Wani dan Boko Haram da ya nemi tursasa wa mahaifinsa, Alhaji Adamu Kwaramtcheri ya shiga kungiyar ya kashe shi a garin Muktum da ke karamar Hukumar Gujba, Jihar Yobe.
Hakan ya faru ne a daren Litinin da ta gabata, inda yaron tare da wasu ’yan Boko Haram uku suka yi wa kauyen Muktum din kawanya da misalin karfe 11:35 na dare. Mutanen kauyen sun tabbatar wa Aminiya cewar babban dan mamacin, Ndotti Alhaji Adamu da dan rikonsa, Bukar Kawu Adamu na daga cikin wadanda suka yi aika-aikar.
Malam Usman Kura, mazauni garin ya bayyana wa wakilinmu cewa daga cikin ’yan Boko Haram din an gane fuskar dansa. Ya kara da cewa yaran sun same shi ne a bisa gadonsa yana kwance, inda suka yi masa harbi hudu a kirji kafin suka ci gaba da harbin iska.
Kakakin ’yan sanda a Jihar Yobe, DSP Zubairu Jafiya ya tabbatar da kisan, inda ya bayyana wa Aminiya cewa ’yan ta’addan su hudu sun zo da bindigogi suka tsorata mutanen garin, kafin su aiwatar da kisan. “Har yanzu ba mu kama kowa ba, amma ana kan tsananta bincike kan hakan,” inji Kakakin na ’yan sanda.
Wani mazauni garin da ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana wa Aminiya cewar yaron mai suna Ndotti Alhaji Adamu, ya shiga kungiyar ce yana kimanin shekara 16 tare da yaron da maihaifin nasa ya rika.
“Babu yadda maihaifin bai yi ba don ganin ya saita tarbiyar yaron amma abin ya ci tura. Ya ki yin ilimin addinin Musulunci balle na Boko. Daga baya sai ya shiga kungiyar Boko Haram.
“Daga bisani suka zo domin tafiya da mahaifin nasu amma ya guda zuwa wani gari amma daga baya suka bi shi har can. Allah Ya taimake shi ya tsira da ransa amma suka kona masa mota da gidansa.”
Malamin ya ci gaba da cewa: “Daga bisani Alhaji Kwaramtcheri ya dawo kauyen Muktum ya ci gaba da noma da dillancin dabbobi, kafin yaran suka kashe shi.”
Sai dai wani dan uwan mamacin da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce Alhaji Adamu Kwaramtcheri ya mutu yana da mata biyu da ’ya’ya maza da mata da bai fadi adadinsu.
Haka kuma ya ce, Ndotti shi ne dan mamacin na farko. “Mahaifinsa dan siyasa ne, ya yi Kansilan riko na kimanin wata shida a lokacin Gwamna Mamman Ali. Ya taba gaya mani cewa yaran suna zarginsa da tona masu asiri wajen jami’an tsaro, wanda haka ya sa suke bibiyar ransa. Amma, hakan bai hana shi dawowa kauyen ba saboda a nan yake neman abincin da zai ciyar da iyalinsa.”
Tuni dai wasu daga cikin mutanen garin Muktum suka fara gudun hijira zuwa makwabtan garuruwan da ke da cikakken tsaro a wannan yanki.