✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda daɗin zama ke haɗa auratayya tsakanin ’yan Arewa da ƙabilun Kuros Riba

’Yan asalin Arewacin Nijeriya sun fara zuwa Jihar Kuros Riba ne lokacin tana hade da Jihar Akwa Ibom.

Kamar yadda masu azancin magana ke cewa, “zamani riga”, haka za a iya cewa dangane da yadda zamantakewa tsakanin ’yan Arewa da kuma ’yan asalin Jihar Kuros Riba ta hanyar auratayya da kasuwanci ya mayar da al’ummun biyu tamkar Danjuma da Danjummai.

’Yan asalin Arewacin Nijeriya sun fara zuwa Jihar Kuros Riba ne lokacin tana hade da Jihar Akwa Ibom kuma ana kiran ta a waccan lokaci da Jihar Kudu Maso Gabas, inda kuma suke zuwa garin Kalaba don fatauci, suna komawa gida.

Ta jihar ce dai ’yan Arewan suke ketarawa kasashen Jamhuriyar Kamaru da ta Tsakiyar Afrika, wato birnin Malabo na kasar Angola domin yin kasuwanci da kamun kifi da kuma yin Farauta.

Farkon garin da ’yan Arewa suka fara zama shi ne Gadar Raga, wanda wata mahada ce da ke da kogi da wadataccen wajen kiwo domin shayar da dabbobi da kuma ciyar da su.

Alhaji Kasimu Ali Haruna shi ne Sarkin Hausawan Obudu ya bayyana wa wakilinmu da ya kai ziyarar gani da ido zuwa garin yadda kakanninsu suka tare a wurin bayan sun baro Arewa.

“Lokacin da kakanninmu suka yi kaura daga Bauchi suka zo nan mafarauta ne kuma akwai mahauta da masunta da suka hadu suka zauna a nan Gadar Raga.

“Masu farauta na tafiya farautarsu ta kama giwa wato farautar giwa, suna cire haurenta. Naman kuma su ba sarki da sauran kabilun da suke kewaye da su kyauta.

“Da garin ya bunkasa sai sarkin Obudu na wancan lokaci ya kira shugaban Hausawa ya kuma ce da shi, tunda mutanenka nata kara karuwa ku dawo nan kusa, ku zauna, ku ci gaba da harkokinku,” inji shi.

Sarkin ya kuma ce, wannan unguwar tamu ta ’yan Arewa inda suke yanzu tun gwamnatocin baya aka ware musu ita, wanda ya samo asali daga kyautar da wanccan Sarkin na Obudu ya yi musu,yana mai nuni da hannunsa yadda girman wurin yake yana cewa, “nan duk inda ka gani fadin da yawan unguwar nan tamu ce,” in ji shi.

Baya ga noma da kiwo da kuma kasuwanci, ’yan Arewa suna wasu sana’o’i da suka gada daga iyaye da kakanni kuma suka yi fice da ita har ta jawo musu kima da martaba a wajen sauran kabiliun wajen. Daya daga cikinsu ita ce sana’ar fawa.

Alhaji Lawan Katsina shi ne Sarkin Fawan Apiapum daya daga cikin garuruwan na yankin da ’yan Arewa ke gudanar da harkokinsu, ya fada wa Aminiya asalin yadda aka yi suka samu karbuwa har ta kai ga auratayya.

“Kakanninmu da suka zo nan sun samu kabilun nan ba su iya fidar dabba ba, komai girmanta kuma komai kankantar.

“Babbakewa kawai suka iya, kuma ba sa yanka, domin karfe suke samu mai nauyin gaske su buga mata a ka, dabbar ta tadi tana shure-shure har sai ta mutu sannan su babbake ta.

“Bayan zuwan Musulmai ’yan Arewa sai suka ga yadda suke yanka dabba su fede, da haka suka koya a wurin kakanninmu da iyayenmu har ga shi yau ta kai lokacinmu,” in ji shi.

Baya da garin Ogoja da akwai Igoli da Ugep da kuma Ikom wasu daga cikin manyan garurunwan da ’yan Arewa ke zaune suke kuma da kyakkyawar ma’amala ta zamantakewa da ta kai ga auratayya.

Hakan kuwa ya faru ne kasancewar rashin samun tangarda a duk irin kasuwanci da dan Arewa yake yi na goro ne ko manja ko kuma wata sana’a kamar fawa yadda ta kai idan taku ta zo daya da dan kabilar yankin zai iya ba ka kudi ka juya bisa zuwa wani lokaci.

A bangaren auratayya kuna mazansu na auren ’yan Arewa haka ma matansu, musamman idan mace ta karbi Musulunci.

Wannan zama da mu’amalla mai kyau da kuma kasuwanci da noma da kiwon da ’yan Arewa ke yi a Obudu ta sa auratayya ta shiga tsakanin kabilun da kuma bakin nasu.

“Akwai wasu iyalan da Allah Ya nufe su da karbar addinin Musulunci suka kuma auri Musulmi har suka hayayyafa.

“Idan suka Musulunta, suna da kokarin rike addinin kuma babu wata matsala ta zamantakewa ko wani tashin hankali,” in ji Sarkin Sarkin Hausawan Obudu.