✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Dokar Hana Fita Ta Jefa Mutanen Jos Cikin Kunci

Gwamna Simon Lalong ya sassauta dokar ta sa'o'i 24 da ya ayyana ranar Lahadi


Domin sauke shirin latsa nan

Gwamna Simon Lalong na Jihar Filato ya sassauta dokar hana fita ta sa’o’i 24 da ya dora a kan Karamar Hukumar Jos ta Arewa tun ranar Lahadi.

Daukar matakin sassauta dokar, wadda yanzu za ta fara daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe, ya biyo bayan wata ganawar bita da gwamnan ya yi da shugabannin hukumomin tsaro a jihar.

Kafin sassauta dokar, shirin Najeriya a Yau ya yi nazari a kan halin da mutanen yankin suka tsinci kansu a ciki.