✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati ta soma ɗaukar mataki kan fim ɗin wulaƙanta Hijabi

Bincikenmu ya nuna cewa ba a fitar da fim ɗin a kasuwa ba balle a miƙa shi don tantacewa.

Hukumar tace finafina ta Nijeriya (NFVCB) ta ce ta karɓi ƙorafe-ƙorafe game da wani fim da ake shirin fitarwa, wanda aka yi amfani da Hijabi wajen nuna wasu munanan halaye.

Hukumar NFVCB ta ce ba za ta amince da ayyukan da ke zubar da ƙima ko darajar wani addini ko al’ada ko kuma ƙabila ba a finafinai da ake shiryawa a ƙasar.

Hukumar ta bayyana haka ne bayan wasu ’yan ƙasar musamman waɗanda ke amfani da shafukan sada zumunta sun yi ta korafe-korafe game da wani fim da ake shirin fitarwa a ƙasar inda aka yi amfani da Hijabi wajen nuna munanan halaye.

Jaridar Punch ya ruwaito cewa, a bayan an rika tayar da jijiyoyin wuya musamman a tsakanin al’ummar Musulmi bayan wata fitacciyar jarumar a Nollywood, Nancy Isime ta wallafa fastar wani fim ranar Litinin a shafinta na Instagram.

Fastar fim din dai na dauke da hotunan wasu mutane sanye da hijibi da nikabi mai nuna alamar suna aikata mummunan aiki.

Tuni dai Kungiyar Musulmi ta MURIC cikin wata sanarwa da shugabanta, Farfesa Ishaq Akintola ya fitar a ranar Alhamis, ta yi kira da a gaggauta haramta fim da ke shirin fitowa.

Kungiyar MURIC ta bayyana fim din a matsayin shaidanci da ya nuna mata musulmi suna aikata fasadi wanda kuma hakan yana harzuka jama’a.

Bayyana fastar fim din dai ta haifar da zazzafar muhawara a shafukan sada zumunta inda mafi yawan mutane musamman Musulmai suka yi ta sukar fim ɗin, suna masu kira ga NFVCB da furodusoshin shirin kan su mutunta addinin Musulunci wajen cire duk wani wuri da aka nuna Hijabi a yanayi mara kyau.

Sai dai cikin sanarwar da Darakta-Janar na Hukumar NFVCB, Shuabu Husseini ya fitar da yammacin ranar Alhamis, ya bayyana cewa tuni sun tuntubi masu shirya fim din dangane da wannan lamari.

A sanarwar da NFVCB ta fitar ta bayyana cewa ta ƙarbi ƙorafe-ƙorafe game da batun kuma tuni ta soma ɗaukar mataki.

Hukumar ta ce “bincikenmu ya nuna cewa ba a fitar da fim ɗin a kasuwa ba balle a miƙa shi ga NFVCB don tantacewa kamar yadda doka da kuma tsare-tsarenmu suka tanadar, duk da haka mun samu damar isa ga masu furodusoshin fim ɗin kuma mun ɗauki matakai don magance ƙorefe-ƙorefen al’umma game da shirinsu.”

Ta ƙara da cewa “NFVCB ba za ta bar duk wani fim ko bidiyo, ciki har da gajerun bidiyoyi da ya zagi ko wulaƙanta duk wani addini ko al’ada ko ƙabila ba.

“Za mu ci gaba da sadaukar da ayyukanmu don samar da ingantaccen canji a tsakanin al’ummar Nijeriya ta hanyar tace finafinai da shirye-shiryen bidiyo,” in ji hukumar.

NFVCB ta ce, “Manufarmu ita ce samar da daidaito tare da kiyaye ’yancin faɗin albarkacin baki kamar yadda doka ta tanadar tare da rage take haƙƙi a zamantakewa da al’adu kuma da addini da finafinai ke haifarwa.”