Kanshi abin so ne ga kowa don karramawa. Mata sun kasance masu sanya turaren wuta a kullum.
Shin ko kun san cewa, wannan turaren wutar za a iya amfani da shi da kabbasa don turara su zanin gado da rigar sawa?
Bayan haka, akwai turaren humra wanda za a iya shafa shi a gashin kai. Akwai na hammata daban sannan akwai na shafawa kamar mai wanda aka fi sani da kulacca da kuma na riga.
Lallai duk macen da ta kasance cikin kanshi, za ta samu girmamawa a cikin al’umma da kuma mai gidanta.
Kuma akwai turaren kanti kamar su ‘Dior’ da Cool Water da sauransu.
— Yadda za a yi amfani da turaren gargajiya
A samu kabbasa (za a iya samun sa a Borno) da kasko, a zuba garwashin wuta, sannan a xora kabbasar a kai.
A kuma zuba turaren wuta a cikin garwashin sannan sai a rufe kabbasa da kayan da za a sanya na ranar ko kuma wandanda za a je unguwa da su, hayakin ya shiga kayan sosai.
Bayan haka, sai a shafa kulaccam (kamar man shafawa yake, amma da turaruka aka hada shi). Bayan an yi wanka sai a shafa a matsayin man shafawa.
Sannan a sanya riga a shafa humra fari ko baki a jikin kayan. Idan kayan mai duhu ne sai a sanya humra baki, idan ko kayan mai haske ne sai a sanya farin humra.
Idan ko ana son amfani da turaren kanti, fesawa kawai ake. Amma na gargajiya ya fi dadewa a jiki don ko kaya sun yi dauda da kyar a ji warin kayan don kanshin turaren.
Irin wadannan turarurruka na taimaka wa masu jego wajen rage karnin nono a jikinsu da kuma jikin jariri.
Sai a ga wadansu mata daga sun haihu suna karni, har ma idan aka dauki dan sai a ji yana karni. Wani karni jinjirin ma har ya shafi wanda ya dauke shi.
Don haka, sai a kula wajen amfani da turare domin magance wadannan matsalolin.