Janar Abdulsalami Abubakar fitaccen dattijo ne da ya mulki Najeriya a tsakanin 1998 da 1999, inda ya mika mulki ga gwamnatin farar hula.
A wannan tattaunawa da gidan talabijin na Trust TV, Janar Abdulsalami, ya tuno baya kan rayuwarsa, irin kiki-kakar da aka samu ranar da tsohon Shugaban Kasa Janar Sani Abacha ya rasu, alakarsa da Abacha tun sun samari, yadda ya fara mulkin Najeriya daga cikin bariki, abin da ya shi neman ya mulki bayan wata shida da hawansa, dambarwar rasuwar Abiola, yadda Obasanjo ya zama shugaban kasa bayan fitowa daga kurkuku, dalilin da tsohon Shugaban Kasa Jonthan ya karbi kaye a zaben 2015 da sauransu:
Ku biyo mu:
Ta bayyana ka fara aikin soja ne a matsayin sojin sama sannan ka koma sojin kasa. Me ya kawo wannan canji?
Na fara aikin soja ne da sojin kasa sannan sojin sama sai na dawo sojin kasa. Abin da ya sa na ce haka, na halarci ganawa don shiga sojin kasa ne a Disamban 1962, lokacin da muka kammala makarantar sakandare.
A lokacin ana ta kokarin samar da hafsoshin soji ’yan kasa, a lokacin sojin ruwa da sojin kasa ne kawai ake da su.
To a 1962 sai muka halarci ganawa da hukumar zabar sojin kasa. A lokacin akwai karancin gurabun horar da kananan jami’ai a Makarantar Horar da Sojin Kasa ta wancan lokaci, wadda ta zama NDA.
To bayan hukumar ta tantance sai aka raba mu kashi biyu; kashi na farko suka fara samun horo a makarantar horar da sojin kasa, wannan kashi ya kushi Shugaba Ibrahim Babangida da Janar Abacha da Janar Nasko da Janar Magoro da Janar Sani Sami da Janar Omu da sauransu.
To sai muka yi zaman jira su kammala kafin mu fara. To a wannan jira ne aka kafa rundunar sojin sama. Don haka wadansunmu da muke zaman jira aka ce, “Me zai hana ku je ku fara yin horo a sojin sama?” Don haka muka zama na farko a sojin sama.
Jamusawa suka zo muka samu horon sojin sama, wanda nake jin a wata uku ne ko shida, bayan haka aka tura mu Jamus.
Muna Jamus ne Yakin Basasa ya barke kuma aka samu mutuwar hafsoshi a sojin kasa, don haka aka mayar da wadansunmu sojin kasa.
Aka tura mu NDA, wadda a lokacin ta fara aiki domin mu yi abin da ake kira horon gaggawa wanda bayan haka aka yaye mu aka tura mu fagen daga, wannan shi ne abin da ya faru.
Wato tun kana sakandare kake son zama sojin kasa, kuma me ya karfafa maka hakan?
Kamar yadda na shaida maka, a lokacin, muna shirin kammala karatun sakandare a 1962, kuma akwai shirin karfafa samar da hafsoshi ’yan kasa a Sojin Najeriya.
Akwai wani kwamiti da Ma’aikatar Tsaro ta kafa don jawo ra’ayin masu kammala makaranta su shiga soja.
Bari in koma baya kadan, kan lokacin makarantata, tun daga babbar makarantar firamare har zuwa sakandare, ni mai son shiga jama’a ne, don haka na zama dan Sikawut.
Idan muka koma kan yunkurin gwamnati na jawo ra’ayin masu kammala makaranta su shiga soja, sun kafa kwamitin da ke zagayawa yana jawabi ga masu kammala makaranta.
Makarantarmu tana cikin wadanda aka je, kuma kwamitin ya kunshi Kyaftin Gowon, Janar Gowon wanda ya zama Shugaban Kasa.
Suka zo mana sun cancada ado da kakin soji, suka yi mana bayani kan aikin soja da damarmakin da suke ciki da sauransu.
Wannan ya karfafa min a karshen jarrabawar satifiket din sakandarenmu muka rubuta neman aikin soja hukumar ta tantance mu.
Shin da gaske ne ana shirin yi maka ritaya kana Babban Hafsan Tsaro a 1998 kwana daya kafin ritayar Abacha ya rasu, maimakon ritayar aka nada ka Shugaban Kasa?
