✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda direba da yaron mota suka kone kurmus a Shika

A ranan Alhamis ta makon da ya gabata ne wata motar dakon man fetur ta fadi a garin Shika ta Karamar Hukumar Giwa a Jahar…

A ranan Alhamis ta makon da ya gabata ne wata motar dakon man fetur ta fadi a garin Shika ta Karamar Hukumar Giwa a Jahar Kaduna, inda direba da yaron motar suka kone kurmus a yayin da daya yaron motan ya shige daji cikin dimuwa, ba a same shi ba. Haka kuma gidaje bakwai sun kone kurmus.

Da faruwar hatsarin Aminiya ta ziyarce garin Shika, a inda ta tarar da hanyar da ta taso da ga Zariya zuwa Funtuwa ta toshe, sakamakon tashin gobara da tankar ta haddasa, wakilinmu ya ji ta bakin wadda motar ta fadi a kofar gidansa mai suna Yusuf Bala Tanimu Shika, inda ya ce gidaje bakwai ne suka kone a yayin gobarar.

“A kofar gidana ne motar ta fadi kamar yadda kake gani, kuma gidaje bakwai ne suka kone kurmus ba a fitar da komai a gidajen ba, sai dai mun yi sa’a babu hasarar rai a cikin gidajen da suka kone.

Haka kuma magidancin ya labarta wa Aminiya yadda hadarin ya faru, inda ya ce, “Shi mai tankar ya nemi kaucewa wani rami ne domin hanyar ta lalace, sai kawai bodin ya rinjaye shi sai ta kwanta, kwantawarta ke da wuya sai mai ya fara malala a kasa, sai kawai nan take ta kama da wuta ni ina bayan gida ina wanka sai na fito a gigice, hatta rigar jikin nan nawa da ka gani wani ya bani ita,” inji shi.

Motocin kashe gobara na ma’aikatu kusan shida ne suka kai gudumuwar kashe gobarar, kuma daya daga cikin ma’aikatan ya yiwa wakilinmu karin bayani kamar haka, “Sunana Isa Mohammed kuma jami’i ne na ma’aikatan kashe gobara na Jami’ar Ahmadu Bello dake Kongo, mun sami labarin faruwar lamarin, kuma har ma gidajen dake wurin sun kama da wuta, dan haka muka zo kuma cikin ikon Allah mun yi kokari wajen kashe wutar, sai dai har zuwa yanzu bamu san abin da ya haifar da hadarin ba, sai dai mun tabbatar da cewa direban motar da yaron motar duk sun kone, dan haka mutane biyu kenan suka kone a halin yanzu,” a cewarsa.

Al’umar garin na Shika wadanda gobarar ta shafa sun yi kira ga gwamnati da ta agaza musu, kasancewar duk kusan abin da suka mallaka sun kone kurmus, kuma wasu har ma da amfanin gonansu da suka fara kawowa gida duk sun kone.