Kayan hadi
. Shinkafa
. Ganyen Fasili
. Man gyada
. Tafarnuwa
. Sinadarin dandano
Yadda ake yi
Da farko uwargida za ta samu shinkafarta ta zuba mata ruwa ta dora a wuta, ta dafa ta. Amma kada ta dahu sosai, sai ta sauke ta wanke ta kuma tace ta bar ta a cikin matsami ta karasa tsanewa.
Daga nan sai ta samu wata tukunyar ta zuba man gyada a ciki, ta kawo tafarnuwa ta zuba, ta soya shi sama-sama. Sai ta dauko shinkafar nan da ta dafa ta zuba a ciki sai ta juya. Daga nan sai ta zuba sinadarin dandano.
Sai kuma ta dauko ganyen fasili mai yawa ta gyara ta yanka shi. Sai ta zuba a cikin shinkafar nan, sa’annan ta sa murfi ta rufe. Idan ta dahu sai a sauke a kwashe.
Ana cin wannan shinkafa da miyar nikakken nama.