Babban Bankin Najeriya (CBN) ya jefa ’yan Najeriya cikin rudani bayan ya fitar da sanarwa masu cin karo da juna kan ci gaba a karbar tsoffin takardun N500 da N1,000 cikin dan kankanin lokaci.
CBN ya lashe amansa ne bayan manyan bankunan kasuwanci irinsu UBA da First Bank sun tura wa abokan huldarsu sakonni cewa za su ci gaba da karbar tsoffin takardun N500 da N1,000.
- Tsoffin kudi: ’Yan Kaduna sun yi watsi da El-Rufai
- Masu tsoffin kudi sun yi wa CBN cikar kwari a Legas
Bankunan sun yi haka ne bayan wata sanarwar da kakakin CBN, Osita Nwanisobi, da ke umartar su da karbar kudin matukar ba su wuce N500,000 ba.
Sakonsa ga ga bankunan ya ce,
“Hukunar gudanarwar CBN ta umarce ni in sanar da bankunan kasuwanci cewa su fara karbar tsoffin takardun N500 da N1,000 daga hannun kwastomominsu nan take.
“Kwastoma zai iya kai har N500,000 bankin kasuwanci, amma abin da ya haura hakan sai dai ya kai ofishin CBN.
“Don haka ana bukatar ku bi wannan umarnin,” in ji wasikar farko da babban bankin ya aike wa manajojin reshe da ayyukan bankunan kasuwancin.
Bayan fitowar wasikar, ’yan jarida sun tuntubi Mista Nwanisobi, game da ita, wanda ya tabbatar musu da sahihancinta.
Sakon da First Bank ya aike wa kwastomominsa ya ce, “Rassanmu za su ci gaba da karbar tsoffin takardun N500 da N1,000 da ba su wuce N500,000 ba daga hannun mutanen da suka yi rajista a shafin CBN.
“Duk wanda ke da tsoffin takardun kudin da suka haura N500,000 ya kai ofishin CBN mafi kusa
“Muna kuma sanar da ku cewa za mu bude rassanmu gobe Asabar 18 ga Fabrairu, 2023.”
Shi ma bankin UBA ya tura irin wannan sako ga kwastomominsa kamar haka: “Ba mu daina amsar tsoffin takardun N500 da N1,000 ba, matukar ba su haura N500,000 ba.
“Gobe Asabar ofisoshinmu za su kasance a bude domin ci gaba da karbar tsoffin takardun kudin.”
Bankunan sun tura sakonnin ne a ranar Juma’a.
Amma kafin a jima, bayan kafofin watsa labarai su wallafa labarin, sai CBN ya fitar da wata sabuwar sanarwa, yana karyata umarninsa na farko da ya baiwa bankuna su ci gaba da karbar tsofaffin N500 da N1000.
A sabuwar sanarwar, kakakin na CBN ya zargi kafofin watsa labarai da yada labarin karya — wato sanarwarsa ta farko wadda shi da kansa ya tabbatar musu da sahihancinta.
Sakon na biyu ya ce, “Mun lura da wani labari mara tushe da ke yawo a kafofin yada labarai cewa CBN ya umarci bankunan kasuwanci da su ci gaba da karbar tsoffin takardun kudi na N500 da N1,000.
“ To a sani cewa, kamar yadda Shugaban Kasa ya ba da umarni, tsoffin takardun kudi da za a ci gaba da amfani da su, su ne N200 na tsawon kwana 60 zuwa ranar 10 ga watan Afrilu.”
A kan haka ne First Bank ya goge sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Wannan dambarwar ta zo ne washegarin jawabin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, inda ya ba da umarnin a ci gaba da amfani da tsoffin takardun Naira 200 tare da sabbin takardun Naira 200, 500 da kuma 1,000 har zuwa 10 ga watan Afrilu, ranar da tsohuwar 200 za ta daina aiki.
Buhari ya sanar da haka ne a jawabinsa ga ’yan Najeriya da ke ci gaba da surutu kan sauyin takardun kudin da CBN ya yi, da kuma karancin sabbin da ya jefa su cikin damuwa.
Hannu guda kuma gwamnatocin was jihohi sun maka Gwamnatin Tarayya a Kotun Koli suna neman ta soke dokar haramta amfani da tsoffin kudin.
Batun karancin sabbin takardun kudin dai ya jefa ’yan Najeriya cikin kunci, har da asarar rayuka.
A wasu jihohin Kudu abin ya kai ga tarzoma da kona bankuna.