Fassarar Ahmed Garba Mohammed da Jamilu Adamu da Umar Mohammed Gombe da Isiyaku Mohammed
Wani rahoto da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya fitar ya nuna yadda bankunan Standard Chartered Bank da Stanbic IBTC da Citi Bank da kuma Diamond Bank suka hada baki da kamfanin sadarwa na MTN wajen janye kudaden waje da suka kai Dala biliyan 8 da miliyan 100.
Takardun da wakilinmu ya gani a karshen mako sun nuna cewa babban bankin ya gana da dukan masu hannu a cikin lamarin tare da tabbatar da hadin bakinsu kafin ya ci tatarsu. Bankin CBN ya ci tarar bakunan hudu Naira biliyan 5 da miliyan 870.
Sannan CBN ya nemi bakunan su dawo da Dala biliyan 8 da miliyan 134 da dubu 312 da 397 da senti 63 din, kan abin da ya bayyana da “mummunar keta dokoki da ka’idoji Tarayyar Najeriya ciki har da Dokar Musayar Kudaden Waje (Sanya ido da Sauran Tanade-Tanade) ta 1995 ta Tarayyar Najeriya da kuma jagoran musayar kudeden waje na shekarar 2006.”
Tara mafi girma ita ce wadda aka yi wa Bankin Standard Chartered ta Naira biliyan 2 da miliyan 470 da dubu 604 da 767 da kwabo 13. Sannan an ci bankin Stanbic IBTC Nigeria tarar Naira biliyan 1 da miliyan 885 da dubu 852 da 847 da kwabo 45. Shi kuwa Citi Bank an ci tararsa Naira biliyan 1 da miliyan 262 da dubu 541 da 562 da kwabo 31 yayin da aka ci tarar Bankin Diamond Naira miliyan 250 saboda saba ka’idoji.
Sannan an bukaci Kamfanin MTN da bankunan hudu su dawo da Dala biliyan 8.1 ga asusun Bankin CBN, saboda cire su ta haramtacciyar hanya.
Sai dai Kamfanin MTN ya musanta wannan zargi da kakkarfar nurya, inda ya ce babu wata riba da aka bayyana ko MTN ya biya baya ga wanda ya dace da takardar shaidar shigo da jari (CCIs) da aka ba bankunan tare da amincewar Bankin CBN, kamar yadda doka ta tanada.
Sai dai a wata wasika da Gwamnan Bankin CBN, Mista Godwin Emefiele ya tura ga bannkunan da lamarin ya shafa da kuma MTN, ya ce Kamfanin MTN da bankunan hudu sun hada baki ta haramtacciyar hanya wajen sauya rancen masu hannun jari don fifita hannun jari (zuwa rance marar ruwa) da suka kai Dala miliyan 339 da dubu 594 da 146. Sannan adadin Dala biliyan biliyan 8 da miliyan 134 da dubu 312 da 397 da senti 63 bankunan suka fitar a madadin kamfanin MTN Nigeria Communication a tsakanin shekarar 2007 zuwa 2015.
A cikin wasikar ta Mista Emefiele ga bankunan ya ce, sakamakon kammala bincike Kwamitin Gwamnonin Babban Bankin ya gana da shugabannin bankunan da wakilan Kamfanin MTN a Jihar Legas a ranar 25 ga Mayun 2018 don ya ba kowane bangare damar kare kansa, kafin daukar mataki a kan lamarin. Wasikar Bankin CBN ta ce, bin diddgin bayanan kudi Kamfanin MTN wanda ya zo karshe a ranar 31 ga Disamban 2017 ya gano an sa Dala miliyan 399 da dubu 594 da 146 a matsayin adanannu/hannun jari a matsayin rancen masu hannun jari da kuma Dala miliyan 2 da dubu 996 da 117 a kudin da aka zuba jari bisa yarjejeniyar masu hannun jari wanda ya saba da takardar shaida ta CCIs da bankunan suka bayar.
Ya ce bisa bukata daga Kamfanin MTN ta hannun bankin Standard Chartered Banki ta neman CBN ya amince ya mayar da rancen masu hannun jari ya koma hannun jarin da aka fi fifitawa, sai aka bayar da amincewa bisa dacewa ta wasika a ranar 13 ga Nuwamban, 2007 da sharadin za a bayar da amincewa ta karshe ne idan kamfanin ya cika wasu ka’idoji.
ka’idojin sun hada da aiwatar da shawarwarin da ke mai lamba 5B na shawarar da hukumar ta yanke a ranar 8 ga Nuwamba 2007 da kuma mika takardun shaida ga Daraktan Sashen Kasuwanci da Musayar Kudi na Bankin CBN da tanadin daukar alkawarin ba za a tura kudi kan riba ko biyan uwar kudi ba ga masu hannun jari daga ranar da aka sauya rancezuwa hannun jarin da aka fifita.
Kuma duk da rashin cika sharudi na (b) da ke sama da kuma rashin samun amincewar karshe daga Bankin CBN, bankunanku sun sauya rancen masu hannun jari zuwa hannun jarin da aka fifita, inda bankin Standard Charted Bank ya bayar da sabuwar takardar shaida ta CCIs don sauya wa kudin hanya ta haramtacciyar hanya.
