Jam’iyyar APC ta sake fadawa a wani sabon rudani bayan da a ranar Litinin Gwamnan Jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello ya yi ikirarin karbar jagorancin jam’iyyar a matsayin Mukaddashin Shugaban Riko.
Rahotannin sun ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne ya amince da sauke Shugaban riko na Jam’iyyar APC, kuma Gwamnan Jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni daga shugabancin jam’iyyar.
- Buni muka sani shugaban APC ba kai ba —INEC ga Bello
- ’Yan siyasa sun koka da kamun ludayin sojojin da suka yi juyin mulki a Guinea
Gwamna Abubakar Sani Bello wanda yake cikin kwamitin rikon mai mutum 13 ya isa Sakatariyar Jam’iyyar ce a ranar Litinin inda ya jagoranci gudanar da ayyukan jam’iyyar.
A lokacin da yake magana da manema labarai a Sakatariyar, Gwamna Bello ya bayyana kansa a matsayin Mukaddashin Shugaban Riko, inda ya jagoranci zama da jiga-jigan jam’iyyar, kuma ya yi haka ne a daidai lokacin da wasu rahotanni ke cewa Shugaba Buhari ya amince da cire Gwamna Mai Mala Buni daga shugabancin kwamitin rikon, saboda zargin da ake yi cewa ba shi da niyyar gudanar da babban taron jam’iyyar.
Sai dai Gwamna Abubakar Sani Bello, ya ce bai san da maganar karɓar shugabanci daga hannun Gwamna Mai Mala ba.
Ya ce abin da ya kai shi Sakatariyar APC shi ne ya je tattaunawa da Kwamitin Riko na APC ya shirya kafin babban taron jam’iyyar da za a yi.
Kuma ya ce wani abin da ya kai shi sakatariyar shi ne rantsar da shugabannin jam’iyyar na jihohi, inda ya ce bai san tushen zancen da ake cewa ya karɓe kujerar Gwamna Mai Mala Buni ba.
Ya ce akwai ka’idojin da ake bi idan za a karɓi jagorancin, inda ya ce ya je ne a matsayin Mukadashin Shugaban Jam’iyyar domin ci gaba da aikin jam’iyya.
Mutane da dama sun rika nuna shakku a kan lamarin, inda suke cewa da alama salo ne na mamaya.
Fadar Shugaban Kasa ta yi gum kan ikirarin da ake yi cewa Shugaba Buhari ne ya amince da sauke Shugaban Rikon, wanda hakan ya dada jefa kokwanto a zukatan magoya bayan jam’iyyar.
Sai dai tun a ranar Litinin din Jam’iyyar APC ta musanta rahotannin da suke cewa an samu sauyin shugabanci a cikinta.
Hakan yana kunshe ne a wata sanarwa da Sakataren Jam’iyyar Mista John Akpanudoedehe ya raba wa manema labarai.
Akwai rade-radin gwamnonin jam’iyyar ne suke son yin waje da Gwamna Mai Mala Buni daga shugabancin jam’iyyar, inda wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa a ranar Alhamis din makon jiya wadansu gwamnoni sun kitsa kawar da shi a wani taro da suka yi a Abuja. Majiyar ta ce, bayan wannan yunkuri gwamnoni wadanda suka hada da na Ekiti da Jigawa da Filato da Kebbi da Neja da Kaduna sun gana da Shugaban Kasa a ranar Asabar, inda suka samu umarninsa na a cire Buni daga shugabancin jam’iyyar.
Bayanai sun ce an shaida wa Shugaban Kasar shirin Buni da abokan tafiyarsa ciki har da wadansu jami’an Fadar Shugaban Kasa na hana gudanar da Babban Taron Jam’iyyar da aka shirya yi a ranar 26 ga Maris din nan.
Aminiya ta samu labarin cewa har an samu umarnin wata kotu na hana babban taron, kamar yadda Aminiya ta ga takardar hana jam’iyyar yin taron daga wata Babbar Kotun Abuja da ke Bwari, har sai kotun ta saurari karar da aka kai gabanta.
Mutane da dama suna ganin irin wannan dambarwar shugabanci da APC ke fama da ita tana iya rage karfinta musamman a daidai wannan lokaci da ake fuskantar babban zaben badi.
Wani masanin siyasa Dokta Abubakar Kari, malami a Jami’ar Abuja, ya shaida wa BBC cewa rudanin alamu ne da ke nuni da cewa ana tsananin gwagwarmaya a tsakanin bangarori dabandaban na Jam’iyyar APC, inda kowane bangare yake kokarin ganin ya kwace mulkin jam’iyyar.
“Wannan ya haddasa tsananin rashin yarda da rashin hadin kai ta yadda duk wani mataki da aka dauka a jam’iyyance sai an ba shi fassarori mabambanta,” inji Dokta Kari.
Duk da cewa wasu na ganin rigimar da ke tattare da shugabancin kan iya sanadin kawo karshen APC, sai dai Dokta Kari yana ganin da wuya APC ta mutu sai dai watakila ta sha wuya.
Ya ce rashin yarda da rashin jituwa babbar matsala ce ga Jam’iyyar APC, amma a ganinsa bai kai a ce jam’iyyar za ta wargaje ba, musamman ganin cewa jam’iyya ce wadda take da mulki da Gwamnatin Tarayya da kuma kusan biyu bisa uku na jihohin Najeriya.
Amma ya ce abin da ke faruwa a halin yanzu yana da matukar hadari a jam’iyyar ganin cewa idan abubuwa suka ci gaba da faruwa, ko da jam’iyyar ba ta wargaje ba za ta iya rasa karfin da take da shi