Wakilin shiyyar Borno ta Kudu a Majalisar Dattawa, Sanata Ali Ndume, ya bayyana yadda a rana daya ’yan Boko Haram suka kashe mutum 93 a mahaifarsa ta garin Gwoza da ke Karamar Hukumar Gwoza ta Jihar.
Ya ce 73 daga cikin dattawa 75 da aka kashe, an kai su wata mahauta aka yi musu yankan rago, baya ga wasu almajrai 20 da aka harbe su har lahira duk a rana daya.
“Wata rana da sanyin safiya, mayakan Boko Haram suka debi dattawa 75 daga garin namu, suka kai su abbatuwa a Gwoza kuma suka rika bi daya bayan daya suna musu yankan rago, sai dai mutum biyu sun tsira sakamakon jini da ya rufe su aka zata su ma matattu ne”, inji shi.
“Mallam Durubu wanda makwabcina ne, mayakan Boko Haram sun harbe almajiransa 20 a rana daya. Har yanzu zan iya tuna gidansu, ina iya tuna ranar da aka kwantar da su a kasa aka rika yi musu ruwan harsashi na bindiga.
“Wani abun ba zan iya fadinsa ba a nan,” inji shi.
Sanata Ndume ya bayyana hakan ne ranar Laraba a Maiduguri, yayin wani zaman sauraron ra’ayoyin al’umma tare da masu ruwa da tsaki.
Aminiya ta fahimci cewa, Kwamitin Ayyuka na Musamman na Majalisar Dattawa da kuma Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabas (NEDC) su ne suka dauki nauyin shirya taron wanda aka gudanar domin yin bita a kan halin da yankin ke ciki a yanzu.
A yayin taron, Ndume ya ce a halin yanzu duk da kasancewarsa Sanata, ba ya da ikon shiga mahaifarsa ta Gwoza saboda rashin aminci da halin na rashin tsaro ya haifar.
Ya ce: “Ba na iya samun damar shiga dole sai dai a cikin tawaga ta rundunar sojoji”, inji Ndume wanda shi ne Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Rundunar Soji ta Kasa.