Haka Allah Madaukaki Ya tsara haka. Gaskiya tun daga fara mulkin Abacha, akwai wadansu mukarrabai a sojoji da ba su aminta da wasunmu ba, don haka aka shirya yi mana ritaya, amma na ci sa’a na yi ta tsallake ritayar har zuwa lokacin da Allah cikin hikimarsa Ya yi abin da Ya so na zama Shugaban Kasa.
Shin alkarka da Janar Babangida ce ta zama dalilin da suka ga cewa mai yiwuwa ka zama wani mutum da zai iya mulkin?
To, hakika ba na cikin tunanin mukarraban, amma kana da damar fadin haka. Wasu lokuta alaka takan shafi matsayin rayuwar mutum, wannan bisa ma’aunin zato ne da sauransu.
Kai ba abokin Abacha ba ne. Ina ganin kamar kun dade tare?
Eh haka ne, bari in fadi wannan; mu sa’o’i mun san kanmu, ya alla mun fito daga makaranta daya ce ko a’a, matukar dai kana yin wani wasa.
Ka san a lokacin akwai wasannin da ake gasa a tsakanin makarantu inda aka karkasa mu a Arewacin Najeriya, mu rika wasanni a tsakanin makarantu har a zo wasan karshe. To ni dan wasa ne haka ma Abacha.
Wadanne wasanni ke nan?
Kwallon kafa da kwallon gora da kurket da guje-guje da sauransu; ka san a karshen kowace shekara makarantu sukan fafata a tsakaninsu. Kuma a irin wadannan wasanni ne muka san juna.
Mu sa’o’i ne, na fito daga Makarantar Sakandare ta Bidda, Abacha kuma daga Kano, ta haka muka hadu.
Kuma kamar yadda na fada akwai batun karfafa wa masu kammala makaranta su shiga aikin soja. To kamar yadda kwamiti ya zo makarantarmu haka ya je Kano da sauran makarantu, sannan muka kammala a Disamban 1962, shi da ni mun fito a wannan rukuni.
Dukkanmu mun yi sha’awar shiga aikin soja kuma duka muka halarci ganawar tantancewar.
Kamar yadda na fada maka a wajen waccan tantancewar muna cikin jerin sunayen wadanda suke jira; kuma a wancan jerin kai-tsaye ni nake bin Abacha.
Ka san Abacha gajere ne, don haka idan muka zo inda ake tsalle a kamo karfe ko gini mukan taimaka masa ya haye.
Don haka alakata da Janar Abacha ta faro ne tun muna makaranta kuma ta ci gaba har zuwa lokacin da muka samu kanmu a aikin soja, kuma a lokacin Yakin Basasa, muka samu kanmu muna yaki a birged guda.
Ina jin yana jagorancin Bataliya ta 95 ni kuma ina jagorancin Bataliya ta 84 a karkashin Birged ta 9 da marigayi Janar Shehu ’Yar’aduwa ke jagoranta.
Don haka mun yi yaki ne a fage guda a lokacin yakin. Hakika wannan shi ne ya karfafa dangantakarmu sosai.
Amma sai ga shi hakan bai kubutar da kai daga yiwuwar yi maka ritaya a 1998 ba?
Eh, wannan shi ne burin sauran mukarraban da suke damawa a lokacin, a fahimtata wannan ba ra’ayinsa ba ne.
A gaskiya, a wurina Abacha mutum ne mai matukar kyautata wa abokansa da mutanen da ya sani. Bai taba cin wata amana ba, mutum ne tsayayye, kaifi daya har zuwa lokacin da ya rasu.
Kamar yadda na ce, tun daga ranar da ya zama Shugaban Kasa, akwai mutanen da kwata-kwata ba su gamsu da wasunmu ba, don haka suka so a yi waje da mu, amma ya tsaya kan bakarsa, ya ki ya yi min ritaya ni da sauran wadanda suke son tafiya tare da shi.
Na san akwai matsi sosai gare shi kan ya yi ritaya wa mutane kamar Janar Haladu da Janar Duba da Janar Usaini da ni kaina da sauran mutane, amma aka ci sa’a wasunmu suka tsallake wannan shiri.
Akwai wadanda suke ganin Janar Usaini babban amininsa ne, kuma ana ganin suna da cikakken kusanci. Don haka saboda shi abokin Janar Abacha ne, sauran mukarraban suke da wani tunani na daban.
Yallabai, ko za ka yi mana bitar ranar da Abacha ya rasu da tataburzar da ta faru da yadda ka zama Shugaban Kasa?
Abubuwa da dama sun faru a ranar da Janar Abacha ya rasu.
