Wani dan hidimar kasa mai suna Afolabi Adefolarin da aka tura Jihar Adamawa, ya kirkiri fasahar amfani da hasken rana wajen samar da wutar lantarki. Dan asalin Jihar Oyo Adefolarin, mai shekara 24 ya ce dalilinsa na wannan kirkira shi ne yadda Jihar Adamawa ke da yawan zafin rana, hakan ya sanya ya yi amfani da yanayin wajen amfani da hasken rana don samar da wutar lantarki tare da yin na’urar bada wutar lantarki a gidaje.
Ya ce ya bude wajen da yake koyar da matasa yadda ake amfani da wannan kirkira domin samar da wutar lantarki.
Afolabi ya ce kasancewar ya karanci injiniyancin fannin wutar lantarki hakan ya taimaka masa wajen samun ilimi a wannan fanni.
Ya ce amfani da hasken rana wajen samar da lantarki shi ne irin lantarkin da za a yi rika amfani da shi nan gaba.
“Za a zo lokacin da wadannan hanyoyin samar da wutar lantarki na yanzu za su gushe,” inji shi.
“Tunda muna da isasshiyar hasken rana a Jihar Adamawa, ina son ganin yadda matasa za su amfana da wannan ilimi da na samu domin su samar wa kansu wutar lantarki. Mun koyar da dalibai da dama daga makarantu takwas da ’yan hidimar kasa da marasa aikin yi a nan jihar,” inji Afolabi.
Ya ce rashin isasshiyar wutar lantarki, na sanya wasu harkokin kasuwanci gurguncewa. Ya ce don kawo karshen wadannan matsaloli, ya sa yake koyar da matasa wannan kirkirar domin samun mafita a duk inda suka tsinci kawunansu.
“Najeriyar yanzu ba kamar Najeriyar da ba ce, domin sai an gama karatun ake koyon aiki. Amma a da ana koyon aiki ne kafin a fara karatu. A kasar nan ba lallai ba ne takardar karatu ta samar maka da aikin yi, sai dai aikin hannun da ka koya,” inji shi.
Ya bukaci matasa su koyi aikin hannu; sa’annan su kasance masu aiki da abin da suka koya.
Shugabar wurin koyar da matasa aikin hannu, Misis Jummai Kwache ta ce, Afolabi ya yi aikin hidimar kasarsa ce a wajensu sannan ya taimaka wa wadansu ’yan hidimar kasar kan ayyukan hannu irin nasa har ya gano cewa yana yin na’urar yada wutar lantarki idan an dauke wuta a cikin gida (Inverters). Na sayi daya daga cikin na’urorin kuma tana amfani sosai akalla na yi amfani da ita yanzu tsawon wata shida zuwa bakwai,’ inji ta.
Ta ce ta amfana da na’urar sosai ba kamar amfani da janareta ba wanda ake kashe kudin man fetur. Ta ce wannan daga rana ta haska za ta fara daukar caji ga rashin damun makwabta, kuma ko ’ya’yanta na iya kunna ta cikin sauki.
Misis Kwache, ta ce: “Ina amfani da ita na’urar na tsawon sa’o’i takwas a kullum, takan dauke ni kwana uku ina amfani da ita kafin ta bukaci sabon caji. Akwai ilimantarwar da muke yi ga wadanda suke zuwa hidimar kasa, mun dauke shi a matsayin mai ilimantar da su a wannan fanni na kirkirar.”
“Mukan hada gwiwa da matasa a nan Jihar Adamawa saboda su amfana saboda rashin issashiyar wutar lantarki a jihar,” inji ta.
Misis Kwache ta kara da cewa, akalla matasa 20 ne suka amfana daga wannan ilimi, inda suke neman musu tallafi daga Bankin Masana’antu (BoI) domin samar musu da rancan kudi don gudanar da ayyukansu.
Daya daga cikin ’yan hidimar kasar da Afolabi ya koyar, mai suna Emmanuel Efe, ya ce: “A lokacin da aka zo koyar da mu ilimin amfani da wannan fasahar nan take na ji ina son koyon irin wannan ilimi. Kuma da ya gama koyar da mu sai da na bukaci ganinsa domin ya kara min haske a kan wannan ilimi.”
Ya nuna farin cikinsa game da wannan fasahar da ya samu, sa’annan ya dauki alkawarin nakaltar fasahar, har sai ya kware domin cimma burinsa wajen ganin ya zama tsayayye a wannan fanni.