✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda dakunan kwanan daliban jami’o’in gwamnati suka lalace

Sun yi matukar lalacewa gami da karancin abubuwan jin dadin rayuwa.

Dakunan kwanan dalibai a jami’o’in Najeriya da dama mallakin gwamnati sun yi matukar lalacewa sakamakon karancin abubuwan jin dadin rayuwa, kamar wutar lantarki da ruwan sha.

Wasu daga cikinsu ma ba su dace da muhallin dan Adam ba, sadoda karancin tsaftarsu da lalatattun ban-dakuna da karancin kula da su.

Dalibai da dama ba suna zama a cikinsu ne saboda ba su da wani zabi, duk kuwa da irin munin halin da suke ciki.

Wakilan Aminiya sun zagaya don tattaunawa da daliban wasu jami’o’i don jin korafe-korafensu a kan lamarin.

– Ban-dakuna a Jami’ar Jos sun yi matukar lalacewa

A Jami’ar Jos da ke Jihar Filato, daga waje, bandakunan daliban tsaftsaf suke, amma suna cike da kazanta daga ciki.

Dakunan dalibai ma suna fama da rashin tsafta saboda karancin ruwa.

A tattaunawarsu da wakilinmu, wadansu daga cikin daliban sun ce galibi matsalolin da ake fama da su daga cikin dakunan ne.

A lokacin da wakilinmu ya ziyarci dakin kwanan dalibai na Naraguta da ke jami’ar, daliban sun shaida masa cewa ban-dakunan cike suke da kazanta.

Wani dalibi a jami’ar da ya nemi a sakaya sunansa ya ce ruwa ba ya zuwa saman benen wanda ke da hawa uku, saboda famfunan wajen ba su da bututun da ke kai musu ruwa sama.

Hakan a cewarsa ya tilasta wa daliban dole su sauka kasa kafin su samu ruwan.

“Kamar mu da muke saman bene, ba ma samun ruwa saboda famfuna ba sa kai ruwa sama, wannan ne babban kalubalenmu.

“Kodayaushe sai mun sauko kasa muke samun ruwa, lamarin babu sauki ko kadan.

“Wannan ne ya sa ban-dakunanmu suke cikin yanayin kazanta, ko da kuwa masu shara sun wanke su,” inji dalibin.

A dakin kwanan dalibai na Village kuwa, wasu daga cikin ban-dakunan suna cikin yanayi mai kyau, wasu kuma suna fama da kalubalen rashin ruwa.

Wani dalibi ya shaida wa wakilinmu cewa ba su da wani zabi face su yi amfani da su a yadda suke.

“Duk da yake akwai ruwa a cikin dakunan, amma ba ya zuwa cikin ban-dakunan,” inji shi.

Sun yi kira ga hukumomin jami’ar su gyara matsalolin kafin lamarin ya kara tabarbarewa.

– Jami’ar Tarayya da ke Lakwaja ma sammakal

A Jami’ar Tarayya da ke Lakwaja a Jihar Kogi ma lamarin kusan daya ne da na Jos, inda wakilinmu ya gano cewa dakunan kwanan dalibai na Adankolo sun yi matukar lalacewa, amma yanzu haka ana aikin gyara su.

Sakamakon haka, shafin intanet din da dalibai kan ziyarta don samun dakuna ya kasance ba ya aiki har sai abin da hali ya yi.

Sai dai babu wani tanadi da aka yi wa kowane dalibi a zangon karatu na bana, ko da yake jami’ar ta ce tana iyakar kokarinta wajen ganin ta kammala aikin a cikin kankanin lokaci.

Injiniya Patrick Umeh, wanda ke aiki a Sashen Kula da Gyaran Dakuna na Jami’ar ya ta’allaka halin da dakunan suke ciki da rashin kula da su daga daliban.

Kazalika Patrick ya ce dalibai sun lalata kusan dukkan makullai da kofofi, yayin da akasarin rufin dakunan suke bukatar kwaskwarima.

Ya ba da tabbacin cewa sashen nasu zai ci gaba da aikin gyaran zuwa dakunan Felele da zarar an fitar da kudin yin aikin.