Ina jin ya rasu ne a ranar da aka shirya zai je Togo, don halartar taron ECOWAS ko AU. Sai na samu kira daga Fadar Shugaban Kasa, cewa Janar Abacha yana son gani na.
Nan take na fara tunani cewa ina fata ba dai ya canja ra’ayinsa na zuwa Togo ba ne, yana shirin tura ni saboda a lokacin, ni ne mutum na biyu a gwamnatin domin a lokacin Janar Diya da sauransu suna fama da matsalar zargin juyin mulki.
Don haka sai nake tunanin Janar ya canja ra’ayinsa ne zai tura ni, domin a lokuta da dama akan kira ni, in je in wakilici Shugaban Kasa.
Lokacin da zan shiga wanka, sai na fada wa matata cewa, “Ina jin zan tafi taron AU, ki taimaka ki kintsa min jakata,” amma kafin in gama sai ga wani kiran.
Shin da safe ne?
Eh, da safe ne. Sai kuma ga wani kiran cewa; “Shugaban Kasa yana jiran ka.”
Na ce, “To gani nan zuwa.” Sai kawai na sa rigar motsa jiki, tunda babu lokacin sa yunifom da sauransu, domin an matsa cewa ana bukata ta da gaggawa.
Na je da kayan motsa jiki, ina jin ina sanye da silifas. Lokacin da na shiga sai suka ce, “Janar yana cikin ofis.”
To na saba idan na je ofishin ko wa ke tare da Janar Abacha nakan shiga ne in same shi, yana iya cewa “Ka jira in gama da wannan bawan Allah ko ya bukaci wancan ya bar mu.”
To abin mamaki lokacin da na zo, ina hawa benen, sai wani ya ce, “A’a ya ce ka jira a dakin karbar baki.”
Kuma abin mamaki na zauna a dakin karbar bakin har minti 30 ko 40, sai na rika mamakin abin da ke faruwa.
Duk lokacin da na yi niyyar zuwa sama sai su ce a’a Janar ya ce, in jira. Bayan kamar minti 40 ina jira sai marigayi [Ibrahim] Coomassie, wato Sufeto Janar na ’Yan Sanda ya zo inda nake ya ce, “Yallabai ka zo.”
Kuma maimakon zuwa ofishin sai muka fita, ya ce, “Za mu je gidan ne.” Muna cikin haka ne ya shaida min cewa, “Wato wani abin bakin ciki ne, Janar Abacha ya rasu da dare.”
To a haka muka shiga inda Abacha yake, kuma muna shiga suka nuna min inda gawarsa take, na shiga na yi masa addu’ar neman gafara da sauransu.
Sannan muka shiga falo inda na iske wadansu mutane ciki, Coomassie na wurin da Babban Jojin Najeriya, ina jin da Ambasada Babagana Kingibe da jami’in tsaro daya ko biyu ba zan iya tuna kowa da kowa ba.
Shin mutuwar ta Allah ce saboda akwai zarge-zarge da dama?
To a lokacin da aka shaida min ya rasu, babu wadannan zarge-zarge, daga baya suka taso. Damuwarmu a lokacin ita ce Shugaban Kasa ya rasu, yaya za mu sanar da kasa da sauransu.
A lokacin Babban Joji ne ya jagorance mu ya ce, “Kun gani an dauki lokaci akwai bukatar a sanar da ’yan Najeriya kan rasuwar Shugaban Kasa, ba za a bar gibi ba, wajibi ne a samu Shugaban Kasa kafin ku ci gaba da gudanar da sauran abubuwa.”
Ina jin wannan ne ya aza harsashin sauran abubuwan. Don haka nan take a matsayina na Babban Hafsan Tsaro na lokacin na hanzarta kiran taron Majalisar Kasa.
Kana cikin tufafin motsa jikin ko ka canja a lokacin?
Ina sanye da tufafin motsa jikin, saboda babu lokaci, kuma saboda mun samu kanmu a cikin kaduwa da tashin hankali.
Daga baya ne bayan mun shirya taro na koma gida na sa yunifom.
A lokacin an cimma matsaya ce ko an yi takaddama kan wanda zai zamo Shugaban Kasa?
Lokacin da na dawo na sa tufafi sosai, a lokacin wakilan Majalisar Mulkin Soja sun fara isowa, da muka hadu, sai muka shiga taro.
Muka fada musu abin da ya faru duk da cewa duk mambobin sun san Mai Girma Janar Abacha ya rasu. Muka sanar da majalisar rasuwarsa da shawarar da Babban Joji ya bayar kafin mu yi komai cewa wajibi ne a samu wanda zai karbi ragamar mulki.
