✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda bikin auren wadda ta auri kanta ya gudana a Indiya

Ban taba son yin aure ba, amma ina so in zama amarya.

Wata mata a kasar Indiya ta kafa tarihi bayan ta yi abin da ake zaton shi ne bikin aure na farko irinsa a kasar.

Rahotanni sun ce, matar mai suna Kshama Bindu mai shekara 24, ta auri kanta da kanta ne tare da gudanar da bikin auren a gidanta a gaban kawaye da abokan aikinta a ranar 8 ga Yunin da ya gabata.

Da farko ta shirya yin bikin auren ne a wani wurin bauta tare da wani limamin wurin bautar a birnin Badodara, amma Shugabar Jam’iyyar Bharatiya Janata, Sunita Shukla, ya yi adawa da bikin auren a wurin bautar.

An gaya mata cewa, a addinin Hindu ba a yarda mace ta auri kanta ‘sologamy’ ba, don haka bikin ba zai gudana ba.

Sunita ta ce: “Ina adawa da zabin wurin kuma ba za a bar ta ta auri kanta a kowane wurin bauta ba.

“Irin wannan aure ya saba wa addinin Hindu kuma hakan zai rage yawan al’ummar Hindu.

“Idan wani abu ya saba wa addini, to babu wata doka da za ta yi tasiri a kan wannan abu,” inji ta.

Amma ga Kshama, auren kanta ‘tamkar sa kai ne’ na tallafa wa kanta da ‘kauna marar iyaka’.

Da wannan tunani ta yanke shawarar ci gaba da auren kanta kuma ta samu sabon wuri – duk da ana jayayya.

Ta ce: “Ban taba son yin aure ba, amma ina so in zama amarya – don haka na yanke shawarar in auri kaina.

“Ba zan iya kwatanta hakan da kalmomi ba, amma kowa yana mini fatar alheri tare da kwatanta lamarin da barkwanci, faruwar hakan ya dauki hankalina.

“Ina zubar da hawayen farin ciki idan ina karanta sakonni da labarai kuma ina matukar farin ciki da ranar aurena,” inji ta.

Kshama ta fuskanci kalubalen dakatar da burinta, kamar yadda limamin wurin bautar ya fara shirin yi mata, an yi shirin soke alwashinta tana gab da auren.

A karshe, ta samu damar kammala auren kanta ta hanyar bin al’adun ‘Mehendi’ da ‘Haldi’ – nau’in fasahar yin zane a jiki da amfani da hodar Turmeric don gyara jikinta.

Duk da koma-baya da ta samu, ta tabbatar da muradinta- kodayake iyayenta sun goyi bayan zabinta kuma sun kasance tare da ita a shirin auren kanta.

Kshama ta shirya tafiya hutun amarcinta a garin Goa a ci gaba da shagalin bikin auren kanta.