– Dakunan dalibai a jami’o’in da ke Binuwai suna cikin garari

Dakunan kwanan dalibai an Jami’ar Jihar Binuwai (BSU) ba wai suna cikin yanayi mara kyau ba ne kawai, suna kuma fama da matsalar cinkoso.

A tattaunawarsu da wakilinmu, wadansu daga cikin daliban da ba su amince a ambaci sunansu ba sun ce sababbin dakunan suna cikin yanayi mai kyau, amma tsofaffin suna fama da matsala mai yawa.

Wani dalibi da yake aji biyu ya ce, “Muna da dakuna masu kyau, amma suna da matukar tsada.

“Amma wanda nake zaune a ciki ba ya da kyau, akwai ma wadanda sun fi shi lalacewa.”

Dalibai da dama a Jami’ar Joseph Sarwuan Tarka da ke, Makurdi babban birnin jihar (JOSTUM) sun koka kan yanayin da dakunan nasu suke ciki.

Wakiliyarmu ta gano cewa baya ga dakunan dalibai na Suswan da aka gina shekara shida da suka gabata da suke cikin yanayi mai kyau, ragowar suna bukatar gyara.

Wata daliba da ba ta amince a bayyana sunanta ba, ta ce yanayin tsaftar dakunan ya kara tabarbarewa matuka.

“Mazauna dakunan nan har a cikin leda suke yin kashi, gaskiya akwai kazanta sosai a cikinsu,” inji dalibar.

Shi ma wani dalibi ya ce matsalar ta fi kamari ne musamman lokacin damina saboda sharar da take taruwa tare da barazanar yaduwar cututtuka.

“Dakunan ba su da tsafta, musamman ban-dakuna da wuraren wanka,” inji dalibin.

“Tagoginsu sun karairaye sosai ta yadda dole sai dalibai sun nema wa kansu hanyoyin toshe su saboda hana sanyi da ruwan sama shiga dakunan.

“Wasu daga cikin ragar da suke jikin tagogin kuma sun yayyage, sauro ya zama abokin zamanmu,” inji shi.

– Karancin ruwa da wutar lantarki ya addabi daliban Jami’ar Bayero

Wata daliba da ke aji uku a Jami’ar Bayero da ke Kano (an boye sunanta), wacce take karatu a Sashen Yada Labarai da Aikin Jarida kuma take zaune a dakin Asiya Bayero ta ce, “Wasu daga cikin hanyoyin ruwa da na ban-dakunanmu duk sun tottoshe.

“Gaskiya akwai karancin kula da dakunanmu, wasu daga cikin kwayayen lantarkinmu da soket-soket dinsu da fankoki a dakuna da dama duk sun lalace.

“Ko da masu gyara sun zo sun gyara ba a jimawa suke sake lalacewa.

“Kai akwai dakunan da ma kayayyakin lantarkinsu sam ba sa aiki.

“Yanzu a ’yan kwanakin nan ma samun wutar ya zama sai addu’a, lamarin kullum kara tabarbarewa yake yi.

“Babu ruwa, babu wuta; Ana kawo mana wuta ce kawai na wasu ’yan sa’o’i lokacin da ake kunna injin janareta da dare, inda a wannan lokaci ne ake samu a turo ruwa, wanda kuma ba ya wuce sa’a 15 shi ma yake karewa.

“Ala tilas wadansu sai dai su hakura da ruwa saboda dogon layin da ake fuskanta a famfuna,” inji dalibar.

Shi ma wani dalibi da ke aji uku a Sashen Kimiyyar Siyasa na jami’ar, wanda ke zaune a dakunan kwanan dalibai na Aliko Dangote, ya yi korafi a kan cinkoson dalibai a dakunan da karancin tsaftar ban-dakunansu.

“Daliban BUK masu zama a cikin dakunan dalibai na makaranta suna cikin mawuyacin hali.

“Da dare ne kawai muke samun wuta in aka kunna janareta.

“A zahirin gaskiya ma wannan ne ummulhaba’isin matsalar ruwan da muke fuskanta,” inji shi.