Akalla sama da mutum 500 ne suka rasa matsuguninsu sakamakon wani mamakon ruwa da ya haddasa ambaliyar ruwa a gabashin kasar Afirka ta Kudu.
Ambaliyar ruwan da ta faru a tekun gabashin kasar a ranar Lahadi, wata guda bayan da ambaliyar ruwa mafi muni ta auku a kasar da ta kashe mutane sama da 400.
- IPOB: ’Yan bindiga sun fille kan dan majalisa a Anambra
- Bayan shekara 11 AC Milan ta sake lashe gasar Serie A
Bayanai sun ce ambaliyar ruwa ta mamaye yankin Chatsworth, da ke wajen birnin Durban a Afirka ta Kudu.
Jami’an agaji sun ce ba a samu asarar rayuka ba, amma an yi asarar dukiya mai tarin yawa, musamman a Durban babban birnin lardin KwaZulu-Natal.
A watan Afrilu ne ruwan sama kamar da bakin kwarya ya kashe mutane 435 sakamakon ambaliyar ruwa da zabtarewar kasa, inda wadanda suka tsira daga Iftila’in suka shafe kusan makonni biyu ba tare da ruwan sha ba.
Kazalika, a watan Afrilu, gamayyar kungiyoyin masu fafutukar yaki da matsalar sauyin yanayi sun garzaya kotu, inda suka shigar da kara kan shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa da wasu ministocinsa, bisa gaza daukar mataki kan sauyin yanayi a kasar.
Afirka ta Kudu na ci gaba da fuskantar barazana daga ambaliyar ruwa musamman a yankin gabashin kasar, lamarin da ya sa ake ci gaba da samun salwantar rayuka da dukiya mai tarin yawa.