✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda dubun mai yi wa yara maza fyade ta cika

An kama wani matashi mai yi wa yara maza fyade ta hanyar luwadi.

An kama wani matashi da ya yi kaurin suna wurin yi wa kananan yara maza fyade ta hanyar luwadi.

’Yan sanda sun kama matashin wanda kuma dan tireda ne da bidiyo da kuma hotunan tsiraicin kananan yaran da ya yi fyade ta hanyar luwadi da su.

A ranar Alhamis ’yan sanda daga caji ofis din Makinde da ke Legas suka kama shi bayan wani saurayin da ya nemi yi wa fyade ya fallasa shi.

Kakakin ’yan sandan jihar, Muyiwa Adejobi, ya ce wanda ake zargin ya yaudari saurayin ne ya taso daga Abuja ya same shi a Legas, inda ya yi alkawarin sama masa sana’a ya kafa kansa.

Adejobi ya ce wanda ake zargin ne ya biya wa saurayin kudin mota daga Abuja har zuwa gidansa da ke Oshodi a Legas.

“Asirinsa ya tuno ne mako guda da zuwan bakon, lokacin da ya yi yunkurin zakke wa bakon ta baya da karfin tsiya.

“Bakon ya ki yarda ya kuma nemi tserewa ya koma Abuja, amma matashin ya rika dukan sa, lamarin da ya jawo hankalin makwabta suka kira ’yan sanda.

“Mai gidan da wanda ake zargin ke haya a ciki ya tabbatar cewa matashin ya saba irin wannan ta’asa, shi da kansa ya sha shiga tsakani kan mummunar dabi’an dan hayan,” inji kakakin ’yan sandan.

Ya ce Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Legas, Hakeem Odumosu ya yi tir da lamarin, ya kuma sa a mika batun ga Sashen Kula da Abubuwan da suka shafi jinsi domin kammala bincike da gurfanar da wanda ake zargin.