Martanin MTN
A wani jawabi Kamfanin MTN Nigeria Communications Limited ya ce, sun karbi wasika a ranar 29 ga Agusta 2018 daga Bankin CBN da ke nuna takardar shaida ta CCI da ke bayyana cewa an bayar da amincewa da takardar sauyin rancen kudin masu hannun jari a Kamfanin MTN Nigeria a shekarar 2007, a matsayin wucin-gadi. Kamfanin MTN Nigeria ya yi kakkausar suka kan wadannan tuhume-tuhume, inda ya ce “babu wata riba da aka gabatar ko aka biya daga Kamfanin MTN Nigeriafiye da takardar shaida ta CCI da bankunanmu suka bayar da amincewa daga Bankin CBN kamar yadda da doka ta tanada,” inji MTN.
An tabbatar da shawarwarin da shaidar CCI ta kunsa na cikin binciken da Majalisar Dattawa ta Najeriya ke yi.
A watan Satumba 2016 Majalisar Dattawa ta bai wa kwamitin bankuna da inshora da sauran harkokin kudade don gudanar sahihin bincike korafin da aka gabatar tare da na musayar kudaden waje kamar yadda dokar bin diddigi da wasu abubuwan bincike ya tanadar ga MTN Nigeria da sauransu.
A rahoton da aka gabatar a watan Nuwamba 2017 binciken kamfanin MTN Nigeria bai yi daidai da dokar musayar kudaden waje ba, sannan ba bu wani rahoto dake sukar rahoton kamfanin MTN Nigeria.
Kamfanin MTN ya ce, sake gabatar da wadannan korafe-korafen da ba su ji dadinsu ba saboda lalata kadarorin da suka mallaka za u yi, wanda hakan zai iya dakile shirinsu na ci gaba da farfado da tattalin arzikin Najeriya. MTN ta ce, za mu gayyaci hukumomin da suka dace don kare muradunmu a wannan batun tare da bayyana matsayarmu bayan kammala binciken”.
Jawabin masana:
Da yake jawabi, Farfesa Uche Uwaleke, shugaban sashen nazari harkokin kudade na Jami’ar Jihar Nasarawa cewa ya yi, “bayan cin tarar bankunan, Babban Bankin Najeriya ya nuna cewa lallai akwai dokoki a bangare harkokin kudade na kasar nan da dole kowa ya yi biyayya. Yadda aka samu matsala ba zai yiwu ba sai an samu hadin kai daga bankunan da kuma wasu daga cikin CBN.”
Ya kara da cewa, “baicin tarar da aka ci bankunan, ya kamata EFCC ta shigo cikin lamarin domin a gano wadanda suke da hannu a lamarin nan na yin amfani da kudaden masu zuba jari ba bis ka’ida ba, da kuma ba bankin CBN bayanan karya, sannan a hukunta su. Amma abin da ya faru akwai darasi da za a iya koya.”
A cewarsa, “Yadda bankunan nan suke harkallar canjin kudaden kasashen waje, zai iya zama daya daga cikin abubuwan da suke kawo matsala a harkar canjin kudaden, wanda kuma hakan na shafar masana’antu da farashin kaya.”
Ya kuma nuna cewa “Kamar yadda kididdigar NBS ta nuna a rubu’i na biyu na bana, Bankin Standartd Chartered da Stanbic IBTC su ne suke ta harkar shigo da kaya a rubu’in. Wannan lamarin zai iya canja wannan bayanin akalla na wani dan lokaci.
“Watakila kasuwar zuba jari ta samu matsala sosai ita ma. Bankuna biyu da abin ya shafa wato Stanbic IBTC da Diamond suna cikin kamfanonin kasuwar zuba jari, don haka idan jarinsu ya durkushe, zai iya shafar bankuna domin ’yan kasuwa za su iya janye jiki daga bankuna har sai an gano bakin zaren.
“Haka nan kuma, wannan lamarin zai iya hana MTN shiga cikin tsarin kasuwar zuba jarin. Don haka cin tara na da muhimmanci ga tattalin arzikin kasar nan. Mahukunta ya kamata su ci gaba da tabbatar da cewa duk manyan kamfanonin da suke kasar nan musamman a bangaren mai da bankuna da sadarwa sun kiyaye wajen bin doka.”
A nasa bangaren, Mista Rislanuddeen Mohammed, wanda tsohon Manajan Darakta ne kuma babban Jami’in gudanarwa na rika na bankin Unity cewa ya yi, “matakin da Babban Bankin ya dauka abin a yaba ne, kuma ya kamata ya zama somun tabi ga mahukunta na bangaren da kuma jami’an tsaro wajen tabbatar da ana bin doka a kasuwancin kasar nan, ko kuma a shiga matsala. Kuma wannan lamarin ya nuna cewa watakila akwai sauran rina a kaba.”
Ya ce ya kamata a kara karfafa masu lura da bangaren domin su bankado irin wadannan matsalolin, “irin wadannan matsalolin su suke kawo matsala a farashin man fetur da kuma fitar da man da kuma canjin kudi,” sannan ya kara da cewa “irin wadannan matsalolin ne suke tirsasa gwamnati ta ciyo bashi domin aiwatar da wasu muhimman ayyuka. Kuma hakan yana kawo matsala ga ci gaban tattalin arziki domin rashin canjin kudade da ake amfani da su wajen habaka tattalin arizki da samar da ayyukan yi. Hakanan kuma irin wadannan matsalolin suna jawo matsala ga kudin shiga. Don haka wannan matakin abin a yaba ne. Amma su nemi shawarar masan shara’a domin sanin matakin da za su dauka na gaba.”