✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake gudanar da gasar demben gargajiya a Zariya

A   ranar   Lahadin   da   ta   gabata   ce   ’yan     wasan damben gargajiya suka cika makil a garin Zariya domin ci gaba da wasan damben gargajiya wanda…

A   ranar   Lahadin   da   ta   gabata   ce   ’yan     wasan damben gargajiya suka cika makil a garin Zariya domin ci gaba da wasan damben gargajiya wanda ake yi a kowane yammaci  a filin wasan kwallon kafa da ke Layin Kulob (Club Street) a Sabon Garin Zariya, Jihar Kaduna.

Filin damben wanda ya cika makil da ’yan kallo da bakin shahararrun ’yan wasan dambe daga sassan kasar nan da suka hada ’yan wasa daga bangaren Arewa da bangaren Kudu, ’yan wasan sun fito ne daga jihohin Sakkwato da Zamfara da Kebbi da Kano da kuma Jigawa.

Manyan ’yan wasa ne suka fafata a wasanni daban-daban. Wasa na farko an yi shi ne a tsakanin Shugaba daga bangaren Kudu mai suna Muhammadu Abdurrazak wanda aka fi sani da Ebola da kuma Shugaba na bangaren Arewa mai suna Shamsu Danzaki sai dai wasan ba kisa, amma dai ya kayatar domin da aka kai wa Shamsu Danzaki  wani  mugun bugu Arewatawa sun yi masa gata wato sun tare shi don kada ya fadi da hakan ta sa aka tashi wasan babu kisa.

Sarkin makadan ’yan  dambe, Dan Moyi daga Jihar Sakkwato ya nishadantar da filin wasan da kade- kade da bushe-bushe.

Baban bako a wajen wasan damben Alhaji Aliyu Wushishi, Tafidan Sarkin Wushishi wanda ya taso tun  daga Jihar Neja domin kallon wasan dambe gargajiya ya bayyana farin cikinsa game da irin nishadantarwar da ’yan wasan damben suka yi a yayin fafatawar.

Ya ce ko shakka babu wasan damben gargajiya al’ada ce ta Malam Bahaushe, kuma wata hanya ce da ke isar da sako da tarihi ga na baya.

Ya ce kasashen da suka ci gaba, gwamnati ce take daukar nauyin gudanar da wasannin gargajiya amma a kasashe masu tasowa sai a tarar ’yan kasuwa da masu kudi ne ke daukar nauyin wasannin gargajiya kuma suna samun riba.  “Don haka ina kira ga ’yan kasuwa su rika zuba jari a irin wadannan wasanni na al’adun gargajiya, don akwai riba biyu, za ta taimaki matasa masu tasowa sanin ainihin al’adunsu, sannan kuma za su samu karin kudin shiga.

Na ziyarci kasashe da dama a Nahiyar Afirka na ga yadda ’yan kasuwa da masu hannu da shuni suke daukar nauyin wasannin gargajiya, don haka ina kira ga ’yan kasuwa da masu kudi da ke kasar nan su ma su yi koyi don bunkasa irin wadannan wasanni,” inji shi.

Ya ce a kan haka ne yake kokarin halartar irin wannan gasa, kuma duk inda aka gayyace shi, in dai ya samu dama, to babu shakka yakan halarta.

Daga nan sai ya yaba wa wadanda suka dauki nauyin shirya gasar da su jajirce, su ci gaba da yi, ko ba komai suna daukakar martabar al’adar Malam Bahaushe ne a idon duniya.

Aminiya ta ji ta bakin mai masaukin baki ,kuma  mai gidan damben, Anas Sadauki dan Sarkin Fawa, inda ya ce sun gayyaci ’yan wasan damben ne don su yi gasa a Zariya daga kowane bangare na kasar nan.  Ya ce gasar ta kayatar inda ’yan kallo suka yaba kuma sun kashe kwarkwatar idanu. “Sai dai fatarmu ita ce a rika yin wasa lafiya kuma a tashi lafiya ba tare da fada ko yi wa wani rauni ba,” inji shi.