Gwamnatin Jigawa ta dage dokar hana fita a kananan hukumomi takwas da aka fasa shaguna da sace-sace a yayin zanga-zangar yunwa.
Kwamishinan yada labarai na jihar, Sagir Musa, ya bayyana cewa da dauki matakin ne a ranar Litinin bayan taron majalisar tsaron jihar wanda gwamna Umar Namadi ya jagoranta.
Da farko an sassauta dokar hana fita daga karfe 5 na safe zuwa karfe 9 na yamma a kananan hukumomin da abin ya shafa: Dutse, Kazaure, Gumel, Hadejia, Kiyawa, Birnin kudu, Babura, da Roni.
Sagir ya ce matakin ya biyo bayan nazarin yanayin tsaro da kananan hukumomin da abin ya shafa.
Ya ce yanzu kowa na iya harkokinsa cikin walwala ba tare da wani takura ba.
Sai dai ya bukaci al’ummar jihar da su kiyaye doka da oda domin ci gaban jihar.