Wainar dankali abincin makulashen zamani ne mai matukar dadi; Amma ba a cika mai saboda lafiyar jiki.
Abubuwan da ake bukata:
- Dankalin turawa
- Attarugu
- Albasa
- Sinadarin dandano
- Mai
- Kwai
Yadda ake yin wainar dankali:
A fere dankalin a wanke, sai a nika ya yi laushi da kauri, kada a saki ruwa a nikan, sai idan ya cije, sai a zuba ruwa kadan.
Daga nan sai a zuba markaden a roba a yanka albasa, a sanya sinadarin girki, da gishiri, da kori, da kayan kamshi.
Sai a fasa kwai kamar biyu, a zuba jajjagen attaruhu kadan.
Sannan a dora, a zuba mai kamar cokali biyu.
Idan ya yi zafi sai a dauko kullin dankalin da ba a hada da kayan dandano ba.
A zuba daidai girman ramin tandar, a bar shi har sai ya soyu ya yi ja, sannan a juya.
Amma fa a hankali za a yi don kada ya wargaje saboda ba shinkafa ba ce, ba ta da karfi.
Idan aka juya, shi ma daya bangaren sai a bari idan ya yi ja sai a kwashe.
Shi ke nan an hattama wainar dankali, sai ci.