Akwai abubuwa da dama da ke sa hammata yin baki, ko da an aske gashin wurin.
Yawan gumi ko amfani da man cire gashin hammata da yawan kiba da kuma amfani da turare mai karfi a hammata duk suna sa ta yi baki.
Hanyoyin kawar da warin hammata cikin sauki
Don haka, ga wasu abubuwan da za ku iya amfani da su don hammatarku ta yi haske:
– Garin Kurkum da kwai: Amfani da su na dada wa fata haske. A kwaba garin kurkum da ruwan kwai a shafa a hammata bayan minti 5 zuwa 10 sai a wanke da ruwan dumi. A yi haka kullum kafin a yi wanka.
– Cucumber da lemon tsami: Lemon tsami yana na dada hasken fata, haka ma cucumber na dauke da sinadarin kara wa fata haske da kuma sanya ta laushi da sulbi. A hada ruwan lemon tsami da markadadden cucumber a wuri daya a shafa a hammata, a bari na tsawon minti g 5 zuwa 10 sannan a wanke da ruwan dumi.
– Man kwakwa: Man kwakwa yana dauke da sinadaran kara haske kuma bitamin E. A shafa a hammata a bari na minti 5 zuwa 10 kafin wanka da sabulu mara karfi da ruwan dumi. A ci gaba da yin haka kullum har sai fatar hammata ta yi haske.
Yin amfani da wadannan abubuwan wajen gyaran hammata zai rage warin jiki da hana fesowar kuraje da da kuma rage gumin hammata.