An dauki lokaci mai tsawo kafin wakilan majalisar su samu matsaya. A zauren an samu muhawara sosai. A karshe aka ce muna da Janar Useni wanda a lokacin shi ne hafsa mafi girma, to amma shi yana bangaren gudanarwa ce, shi ne Ministan Birnin Tarayya, ni kuma ni ne Babban Hafsan Tsaro, don haka dayanmu ne zai zama Shugaban Kasa.
Aka kasa cimma matsaya, sai wani ya ce, “Kun gani, dole mu shaida wa duniya cewa Janar Abacha ya rasu, tun kafin lokaci ya kure, mu je mu binne shi kafin mu dawo mu daidaita tsakaninmu.”
A lokacin da hakan ke gudana iyalansa sun yanke shawarar a binne shi a Kano, don haka muna tattaunawa ana tsara yadda za a binne shi a Kano.
Ina jin wannan ya kai mu har dare, lokacin da dukkanmu muka bar wannan batu muka ce a je a yi masa jana’iza mu dawo, wannan shi ne abin da ya faru.
Sai muka tafi Kano muka yi masa biso muka dawo kan batun wanda zai karbi mulki.
Hakika a matsayina na Babban Hafsan Tsaro ni ne nake shugabantar taron; to a karshe bayan kada kuri’a da sauransu mambobin majalisar suka yanke shawarar in karbi mulki a matsayin Shugaban Kasa.
Kuma kana mulki ne rasuwar MKO Abiola mai cike da takaddama ta auku. Har yanzu akwai masu ganin akwai wasu boyayyun abubuwa da suka faru. Ko za ka fayyace hakikanin lamarin, ka shaida mana abin da ka sani?
Eh, akwai zarge-zarge da dama cewa wai mu muka kashe Abiola. Kamar kullum duk lokacin nake magana a kan marigayi Abiola, nakan gode wa Allah da Ya nuna min wasu abubuwa a lokacin da Ya ba ni mulkin kasar nan.
A ranar da Moshood (Abiola) ya rasu, Allah Ya jikan sa, abu biyu zuwa uku suka sa a kullum nake gode wa Ubangijina.
Na daya na karbi bakuncin wani ayari daga Amurka a karkashin jagorancin Pickering (Jakada Tom Pickering) wanda a lokacin, ina tsammanin shi ne Sakataren Wajen Amurka ko wani abu kamar haka.
A cikin ayarinsa ina tunawa akwai Susan Rice. Na tuna da ita sosai saboda rawar da ta taka daga baya.
To bayan ziyarar da tattaunawar da muka yi, lokacin da za su bar ofishina, Pickering ya ce, “Mai girma Shugaban Kasa mun nemi ganin Moshood Abiola amma an hana mu.”
Sai na ce “Me ya sa aka hana ku? Wa ya hana ku?” Sai na yanke shawara cewa, “Za ku ga Moshood, na soke umarnin duk wanda ya ce ba za ku iya ganinsa ba.”
Na kira Babban Jami’in Tsarona, na ce, “A shirya wa wannan ayari su gana da Abiola,” wannan ke nan.
Sannan a lokacin da ake tsare da Moshood Abiola, baya ga likitansa a sanina, babu wani daga iyalansa da ya gan shi.
Don haka lokacin da na zama Shugaban Kasa, bisa tuntuba da ganawa tare da Ambasada Babagana Kingibe, na ba iyalan wata rana da za su zo ganin sa.
To kwana daya kafin ya rasu, iyalansa sun zo Abuja don ganin sa. Saboda wasu dalilai ba dukkan iyalin ne za su iya ganin sa a lokaci guda ba, don haka aka amince cewa idan wannan rukunin iyalan sun gan shi yau, gobe wani rukunin ya gan shi.
Don haka sun gan shi kamar a jiya, yau kuma wannan ayari daga Amurka ya zo don ganawa da ni, kuma na ce su za su iya ganin sa.
A ka’ida da yamma ’yan uwan suke zuwa ganin sa. Don haka saboda na ba wa wannan ayarin daga Amurka izinin ganin sa, hakan ya sa daya rukunin iyalan suka jira don su gan shi.
To a daidai lokacin ganawa da ayarin Amurka, Abiola ya kama rashin lafiya, nan take jami’an tsaro suka kira ayarin likitoci su zo su duba shi, kuma da suka ga halin da yake ciki, sai suka ce ya yi tsanani don haka akwai bukatar a kai shi cibiyar lafiya.
