Fadar Shugaban Kasa ta ce babu shagulgula a bikin cikar Shugaba Muhammadu Buhari shekaru biyar a kan mulki kamar yadda aka saba.
Babban mai taimaka wa Shugaban Kasar kan Harkokin Yada Labarai Garba Shehu ya sanar da haka ranar Alhamis a shafinsa na Twitter.
Garba Shehu ya ce sabanin yadda aka saba, bana ba za a yi bukukuwa ba. Amma tsara yin bayanin nasarorin da gwamnatin ta samu a kafofin sadarwa daga bakin manyan jami’an gwamnati.
Ya ce za kuma a yi amfani da shafukan zumunta na Fadar Shugaban Kasa don watsa bayanai kan ranar kai tsaye.
- Buhari zai kara karbo bashin dala biliyan 5,513
- Buhari ya kai wa majalisa kasafin 2020 da aka yiwa gyara
- Gwamnoni za su gana da Malami kan ‘yancin bangaren shari’a da na majalisa
“Bisa al’ada a irin wannan rana ministoci kan yi bayanin nasarorin da gwamnati ta samu, amma bana ta sauya salo”, inji Shehu.
“Ga masu son ganin irin manyan sauye-sauyen da gwamnatin Buhari ta kawo wa ‘yan Najeriya, sai su yi dakon wannan rana mai dinbin tarihi a wajensu.
“Hakika mun sami nasarori da dama.
“Daga dawowar Shugaban Kasa a zango na biyu wato ‘Next Level’ alal misali, ya yi alkawari cewa shirin gwamnatinsa na N-power zai dauki matasa miliyan daya tare da samar wa kimanin miliyan goma madafa.
“Ya kuma yi alkawarin tallafa wa manoma da basussuka a shirinsa mai taken ‘Anchor Borrowers’.
“Sannan ya yi alkawarin samar da Dala miliyan 500 na tallafa wa masana’antu da kuma samar wa ‘yan kasa ayyukan yi”, inji Garba Shehu.
Ya ce shugaban zai kuma bunkasa ayyukan raya kasa, harkar lafiya, ilimi, kasuwanci da zuba jari da kuma kara shigo da mata a harkokin mulki.