Barkanmu da sake saduwa da ku Uwargida. tare da fatan alheri kuma ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake girka miyar kwai. Wannan miyar ana girkata ne ga manyan gobe domin taimaka musu da abincin gina jiki. Miyar kwai na daya daga cikin abincin da ke taimakawa wajen gina jiki. Mutane da dama na da irin na su hadin da su ke yi wa tasu miyar da kuma mahadinsa. Watau abin da za a ci da ita. Ni dai na fi son cin tawa miyar kwan da dafaffiyar doya.
Abubuwan da za a bukata
•kwai
• Albasa
•Tumatir
•Attarugu
• Magi
• Kori
• Man zaitun/bata
• Yankakkiyar hanta
•Garin tafarnuwa
Hadi
Da farko dai uwargida za ta yayyanka hanta kanana sosai sannan ta tafasa da gishiri har sai ta nuna sannan ta sauke. Bayan haka, sai ta fasa kwai kamar biyar sannan ta yayyanka masa albasa da tumatir da jajjagen attarugu da tafarnuwa da kori. Sai ta kwabasu sosai sai ta a jiye a gefe.
Ta dauko tukunyarta ta aza a kan wuta sannan ta zuba man zaitun a ciki idan ya yi zafi sai ta juye hadin tare da yankakkiyar hanta a ciki a rika juyawa a hankali har sai ruwan jikin kwan ya janye kuma an ga alamar nuna sannan a sauke.
Idan kuma ana bukatar ta dan kone ne za a iya cigaba har sai ya bushe sannan a sauke. A ci dadi lafiya.