Barkanmu da wannan lokaci, a yau Aminiya ta kawo muku yadda ake kula da hammata domin rabuwa da warinta.
Hakan kuma zai taimaka wajen kawar da bakin launin da ke fitowa a karkashinsa kashin hamata.
- Magidanci ya maka dan uwansa a kotu kan abinci
- ‘An cire al’aura da idon gawar mahaifiyarmu a asibitin Gombe’
Ga wasu aubuwan da za a yi da za su sa hammata haske da tare da kawar da warinta.
Akwai abubuwa da dama da suke haifar da warin hammata, musamman a lokacin zafi.
Daga ciki har da yawan sanya matsattsun kaya da kuma maimaita kayan ba tare da an wanke ba.
Don haka ga wasu dabarun da za a yi don hana wannan wari:
– Aske gashin hammata: A daina barin hammata da gashi, a yi kokarin askewa a akai a kai. Barin gashi a hammata na hana gumi bushewa, wanda hakan ke kawo wari. Ko da an fesa turare, sai a ji warinsa daban na hammatar daban. Don haka a yi kokari da aske shi a cikin lokaci.
– Amfani da lemon tsami: A samu lemon tsami a raba biyu a goga a hammata ko a matse a cikin ruwan wanka. Ko kuma a matse ruwan lemon a samu tawul ana tsomawa a ciki ana shafawa a hammatar bayan an yi wanka, haka zai magance wannan matsala.
– Hodar jarirai: Tana magance warin hammata domin ta da kamshi sai a rika shafawa a hammata kullum, bayan an fito wanka.
– Ruwan tumatir: A matse ruwan tumatir a shafa a hammata na tsawon minti 5 zuwa 10 sannan a shiga wanka. Amma irin wannan zai dan dauki lokaci, kamar mako guda kafin a rabu da warin hammata.
– Sandal wood: A samu icen Sandal Wood da hodarsa a kwaba da ruwa sannan a shafa a hammata na tsawon minti 5 zuwa 10 sannan a wanke, za a wuni ana jin kamshinsa a hammata.
– Ma’ul Ward (Rose water): Yana taimakawa wajen magance warin hammata. Don haka sai rika digawa a ruwa a shafa a hammata bayan an yi wanka.