Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya bayyana yadda ya ce dattawan Kudancin suka canza masa tunani a kan daukar Mataimakin Gwamna Kirista a Jihar.
Jaridar Premium Times ta rawaito cewa El-Rufa’i ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da littafi domin karrama kammala aiki na wanda ya kirkiri Kungiyar Kare Muradun Musulmai ta Najeriya (MURIC), Farfesa Ishaq Akintola.
El-Rufa’i, wanda ya mulki Kaduna har na tsawon shekara 8 daga 2015 zuwa 2023, ya kuma bayyana dalilinsa na daukar Mataimaki Musulmi, a maimakon Kiristan da aka saba dauka a Jihar.
Ya ce a wa’adinsa na farko, ya dauki tsohon abokinsa, Barnabas Bala Bantex, amma tun bai fi shekara biyu ba a ofis aka rika musguna masa, har sai da ya yi yunkurin sayka daga kujerar.
Tsohon Gwamnan ya ce wasu da suka kira kansu da dattawan Kudancin Kaduna ne suka rika fushi da shi saboda ya ki ya dauki Mataimaki daga jerin wasu sunaye da suka ba shi shawara.
Ya ce dattawan sun tsani Barnabas ne saboda ya fito daga wata karamar kabila ta Moroa, wacce ba ta da yawa a yankin, a maimakon kabilu irin su Atyap ko Bajju ko Jaba ko kuma Kagoro.
El-Rufa’i, ya ce, “Ni da Barnabas mun fuskanci karan tsana iri-iri daga wadannan dattawan, wadanda yankinsu ya kamata a ce yana wakilta. A shekaru uku na wa’adin farko na mulkina, sau uku yana yunkurin ajiya aiki.
“Da kyar ya samu ya kammala wa’adinmu na farko a daddafe, saboda kulle-kullen da suka yi masa, da kuma rashin lafiyarsa da ta motsa a wancan lokacin.
“Dag bisani kuma ya fadi takarar Sanatan da ya tsaya a shiyyar Kudancin Kaduna, bayan kamar shekara daya kuma da haka ya mutu.”
Tsohon Gwamnan ya ce abin da aka yi wa Barnanbas ne ya sa ya canza shawara a kan daukar Mataimakinsa a 2019.
Ya ce daga bisani ne ya yanke shawarar daukar Musulma, inda ya dauko Hadiza Balarabe, amma duk da haka dattawan ba su mayar da wukarsu cikin kube ba.