Don haka ayarin likitocin da na Amurka ne suka kai shi asibitin, abin takaici a asibitin rai ya yi halinsa. Sai Babban Jami’in Tsarona ya kira ni ya ce, “Ga wani bakin labari.” Na ce mene ne? Ya ce “Abiola ya rasu.”
Sai abin ya kada ni. Ya ce mini yana can tare da ayarin Amurka, a lokacin ina zaune a cikin bariki, ban koma fadar Shugaban Kasa ba, sai na ce to, ya taho da ayarin Amurkawan gidana, zan gana da su a gidan.
Don haka na tashi daga ofis, na tafi can. Abin da ya saura yanzu shi ne yadda zan sanar da rasuwar Abiola ga iyalansa da yadda za mu shaida wa duniya Abiola ya rasu.
Dole ne in yi godiya ga Allah, sannan ga Jakada Kingibe saboda mun kira shi muka ce ya taho da iyalan Abiola. To da suka zo sai na ba su labarin abin bakin cikin da ya faru.
Kamar yadda za ka yi tsammani, sai iyalan suka kama kuka, ban iya tuna wace ce a cikin matan ba, sai na rike ta, tana ta rusa kuka, tana burwaya, sai Susan Rice, shi ya sa nake tunawa da ita koyaushe, ta ce, “Mai girma Shugaban Kasa wannan ba aikinka ba ne, bari in karbe ka,” don haka ta rike wannan mata har ta dan natsu.
Sa’an nan muka kira mataimakina da sauran mutane muka tsara yadda za mu bayyanar da labarin ga duniya.
Shi ya sa koyaushe nake cewa na gode wa Allah da Ya yi mini jagora. Ba don na ce ayarin Amurka su je su gana da Abiola ba, tabbas ban san yadda zan bayyana wa duniya cewa Abiola ya rasu ba, shin ayarin Amurkar za su yarda cewa ba mu muka kashe Abiola ba a lokacin da suke neman ganin sa?
Kana hawa mulki, ka ce za ka mika mulki ga farar hula, hakan ya ba mutane da dama mamaki, saboda mun san ko a yanzu masu yin juyin mulki a Afirka suna nemo hanyoyin ci gaba da zama a kan mulki. Mene ne hakikanin abin da ya sa ka yanke shawarar ka bar mulki da gaggawa?
To, har wa yau ina kara godiya ga Allah wanda tun farko Ya dora mini nauyin shugabancin kuma Ya taimake ni wajen tattaunawa da abokan aikina har muka samu yanke wannan shawara.
A lokacin da karbi mulki, Najeriya tana cikin tsaka-maiwuya.
An yi ta samun kiraye-kiraye daga fararen hula cewa sojoji su mika mulki, idan ka tuna, a lokacin an yi ta samun zanga-zanga da tashe-tashen hankula har da barnata kadarorin gwamnati da sauransu.
Abin da ke faruwa a fagen siyasa sai ya samu shiga cikin aikin soja. Mu sojoji ya kamata mu kare kundin tsarin mulkin kasa tare da martabar kasa ce.
To lokacin da na hau mulki, rundunar sojin ta shiga matsala ita kanta. Na farko, girman matsayi a aikin soja yana ta sukurkucewa, za ka ga karamin jami’i yana ba da umarni ga wanda ke gaba da shi a mukami, saboda yana cikin shugabannin siyasar kasar.
Na biyu, a lokacin za ka samu maimakon mu kasance muna maganar hadin kan Najeriya, sai muka koma tattauna batun yankunanmu; muna goyon bayan ’yan uwanmu fararen hula.
A cikin sojojin?
A cikin sojojin, kuma wannan babban hadarin ne da na tsinci kaina a aikin soja.
Wani abin kuma shi ne, wadansu daga cikinmu da suka fafata a Yakin Basasar Najeriya don tabbatar da dorewar kasar a matsayin kasa guda mun fara tunanin yaya a gabanmu za mu bari aikin da muka yi na tabbatar da wanzuwar kasar nan a ruguza shi a kan idonmu?
To wadannan ne abubuwan da suka auko mana a harkokin shugabanci; sai muka ce bari mu tabbatar kasar nan ba ta wargaje ba, bari mu yi kokarin dawo da kimar sojoji sa’annan mu dawo da abin da aka sani a baya, a rika bin girman matsayi a aiki tare da kishin kasa.
