✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Buhari zai yi godiya da shukura ga Allah

Daga Hudubar Imam Sharfuddeen Abdussalam Aligan Masallacin NASFAT na Kasa Abuja Godiya ta tabbata ga Allah Wanda Yake halitta kuma Ya yi zabi, Shi ne…

Daga Hudubar Imam Sharfuddeen Abdussalam Aligan

Masallacin NASFAT na Kasa Abuja

Godiya ta tabbata ga Allah Wanda Yake halitta kuma Ya yi zabi, Shi ne Mai buwayya da karfi da mulki da malakuti. Godiya ta tabbata ga Allah Makagin halittar samma da kasa, Mai sanya mala’iku a matsayin mazanni ma’abuta fika-fikai bibbiyu da uku-uku da hurhudu, Yana karawa a cikin halittta abin da Ya so, lallai ne Allah a kan komai Mai iko ne.

Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai Yake ba Ya da abokin tarayya a gare Shi, Shi ked a al’amari a gabani da baya. Kuma na shaida cewa lallai Shugabanmu Masoyinmu Jagoranmu, Abin koyinmu Maulanmu Annabi Muhammad BawanSa ne kuma ManzonSa. Ya Ubangiji! Ka kara salati da taslimi a gare shi, salatin da za Ka bude mana kofofin yarda da sauki, Ka rufe mana kofofin sharri da tsanani, kuma Ka kasance mana da ita Majibinci Mai taimako. Kai ne Majibincinmu, kuma Maulanmu, madallah da Maulanmu, madallah da Mai taimako.

Ya bayin Allah! Ku bi Allah da takawa ku bauta maSa ku yi shukura gare Shi, kada ku butulce maSa. Ku sani kyakkyawar karshe ta masu  takawa ce, kuma akibar al’amura naSa ne.

Ya bayin Allah! Hudubarmu ta yau tana magana ce a kan hakikanin shukura da godiya bayan samun nasarar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a zabe da kuma abin da zai biyo bayan nasarar.

Ya bayin Allah! Ba makawa a yi godiya ga Allah Azza wa Jallah. Allah Madaukaki Ya ce: “Ku tuna Ni, In tuna ku, ku yi Min shukura kada ku butulce Min.” (Bakara: 52). Kuma Madaukaki Ya ce: “Ya ku wadanda suka yi imani! Ku ci daga kyawawan abubuwan da Muka azurta ku, kuma ku yi shukura ga Allah, idan kun kasance gare Shi kuke yin bauta.” (Bakara: 172).

’Yan uwa masu girma,mun roki Allah gabanin zaben nan kan Allah Ya karbi addu’armu saboda kada mu hadu da fitinu da masifu da duk wani abu da ke da alaka da tashin hankali da kashe-kashe, kuma Allah Ya karbi addu’o’inmu.

Ya bayin Allah! Mun yi zabe cikin ’yanci da aminici, wanda ya samu nasara ya samu, wanda ya fadi ya fadi, al’amarin dai na Allah ne a gabani da kuma a baya.

Ya bayin Allah! Babu abin da ke kanmu a yanzu face shukura da godiya ga ni’imar Allah wadda ba ta kidayuwa ba ta iyakantuwa.

Allah Madaukaki Ya c: “Idan kuka yi Min shukura, sai in kara muku, kuma idan kuka buttulce, lallai ne azabaTa mai tsanani ce.”

Shukura tana turke ne da samuwar wani abu ko farautar abin da aka rasa, don haka wajibi ne mu yi godiya da shukura ga Allah. Shi kanSa Allah Mai shukura ne Yana shukura ga bawanSa mumini wanda ya yi masa da’a ya kyautata ibadarsa yana mai tsarkake ta domin Allah Ta’ala. Allah Madaukaki Ya ce: “Allah Ya kasance Mai shukura (godiya), kuma Masani.”

Kuma Allah Ya ce: “Allah ne Ya fitar da ku daga cikkunan iyayenku ba ku san komai ba, Ya sanya muku ji da gannai da zukata (tunani), tsammaninku kuna gode maSa.”

Ya bayin Allah! Ku sani wanda ba ya gode wa mutane ba zai gode wa Allah ba, wanda yake gode wa mutane kuma zai gode wa Allah. Don haka wajibi ne a kan kowane Musulmi mai kadaita Allah ya kyautata ga wanda ya kyautata masa, kuma ya kyautata ga wanda ma ya munanta masa. Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ka bi mummunan aiki da kyakkyawa, sai ya shafe shi, kuma ka yi mu’amala da mutane da kyakkyawar mu’amala.”

Allah Madaukaki Ya bayyanar da girmamawarSa da soyayyarSa ga Shugaban Najeriya Janar Muhammadu Buhari, domin Shi masoyinsa ne kuma cewa lallai Shi Ya yarda da shi. Don haka wajibi ne a kan Shugaba Muhammadu Buhari ya kara yi maSa shukura ya yi maSa godiya a fili da boye, wajen yi maSa biyayya da kuma kyautata wa bayinSa. Wannan shi ya kawo mu ga magana a kan hakikanin shukura da godiya.

Yadda Najeriya da kuma musamman Shugaba Muhammadu Buhari za su gabatar da shukura ga Allah a hakikaninta.

1. Godiya ta hanyar furuci da harce da kuma shukura da aiki. A yi ta furtawa da baki ana cewa ‘Alhamdulillahi rabil alamin’ babu iyaka da “Masha Allahu lakuwwata illa billah.’ A aikace kuma ya bayin Allah! A mayar da kyautatawa da kyautatawa ga wanda ya kyautata maka.

2. Mayar da amana. Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ka mayar da amana ga wanda ya ba ka amana. Kada ka ha’inci wanda ya ha’ince ka.”

