✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda cikina wata bakwai ya bace

Wata matar aure mai shekaru 35 da haihuwa, mai suna Halima Dogara da ta fito daga garin Gure a karamar Hukumar Lere da ke Jihar…

Halima Dogara da Mijinta Dogara Jauga KadafiWata matar aure mai shekaru 35 da haihuwa, mai suna Halima Dogara da ta fito daga garin Gure a karamar Hukumar Lere da ke Jihar Kaduna, ta nemi cikin da take dauke da shi mai watanni bakwai ta rasa ba tare ta yi bari ba.
Da take yi wa wakilinmu karin bayani kan yadda wannan al’amari ya faru, Halima Dogara, wadda take karatu a kwalejin ilmi ta tarayya da ke Zariya, ta bayyana cewa, ‘’ainihin abin da ya faru shi ne, na samu juna biyu tun a watan daya(Janairu), amma bayan da aka kai watan bakwai (Yuli) sai na ji Ba na jin motsin wannan ciki nawa. Wannan abu ya faru ne a ranar 6 ga watan bakwai (Yuli) da ya gabata a garin Zariya.
Ta ci gaba da cewa, ‘bayan da na dawo daga rubuta jarabawa a makaranta na tube kayana sai na ga cikina ya sauka kasa, na danna ban ga alamar yaro ba, na zauna sai na ji ba na jin komai. Sai na samu wata anty na ce mata a gaskiya ban gane ba wannan ciki nawa kamar babu komai. Sai ta ce ita ma ta ga kamar babu komai ta ga cikin ya sauka.’’
Halima Dogara ta kara da cewa,  ‘’Da na dawo gida nan Gure sai na je wani karamin asibiti,  domin a wannan asibitin ne nake yin awo tun da aka yi mani awo aka ce ina da ciki. Don haka a duk lokacin da na ji wata damuwa nakan je wajen likitan asibitin kuma ya kan duba mini cikin ya ce mini yaro yana nan lafiya.’’
Ta ce, ‘’a wannan lokacin da naje da ya duba ni sai na ga ya yi shiru, sai na ce masa yaya? sai ya ce mini shi bai ji alamar cikin ba. Sai na ce masa to yaya za a yi ke nan? sai ya ce bari ya debi jinina ya bincika, bayan awa biyu in dawo, domin in ji sakamakon binciken da zai yi, idan ma da cikin zai gani, idan kuma babu zai gani,’’ inji ta.
Ta kara da cewa, ‘’daga nan da na dawo makaranta a Zariya sai na je  wajen wani likita da yake yin hoto a Samuru  ya yi mun hoton cikin, sai ya ce mini shi bai ga komai ba,  kuma komai nawa yana nan daidai, shi bai ga komai ba. Ta ce tun daga lokacin da wannan abu ya faru har ya zuwa wannanlokaci  ba ta jin zafin  komai a jikinta.
Haka kuma ta ce tun a watan biyar ta je babban asibitin Saminaka  suka yi mata awo,  su ma suka tabbatar mata cewa tana da ciki wata biyar. Kuma suka ce mata idan cikin ya cika wata tara ta dawo domin a yi mata aiki, domin ita dama ba ta haihuwa da kanta. ‘’Duk haihuwar da na yi guda biyu tiyata aka yi mini aka fitar da yaron a asibitin Saminaka. Kuma  duk wannan  tiyata da aka yi an cire mini yara maza guda biyu kuma  dukkansu suna nan a raye,’’ inji ta.
Halima Dogara ta bayana cewa a lokacin da wannan abu ya faru ta damu sosai, ta rasa abin da yake yi mata dadi, amma daga baya ta yi hakuri ta mika komai ga Allah.
Shi ma da yake zantawa da wakilinmu, mijin wannan mata, Dogara Jauga Kadafi ya bayyana cewa, ‘’a gaskiya wannan abu da ya faru ya yi matukar ba ni mamaki da tsoro. Domin a ce ciki wata bakwai amma a wayi gari babu wannan ciki, babu zubar da jinni, babu wani ciwo, wannan abu yana da ban mamaki.’’
Ya ce, ‘’a gaskiya ina cike da bakin ciki kwarai da gaske da faruwar wannan al’amari, domin aurena da wannan mata a bana shekara goma ke nan. Mun yi shekaru biyar ba ta samu haihuwa ba, bayan shekara biyar muka fara samun haihuwa, a inda ta haihu sau biyu, muka samu yara guda biyu maza. Sai a wannan na uku ne aka samu wannan al’amari Allah bai nufa za ta haihu ba. Don haka na mika komi ga Allah a kan wannan al’amari.’’
Wakilinmu ya tuntubi babban lilkitan babban asibitin Saminaka Dokta Iliya Bulus kan ko a tsarin likitanci irin na zamani irin wannan al’amari zai iya faruwa, sai ya ce a tsarin ilmin likitanci na zamani irin wannan abu ba zai iya faruwa ba, domin a tsarin likitanci idan  an tabbatar da mace  tana da ciki to babu yadda za a yi a ce an nemi cikin nan an rasa ba tare da an haife shi ba ko kuma an yi barinsa. Ya ce sai dai cikin ya makale amma ba a nemi shi a rasa ba, in dai har akwai cikin.
Dokta Iliya ya bayana cewa, shi da kansa ya taba  cire wa wata mata ciki da ya yi shekaru bakwai a cikinta, a shekarar 2008 a wani asibiti mai suna Zugwai  a garin Kafanchan.  Don haka  ya ce wannan abu  ba zai iya faruwa ba a tsarin ilmin likitanci.
Daga nan sai ya yi kira ga mata masu ciki da zarar sun ga ba su ga al’ada ba su tafi asibiti a duba su a fara yi masu awo, a yi masu hoto har sau uku kafin su haihu.