Sai muka zauna muka yanke shawarar abin da ya fi dacewa a cikin kankanin lokaci shi ne mu ba fararen hula abin da suke muradi kawai; a ba su damar jan ragamar mulkin kasar, sojoji su koma bariki su ci gaba da aikinsu na soja.
To wadannan su ne wasu daga cikin abubuwan da suka sa muka yi abin da muka yi. Ba abu ne mai sauki ba, akwai shawarwari da dama, cewa mu bari mu dauki lokaci mai tsawo, ba abu ne mai sauki a shirya zabe ba, ga wannan da wancan, amma a karshe wadansu daga cikinmu tare da taimakon wadansu da suke tare da ni, muka kekasa kasa muka ce a’a lallai mu mika mulkin cikin kankanin lokaci.
A kashin gaskiya mun so mu yi haka a kasa da wata shida ne, amma sai aka ja kunnenmu cewa shirya zabe ba karamin aiki ba ne, zai dauki lokaci kafin a yi wa jam’iyyun siyasar rajista, sa’annan bayan zabubbukan akalla za a dauki kwana 60 don tabbatar da an kammala shari’o’i da sauransu.
Don haka da muka yi dukkan wadannan lissafe-lissafe kama daga kafa jam’iyyun siyasa da shirya zabubbukan da shirya wa duk wani kalubalantar sakamakon zaben a kotuna; a karshe muka yanke shawarar cewa bari mu yi dukkan abubuwan nan a cikin wata tara.
Kokarin ya kare a samar da wani Janar din a matsayin Shugaban Kasa inda mutane suka yi ta surutu cewa ku janar-janar sai da kuka sake bullo mana ta bayan gida a mika mulkin ga farar hular. Yana kurkuku amma aka yi yadda aka yi aka fito da shi aka yi masa kwalliya a matsayin farar hula dan takara, kuma ya zama Shugaban Kasa. Mutane sun yi amanna cewa manyan janar-janar da ke mulki a lokacin ne suka kitsa wannan?
Na gode da ka yi wannan tambaya. Koyaushe nakan yi murmushi da dariya idan aka zarge ni ko gwamnatina da tilasta wa kasa Obasanjo.
Eh, mun saki Obasanjo da sauran fursunoni muka yi musu afuwa. To a lokacin da aka sako Obasanjo ya zo wajena cewa zai kai gwamnati kara.
“Me ya sa za ka yi haka?” Ya ce sojoji sun durkusar da harkokin kasuwancinsa, sa’annan an take masa ’yancinsa na dan Adam alhalin bai yi wani juyin mulki ba da sauransu.
Sai na ce yallabai ka yi hakuri ka manta da komai, abin da ya wuce ya riga ya wuce, ka gode wa Allah da kake raye yanzu, ka manta da wadannan abubuwa.
Wasu daga batutuwan da ka fadi, zan yi iya kokarina gwargwadon iko in duba su,” sai muka rabu a haka.
Da ya sake zuwa gani na ne, ya shaida mini cewa wata kungiyar mutane ta same shi cewa za ta tsayar da shi takara.
Sai na ce da shi, “Yallabai, in da ni ne kai, ba zan karba ba, don Allah ka manta da wadannan mutane, ka koma gida ka huta ka kula da lafiyarka da sauransu.”
Ya ce, “To na ji, Janar na gode da wannnan shawara taka, zan tuntube ka.” Bai sake tuntubata ba. Abu na gaba da na ji, shi ne yana cikin masu neman takarar Shugaban Kasa.
Na yi kokarin fada wa mutane cewa babu wata rawar da na taka a takarar Obasanjo. Ko me ya faru ya samo asali ne daga jam’iyyun siyasa da sauransu.
Amma ai sai da ka dan dafa masa bayan fitar sa daga kurkuku…
Kamar yadda na yi ga sauran fursunonin! Amma me kake nufi da sai da na dan dafa masa?
Ina nufin kasuwancinsa, ko an tallafa masa da wani abu ya farfado da su wanda yana cikin korafinsa?
Kwarai ma kuwa, ba ma shi kadai ba; dukkan wadanda aka daure a kurkuku saboda dalilai daban-daban, mun yi kokarin tallafa musu; ta hanyoyi da dama.
Mun yi abin da za mu iya yi domin taimaka musu, don haka ba za ka kwatanta wannan da dauko shi domin ya tsaya takara ba.
Ana ganin aminanka na kut-da-kut, Janar Babangida da Janar Gusau suna cikin wannan tsari na PDP, kuma hakan ya sa ake ganin kana da masaniya kuma watakila ka taimaka a nan da can kan lamarin.