3. Bai wa duk mai hakki hakkinsa- wadannan sun kunshi hakkin dan Adam da ’yancin bayyana ra’ayi da makamantansu, wajibi ne Shugaban Kasa da sauran shugabanni da wakilan da aka zaba su kiyaye wadannan ga jama’a.

4. Cika alkawari. Duk alkawuran da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi lokacin yakin neman zabe shi da sauran shugabannin da aka zaba da wadanda za a zaba a gobe wajibi ne su cika su.

5. Karba da rungumar kowane dan Najeeriya, namiji ko mace, karami ko babba. Shugaban Kasa ya dauki dukan al’ummar Najeriya nasa ne ba tare da lura da inda suka fito ba, ba tare da lura da sun zabe shi ko ba su zabe shi ba. Haka ya rika sauraren ra’ayin jama’a kan tsare-tsaren gwamnatinsa. Allah Madaukaki Ya ce: “Ka shawarce su a cikin al’amarin…” kuma Ya ce: “Al’amarinsu shawara ne a tsakaninsu.”

6. Cikakken mika wuya ga Wanda Yake yin halitta kuma Yake zabi, wato Allah.

7. Kara imani da sanin Allah, domin Shi ne Ya tsaya masa ya samu nasara a wannan zabe, kuma zai tambaye shi a gobe Kiyama. Allah Shi ne “Wanda ba a tambayarSa kan abin da Yake aikatawa, amma su (mutane su) ne ababen tambaya.”

Huduba ta Biyu

Godiya ta tabbata ga Wanda sammai bakwai da kasa da abin da ke cikinsu suke yi maSa tasbihi. “Kuma babu wani abu face yana tasbihi gami da gode maSa, sai dai ku ne ba ku fahimtar tasbihinsu. Lallai ne Shi Ya kasance Mai hakuri Mai gafara.” (Isra’i: 44). Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Shi kuma shugabanmu maulanmu Muhammad BawanSa ne kuma ManzonSa, wanda yake cewa “Ashe ba zan kasance bawa mai godiya ba?” Ya Ubangiji! Ka yi salati a gare shi, salatin da zai kusantar da mu zuwa gare shi.

Allah Madaukaki Ya fadi a bisa harshen Dawuda da Sulaiman (AS): “Hakika Mun bai wa Dawuda da Sulaiman wani ilimi sai su biyun suka ce: “Godiya ta tabbata ga Allah Wanda Ya fifita mu a kan da yawa daga bayinSa muminai.”

Yaya ba za su gode wa Ubangijinsu ba, alhali Ya fifita su a kan bayinSa masu yawa? Babu abin da wajaba a kansu face su yi masa godiya da shukura.

Allah Madaukaki Ya ce: “Ku yi tasbihi ga Allah a lokacin da kuka yi maraice da lokacin da kuka yi asubanci. Kuma godiya taSa ce a cikin sammai da kasa da lokacin farko dare da kuma lokacin da kuke cire kaya saboda zafi (azahar).” (Rum:18). Kuma Ya sake cewa: “Idan taimakon Allah ya zo da cin nasara. Ka ga mutane suna shiga cikin addinin Allah jama’a-jama’a. To ka yi tasbihi gami da gode wa Ubangijinka, kuma ka nemi gafararSa. Lallai ne Shi Ya kasance Mai karbar tuba ne.”

Don haka wajibi ne a kan Shugaba Buhari da masu taimaka masa da masu yi masa hidima da sauran shugabanni ko wakilan da aka zabe su yi ta tasbihi gami da gode wa Ubangijinsu, su yi ta istigfari gare Shi daga zunubansu. Domin abu ne mai wahala a ce wani Musulmi ko wani mutum ya zamo dan siyasa ba tare da yana aikata wasu laifuffuka da zunubai da karya ba komai kashinsu kuwa.

An karbo daga Imamatu (RA) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Allah bai ba wani bawa wata ni’ima ba, bawan ya yi godiya a kanta face wannan godiya ta fiye masa alheri daga waccan ni’ima.”

An karbo daga Umar bin Hasin (RA) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Lallai ne mafiya falalan bayin Allah Madaukaki a Ranar Alkiyama su ne masu godiya.” Daga Nu’uman bin Bashar (RA) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: Bayyana ni’imar Allah shukura ce, rashin bayyanata kuma butulci ne.”

Allah Madaukaki Ya ce: “Hakika wani manzo ya zo daga cikinku, abin da kuke wahala da shi yana damunsa, mai yi muku kwadayin sauki ne kuma ga muminai mai tausayawa ne mai jinkai.”

Don haka wajibi ne Shugaban Najeriya ya kyautata ga wadanda suke sonsa da ma wadanda ba su sonsa daga ’yan Najeriya daga dukan kabilu da shiyyoyi, ya raya kowane bangare wajen aiki, shin zabe shi ko ba su zabe shi ba. Idan ya yi haka ya yi shukura ne ga Allah a kan abin da ya samu na ni’imar Allah ta shugabancin kasar nan.

“Lallai Allah Yana umarni da adalci da kyautatawa da ba ma’abucin zumunta hakkinsa. Kuma Yana hani daga alfasha da abin ki da zalunci (ko rarraba kan jama’a). Yana yi muku wa’azi tsammaninku kuna tunawa.”

A cikin wannan aya akwai umarni guda uku akwai kuma hani guda uku wadanda wajibi ne a kan kowane Musulmi ya kiyaye su a kowane lokaci.

Imam  Sharafudeen Abdussalam Aliagan shi ne Babban Limamin Masallacin NASFAT na Kasa da ke Abuja, kuma za a iya samunsa ta tarho mai lamba: 08034710862