✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da Buhari da gwamnoni 19 suka kori Mai Mala Buni —El-Rufai

El-Rufai ya ce bakin alkalami ya riga ya bushe, yanzu Gwamnan Neja ne Shugaban Riko na APC

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce Gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni ya yi sallama da shugabancin Jam’iyyar APC kuma babu abin da zai sake dawo da shi kan kujerar.

El-Rufai ya zargi Mai Mala Buni da shirin hana jam’iyyar gudanar da babban taronta na kasa, inda ya je ya karbo umarnin kotu da zai hana gudanar da taron ya kuma boye shi.

A lokacin da yake tsokaci kan rikicin shugabanci da jam’iyyar ta fada, El-Rufai ya ce Buni wanda yanzu haka ba ya Najeriya zai dawo kasar ne kawai a matsayin Gwamnan Yobe amma ba Shugaban Riko na Jam’iyyar APC ba.

Gwamnan ya ce alkalami ya riga ya bushe domin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari tare da gwamnoni 19 sun amince da tube Buni daga matsayinsa, kuma yanzu haka Gwamnan Neja, Abubakar Sani Bello, ya maye gurbinsa a matsayin sabon Shugaban Rikon APC.

El-Rufai ya ce babu tantama Shugaba Buhari ne ya ba da umurnin tube Buni, kuma an aiwatar da umarnin sabanin rade-radin da jama’a ke yi.

Gwamnan na Kaduna, ya kara da cewa bayan karbar jagorancin jam’iyyar da Bello ya yi, al’amura sun fara daidaita, kuma za su dawo da martabar jam’iyyar wajen gudanar da taron kasa kamar yadda aka shirya.

Ya zuwa yanzu dai Mai Mala Buni wanda ke kasar Jamus domin duba lafiyarsa bai ce uffan ba game da kwace ragamar shugabancin jam’iyyar da aka masa.

APC mai mulki na fama da rikicin cikin gida, inda ta sha dage lokacin gudanar da babban taronta na kasa, lamarin da ya ria jawo ce-ce-ku-ce.