Eh, ina sane da halin da jam’iyyun siyasar ke ciki a lokacin; hakan ne ya sa muka tsoma baki ta wasu hanyoyin domin a samu zaman lafiya.
Mun sa wasu sharuddan rajistar jam’iyyun siyasa, amma don samun zaman lafiya sai da muka tankwara wasu ka’idojin saboda a gaskiya Jam’iyyar AD ba ta cancanci rajistar ba, ina jin kamar jam’iyyyun PDP da APP ne kadai suka cancanci a yi musu rajista a matsayin jam’iyyun siyasa.
Da ba mu yi haka ba, da mun shiga matsala. An samu tada jijiyar wuya a Kudu cewa wai ana tauye musu hakkokinsu da makamantan wadannan korafe-korafe.
Sai muka ce, abin da muke kokarin yi shi ne dawo da zaman lafiya, don haka babu wata dokar da take ta dindindin, bari mu ga abin da ya kamata mu gyara.
To sai muka yi hakan Jam’iyyar AD ta samu aka yi mata rajista, ta haka ne muka kashe wutar da za ta iya haifar da fitina da zarge-zarge.
Don haka, in a kokarin kafa jam’iyyun siyasa ka ji mutane na soki-burutsu a nan da can, to ka cire gwamnatina daga wannan.
Ba abin da muka sani, ba mu ce wai a bai wa wannan ko wancan takarar shugabancin kasa ba, batu ne a tsakanin jam’iyyun siyasa.
Idan kamar yadda ka ce Babangida da Aliyu Gusau sun taka rawa, wannan rawa ce da dama suke takawa tare da jam’iyyun siyasar saboda sun zama mambobin jam’iyyun siyasa.
Kana cikin Kwamitin Zaman Lafiya na Kasa da kake shugabanta, a lokacin mika mulki a 2015 ka taka muhimmiyar rawa don tabbatar da an mika mulkin cikin ruwan sanyi a tsakanin Dokta Jonathan da Janar Buhari. Ina mamaki ko shin akwai kalubale ne, saboda akwai wasu bayanai da suke yawo, ina nufin yadda Jonathan ya amince da kayen da ya sha, shin matsin lamba ne daga kasashen waje ko daga kwamitinka da wadansu?
Ina jin duk wanda yake fadin wadannan maganganu na matsin lamba daga kasashen waje ko kwamitin zaman lafiya kan Jonathan don ya amince da kayen bai yi masa adalci ba.
Shugaba Jonathan ya cancanci duk wani yabo da jinjina kan abin da ya yi na ceto kasar nan daga kara tsunduma a cikin rigimar siyasa.
A kashin kansa ya amince da kayen duk da matsin lamba daga jam’iyyarsa cewa kada ya amince.
Ya amince da shan kayen ya kira Shugaba Buhari ya ce, “Mai girma, ina taya ka murna, ina ganin ka riga ka ci zaben nan; ina taya ka murnar zama Shugaban Kasa na gaba.”
Don haka, ina ganin ba a daraja rawar da Jonathan ya taka ba kuma ba a ba shi hakkin yadda ya dace ba in aka ce an matsa masa ne.
Ina sake tabbatarwa ba matsin lambar kwamitin zaman lafiya ko na kasashen waje ne suka sa shi yin haka ba, bisa radin kansa da son kasa da zaman lafiya da ci gaban kasa ya amince da shan kaye.
A lokacin kiki-kakar siyasar tabbas mun gana da shi da Buhari kan yadda za a warware matsalolin.
Za ka iya tunawa irin wasan kwaikwayon da ya wakana a lokacin da ake hada sakamakon zaben, ba shakka hakan ya daga hankalin kwamitin zaman lafiyar, muka lura cewa lallai akwai gagarumin aikin da ke kanmu wajen magance matsalar da za ta iya tasowa a yayin sanar da sakamakon zaben.
Ina gode wa jami’an tsaro da ’yan Najeriya kan nasarar da ta samu a zaben 2015.
’Yan Najeriya mutanen kirki ne, mutane ne nagari masu gaskiya, masu son kasar nan kuma kowanenmu ya taka rawa wajen ganin an samu zaman lafiya da lumana a 2015.
Ko kana da wata damuwa dangane da zabubbukan da suke tafe a badi?
Ina sa ran ganin karin dattaku da fahimtar juna maimakon neman mulki daga ’yan siyasa.
Da dama daga cikin shugabanninmu da ’yan siyasa sun gaza biyan bukatunmu.
