✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda dubun wasu masu garkuwa da mutane ta cika a Kaduna

Mun so mu yi garkuwa da magidancin sannan mu yi wa matarsa fyade.

Jami’an Sashen Binciken Sirri na Ofishin Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya (IRT), sun cafke wasu ‘yan ta’adda biyu bisa zargin yunkurin garkuwa da fyade a Kaduna.

Abdurahman Lolo da Muhammed Sani sun shiga hannu ne a yankin Bandoko bayan da suka shiga gidan wani magidanci suka yi garkuwa da shi.

Kakakin ‘Yan Sandan Jihar Kaduna, CSP Muyiwa Adejobi, ya ce wadanda ake zargin sun yi ikirarin cewa sun yi  shirin su yi garkuwa da magidancin sannan kuma su yi wa mai dakinsa fyade.

Tawagar jami’an karkashin jagorancin DCP Olatuniji Disu, sun samu nasarar cafke wadanda ake zargin ne bayan da aka kwarmata wa rundunar Operation Puff Adder abin da ya faru.

A cewar Kakakin, ‘yan ta’addan sun shaida musu cewar niyarsu ita ce su kama magidancin sannan bayan haka, su taru su yi wa matarsa fyade.

“A ranar 29 ga Afrilun 2022 da misalin karfe 11.30 na dare, wasu ‘yan ta’adda sun kai hari wani gida a Bandoko da zummar yi wa wata mata fyade bayan sun yi garkuwa da ita. Da alama ‘yan ta’addan suna bibiyar matar wadda take sayar da fura da nono kafin harin.

“Bayan sun fasa dakin matar sun shiga suka tarar da ita da maigidanta a kwance, daga nan suka sake lalen shirinsu na garguwa da fyade zuwa garkuwa don neman fansa, sannan suka bukaci maigidan ya mika musu mabudin babur dinsa.

“Bayan haka, sai suka bukace shi ya tube tufafinsa inda suka yi amfani da su wajen rufe masa ido kana suka daure masa hannuwa ta baya. Sannan suka dauko babur dinsa suka dauke shi suka gudu da shi zuwa dajin Gbadoko,” in ji Kakakin.

Ya ci gaba da cewa, “Bayan barayin sun tafi ne sai surukar matar ta yi ihun neman dauki lamarin da ya sa jama’a suka fito amma aka rasa wanda ya iya bin sawun barayin saboda tsoron watakila suna dauke da makamai.

“Nan da nan ‘yan kauyen suka hada kan ‘yan bangan yankin don bai wa jama’a kariya sannan suka sanar da jami’an tsaro abin da ya faru.

“Bayan da ‘yan sanda suka isa yankin ne ‘yan bangan suka nuna musu hanyar da barayin suka bi, daga nan su kuma suka bi sawun.

“Jam’ian sun iya gano mabuyar barayin a dajin Gbadoko da misalin karfe 5 na asuba na ranar 30 ga Afrilun 2022. Ganin ‘yan sanda ke da wuya, ‘yan ta’addan suka ranta a na-kare suka bar magidancin tare da babur dinsa da suka sato.

“Bayan wani lokaci jami’an sun samu nasarar kama daya daga cikin barayin mai suna Abdulrahman Lolo, daga bisani wani mai suna Mohammed Sanni shi ma ya shiga hannu,” in ji CSP Adejobi.

Jami’in ya ce duka su biyun da aka kama sun tabbatar wa ‘yan sanda sun aikata laifin da ake zarginsu da shi, kuma suna ci gaba da taimaka wa ‘yan sanda da muhimman bayanai.

Da yake yi wa ‘yan sanda bayani, Abdurahman Lolo ya ce, “Ni da wani Abubarka Baya makiyaya ne a kauye guda. Abubakar ne ya bukaci in raka shi zuwa wata rugar Fulani da ke kusa.

“Shirinmu shi ne mu yi garkuwa da wata mata don mu yi mata fyade, amma daga baya shirin ya sauya zuwa yin garkuwa da maigidan matar don neman fansa.

“Tocila da adda da kuma sanduna su ne abubuwan da muka rike amma babu bindiga. Wadanda muka kai harin tare akwai Sani da Abubakar da kuma Umar. Kuma dukkanmu yaran Alhaji Lolo na Gadam Mallam-Mamman ne.

“Sauran abokaina da na ambata sun saba zuwa sata, amma wannan shi ne karon farkon da aka tafi da ni. Aikin da aka dora mini shi ne lura da hanya da tura bayanai ga abokanmu da suka tsere a lokacin da ‘yan sanda suka fafare mu,” in ji Abubakar.

Magidancin da lamarin ya rutsa da shi, Jibril Saidu, ya ba da labarin yadda lamarin ya faru kafin zuwan jami’an tsaro.

A cewar Jibril Saidu, “Wani gungun mutanen da ba a san ko su wane ne ba suka shiga mini gida suka haska mini tocila a ido wanda hakan ya hana ni ganin wuri da kyau. Sun yi barazanar kashe ni da iyalina muddin ban ba su hadin kai ba.

“Sun tilasta ni tube tufafina kana suka karbe mubudin babur dina. Sai suka yi amfani da tufafin nawa wajen daure mini fuska da hannuwana ta baya.

“Sai suka ja ni suka fita da ni sannan suka dauke ni a kan babur din nawa suka kara gaba. Daga bisani jami’an IRT suka kubutar da ni,” in ji magidancin.