayayyaki da rashin aikin yi da tsadar sufuri, tare da matsalolin tattalin arziki ga dumbin mutane.
A matsayinta na ƙasa mafi arzikin man fetur a Afirka, Najeriya na neman rancen dala biliyan 1.5 daga Bankin Duniya domin cike gibin kasafin kudinta.
Najeriya ta tsara kasafin kudinta na shekara ta 2023 a kan hasashen dala biliyan 28.1.
Gwamnatin Najeriya kuma na da burin samun tallafin kuɗi daga hukumar raya kasashe ta duniya (IDA), wadda wani reshe ne na Bankin Duniya da ke bayar da taimako ga kasashe masu fama da talauci a duniya.
Tattalin arzikin Najeriya dai na fuskantar kalubale ciki har da ɗimbin basuka da hauhawar farashin abinci da faduwar darajar Naira, wadda a halin yanzu ana canzar da ita a kan sama da naira 1,000 a kan duk dalar Amurka ɗaya a kasuwannin musayar kuɗi.