Eh, akwai wasu kalubale a sha’anin shugabanci, amma ka san siyasar Najeriya kazantacciya ce, kuma muna yin kazamar siyasa ce a kasar nan.
Addu’ata ita ce ’yan siyasa da masu zaben su kwana da sanin cewa abin da suka yi ko suke yi na iya wargaza kasar nan.
Muna da dimbin matsaloli, mutane na yin komai don kawai a zabe su, sa’annan abin takaici masu zaben kan sarayar da ’yancinsu, su bari a yaudare su da dan abin duniya da bai taka kara ya karya ba.
Ina fata yanzu za mu farka mu yi abin da ya kamata, shi ne mu zabi mutanen da suka cancanta kuma masu amanar da za su kula da mu sa’annan su yi shugabancin da ya dace.
Da alama da dama daga cikin masu mulki a yanzu sun kunyata ka ke nan?
Eh, tabbas ba na jin dadin wasu abubuwa, sai dai kamar yadda ka sani idan kana kan mulki akan ce na zaune gwanin kokawa ne.
Ni da kai, na zaune ne, watakila shugabannin suna kallon al’amura ta wata hanyar, amma a gaskiya ya kamata mu fi yadda muke a yanzu.
Dukkanmu shugabannin ne, ina ganin ya dace dukkan shugabnnin su yi kokarin ganin gudunmawar da za su bayar wajen samar da irin wannan shugabanci da jagoranci.
Sa’annan mu ’yan kasa, ya dace mu yi kokari wajen ganin wadanda muka zaba suna yin abin da ya kamata, ba wai mu zama ’yan kanzaginsu ba, su zama sun mai da mutane bayinsu, saboda suna kan gadon mulki.
Mu rika fitowa muna fada wa shugabanninmu cewa, “Abin da kake yi a nan, ka yi mai kyau, nan kuma ya kamata ka kara himma,” da sauransu.
Amma abin takaici dukkanmu mun zauna muna ta korafi a kafofin sada zumunta ta hanyar fitar da bayanai marasa kan gado da sauransu.
Ina addu’ar Allah Ya sa shugabanninmu su ji sa’annan su fahimci al’amura yadda suke don aiki da su a sha’anin mulkinmu.
Manyan janar-janar da irinka da wadanda suke bayanka a soji sun rikide suka sa rigar siyasa; har sun yi takarar mukamai da sauransu; ban sani ba ko ka taba tunanin ka sake zama Shugaban Kasa ta hanyar siyasa?
Saura kadan in cika shekara 80 a duniya, me kuma zan nema illa in jira lokacina; in koma ga Mahaliccina.
Kafin lokacin fa?
Yanzu kana batu ne kan rayuwata, nan kusa zan cika shekara 80, don haka me kuma zan sake nema?
Allah Ya riga Ya yi mini ludufi a rayuwa, yanzu lokaci ne na in saka, ta hanyar shawartar gwamnati da ’yan siyasa kan yadda ya dace su tafiyar da al’amuran kasar nan.
Yanzu ina kula tare da wasa da jikokina ina karfafar su kan yadda za su taso su zama ’yan kasa nagari.
Kuma kowa yana da abin da yake muradi a rayuwa wadansu suna son shiga siyasa, ina jin dadin yadda su ma jami’an tsaro ake damawa da su a siyasar bayan ritayarsu; kuma daga cikinsu akwai wadanda suka tabuka abin kirki lura da tun ranar da mutum ya shiga aikin soja za a fara koya masa shugabanci da hulda da jama’a da ririta abubuwa kuma wadannan ne shugabanci ya kunsa.
Don haka ina jin dadin yadda wadansu daga cikinmu da suka yi ritaya suke shiga siyasar, sun shiga cikinta kuma kamar yadda na nuna sun yi abin a-zo-a-gani.
Ba ka taba jin za ka gwada ba?
A’a ko kadan ban taba ba. Siyasa ba ta taba zama abin da nake so ba, akwai dabi’u da halayen da ake son dan siyasa ya zamo yana da su; ni kuma tun asali ba na so hayaniya, ba na son rikici da duk wasu rigingimu.
Amma sauran mutane kamar yadda ka sani suna da tasu baiwar yin siyasar don haka ina farin ciki da hakan sa’annan ina fata na bayanmu da za su yi ritaya su ma su fada cikin siyasar a dama da su.
Za ka ga ’yan sanda da sojan kasa da na ruwa da na sama da sauransu a cikin siyasa dumu-dumu, suna kara shiga yadda ya kamata.
(Fassarar Salihu Makera da Dalhatu Lima).