✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sassauta dokar hana fita a Kaduna da Zariya

Dokar hana fita ta koma daga ƙarfe 6 na yamma har zuwa 8 na safe a biranen Kaduna da Zariya

Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanar da sassauta dokar hana fita gaba ɗaya da ta sanya a garuruwan Kaduna da Zariya.

Daga yanzu dokar hana zirga-zirgar za ta fara aiki ne ƙarfe 6 na yamma zuwa 8 na safe.

Sanarwar da Kwamishinan Tsaron Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya fitar a daren Laraba ta ce sassaucin zai fara aiki ne a safiyar Alhamis.

Aruwan ya bayyana cewa sassaucin na nufin, jama’a na da damar gudanar da harkokinsu na yau da kullum tun daga ƙarfe 8 na safe har zuwa 6 na yamma.

Amma an haramta zirga-zirga daga ƙarfe 6 na yamma zuwa 8 na safe, kuma an umarci jami’an tsaro da su tabbatar da ganin cewa jama’a sun bi sabuwar dokar.

Ya ce an amince a sassauta dokar hana fitar ce a yayin zaman Majalisar Tsaron jihar, bayan ta tattauna kan yanayin da al’amura suke gudana a manyan garuruwan da aka sa dokar.

Jami’an tsaro, a cewarsa ba za su sassauta ba, wajen ɗaukar ƙwaƙƙwaran mataki kan duk wani al’amari da ke iya kawo tangarɗa a bangaren tsaron jihar.

Kwamishinan ya ce majalisar ta lura cewa al’amura sun daidaita daidai gwargwado, don haka ta cimma wannan matsaya.

A ranar Litinin 4 ga watan na na Agusta ne Gwamnatin Kaduna ta sanya dokar hana fita a garuruwan biyu bayan tarzomar da ta biyo bayan zanga-zangar yunwa da tsadar rayuwa da aka gudanar a faɗin Najeriya.